🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by Oum AmReesh ♥️
(Khaleeseart Raeys ✍️)
Free book📚
Book 1
GARGADI
banyarda wani ko wata yayi amfani da wani sashi na littafinaba ko yayi anfani fashi awani waje ko hadamin document ba tareda sahalewataba, koda allah nabar mutum zaibin kaduna,
TSOKACI
wannan littafin k'irk'irarren labarine banyi dan wani ko wataba , nayine dan nishadan tarwa fadakarwa
GODIYA
ya allah yanda nafara rubuta wannan littafin bani daman kammala shi lapia tareda mika sakon da nakeson isarwa,
game neman karin bayani ko bada shawara whatsapp number 08105565439
Face book name:
Khaleeseart Abdullahi Raeys
My group novel
Six novel khaleeseart hausa novel
Bismillah
Kyakykyawar yarinyace matashiya ketafe kan hanya tana ta tika sauri tamkar kafarta zai tsinke, yanda hanna yanta ke rungume da jikinta tana ta rawar sanyi saka makon ruwanda aketa zabgawa, pink lips dinta se rawa yake, yayinda manyan kyawawa idanuwanta maso dauke da hawaye falciki, gari yayi shiru hanya bakowa se takun sawayenta it tab tab, sauri take kamar mai shirin firewa sama, sautin kukantane kakeji yakara tsananta da alama akwai wani abu datake juyawa cikin ranta, kuka takeyi sosai fiskannan yayi jawur dashi ahankali take furta
" innalillahi wa'inailaihi raju'un abunda take ta dada furtawa kenan yayinda take cigaba da tafiya, ita kanta ba tasan inda take jefa kafartaba itade tasan tafiya kawai take , wani razanannen horn ne yaduke dodon kunnenta wanda yasa kyakykyawar yarinyar rudewa da razana,
jikintane yadau rawa idonta daker take budeshi saboda ruwan da ake, cike da kidima tasuma tunanin kwaucewa tareda kokarin yin gefe , akwai batayi auneba sejinta tayi timm tafadi kasa, motar da ta taho yabugeta , allah ya taimaka bata ji wani rauniba, se dan buguwa da tasamu, head dinta yadan bugu ta baya se hand dinta da takwanta akai, wani razanannen ihu tasaka tafara kokarin tamikewa kamar wacce tazauce tana kokarin zurawa da gudu taji anrukota, kafin tayi wani yunkuri seji tayi anwaketa da mari tass, nanfa tarike gefen face dinta tasuma kokarin magana, kafin tace Wani abu se murya ta tsinkayi da cewa,
" hi you wani irin rashin hankali ne yake damunki da zakizo kitsaya inda kikeso, kinzo kinwani tsayawa mutane akan hanya, ko titin na gidan kune,?are you crazy "
yafaɗi yana jijjiga ta, ganin bata bashi amsaba kanta sunkuye yasa, cikin takaici yaja wani guntun tsaki yana fadin,"matsa kibani waje stupid girl look at you da Allah yafada tareda cillata gefe, tunda yafara magana bata dagu ta kalleshi ba kanta na kasa tanata barzar kukanta, yabugeta da mota kuma ya tsaya yana mata wasu surutai, still bata mata time dayayi, daga kai tayi tareda bin bayansa da kallo time din har yashiga mota yayi mata key yayi kanta dashi kamar zai bugeta, nanfa tamatsa dasuri shiko yayi gaba abunsa,
" Allah ya isa ya allah kasakamin " tafaɗi tareda cigaba da tafiyar ta, bata dau lokaciba takarisa gida,,,
kutsa kai tayi cikin gidan dan ko sallama batayiba takutsaciki, kuka takara fashewa dashi yayinda takarisa inda mahaifiyar tata take kwance tafaɗa jikinta,
" umma kitashi mutafi asibitin nan akwai, naje duk inda muke tunanin za asmu Abba but ban sameshiba, har gdn Mami nakuma zuwa baya nan, na tambayeta ina yashiga ina za asameshi Amma secewa tayi itama bata saniba, nashiga ukuna nikam," tafaɗi tana kuka,
"umma ya zanyi please kitashi mutafi "
tafaɗi tareda kokarin dagata amma inaa takasa, bin mahaifiyar tata tayi da kallo idonta ya kafe , still numfashinta ya tsaya cak kamar bacecciya, tashi tayi dasauri tafara yin baya baya tana fadin," a'a umma karkimin haka tafada tana tana sake binta da kallo, inna lillahi wa'inailaihi raju'un tafadi tareda juyawa tayi waje da gudu, a dadaiba tashigo dagudu cikin rudu, gefenta nadauke da wata mata wacce ta taimaka mata suka daga umma suka fito da ita suka kutsata cikin adaidaita,
"NEESHA Allah ya sauwake yabata lapia" matar tafaɗi
" amin nagode "
Nisha tafada tareda tallafe mahaifiyar tata tana mai cigaba da kuka, har cikin asibitin suka shiga, Nisha tafara kokarin kokarin fito da ita, da sauri nurses dinda ke wajan suka suma kokarin taimaka mata, nan suka daurata gadon potien suka turata izuwa ciki domin duba lapiyarta, itama Nisha binsu take tana surutai har aka isu room din da za ashiga da ita , nanfa nurse din suka dakatar da ita suna fadin "tajira anan, jikin sanyin jiki Nisha tazube saman gwiwowinta tashiga rera kuka mai tsuma rai,
Doctor ne yakunna kai zai shiga cikin room din cikin hanzari Nisha ta tareshi tana fadin," doctor dan allah ka cece ran mahaifiyata ita kadae garan karka please karkabari tamutu.., bata kai ga marishe batuntaba, doctor yayi saurin cewa,
" haba baiwar Allah kefa musulmace kizama mai hakuri mana ran mahaifiyar ki ba ahanunmu yakeba agurin allah yake duk yanda yaso zaiyi ikonsa, ki roki Allah yafito da ita lapia, mukuma zamuyi iya kokarin gurin cetota daga hadari, don't worry comforting you mind " yana gama fadi hakan yakunna kai cikin room din,
"Hasbunallahu wani'imal wakil" abunda ta faɗi kenan takuma zubawa kasa tahada kai da gwaiwa tana cigaba da kuka kasa kasa, jitayi kanta yayi bala'in sarawa yakuma yimata nauyi seyanzu ta tunada da abunda yafaru da ita dazu,
shafa goshinta tayi inda kanta yadan fashe tana sake fadin allah ya isar mata, wasu sabbin hawaye ne suka shiga sakeyin zarya saman face dinta, tana cikin wannan yanayin taji ana faɗin,
" baiwar Allah tasu muje ko?" da sauri Nisha ta dago tana kallon nurse din da ke tsaye kanta, tashiga faɗin,
" yauwa ya umman nawa take tabude ido tana cikin koshin lapia,? "nurse din batace kalaba se jan hand din Nisha datayi takaita dressing room ta zaunar da ita, tashiga mata dressing wajan da taji ciyo agoshinta dayake dan fidda jini, seda ta kammala gyara mata ciyon nurse din tasuma kokarin mikewa,
" bakice min komaiba" Nisha tafaɗi tana kallon nurse din, itama kallonta nurse din tayi tana faɗin,
" sorry doctor zaizo yamiki bayani karki damu" nurse din tafaɗi tareda ficewa, bata dade da fitaba doctor ya shigo room din, zuro taimasa da ido yayinda yake karisuwa ciki,
" yadai ?
yafaɗa yana kallonta, bata cemasa koamiba se tambayar ummanta da take, shima baice wani abuba se cewa yayi tabiyoshi office yamata bayani yana faɗin haka yajuya itama bayansa tabi yana shiga office din yazauna bisa kujera itama yama nuni da tazauna, bai musuba ta zauna kamar yadda yace tana mai kallonshi, shima kallon nata yayi tareda dauko wani file ya ajiye agabansa yana kallon Nisha da itama kallon nasa take,
" bakida dan uwa namiji ko mahaifinki kode wani naki? shiru Nisha tadanyi daga bisani tace
"babu ni kadaice dagani se mahaifiyata"
" okay no problem" Doctor yafaɗi yana dan gyara zama, cikin kagowa da sun sanin halinda mahaifiyarta take ciki Nisha tasuma faɗin,
" bakace min komaiba gameda ummataba , kode tamutune , kafadamin tamutune ko tana raye"
gyara murya Doctor yayi yashiga bata amsa da cewa," mahaifiyarki tanada rai amma a hanlida ake ciki yanzu tana cikin mswuyacin hali mahaifiyar ki tana da hauwan jini ga jiwon zuciya , amma ayanzu duk wannan bayida wani nasaba da halinda take ciki ayanzu, kodar mahaifiyar ki yasamu matsala duk2 za amata aiki kuma ba asu aikin yaja dugun time, ana bukatar kudi so ina bukatar sa hanun ki anan" ya mika mata wani file, tunda yafara magana daga inda take tagagara kwakwaran mutsi se hawaye kawai, daker ta iya sa hanu ajikin takardan ta dago ta kalleshi,
"doctor kudin harnawa ake bukata?"
numfashi yadanja kafin yace,
" 5 million naira, because fitar da ita waja mukeson yi (indian)
"nashiga ukuna wlh doctor ko dubu 10 bamudashi ayanzu balle wadannan kudaden daka lissafomin yanzu, wayyo ya zanyi" tafaɗi tareda mikewa da sauri tayi waje da gudu batareda taji mai zai kara faɗiba, tana fita bata zame ko inaba sae gd,
tana tafe tana kuka tareda tunanin ina zata samu wadannan kudaden, to mesukeda shi da zasu sayar susamin wannan kudin to ko gdnsu suka sayar bazasu sami wadannan kudinga da wannan tunanin ta tsaya cak ta tsaida mai adaidaita sahu, tamasa bayanin inda zata, basu dau wani lokaciba hanya ta kawosu gd, nan ta sallameshi tashiga gdn, shiganta keda wuya tajiyu sautin muryoyi daga cikin gdn, dasauri takarisa ciki..,
tsayawa tayi tana karewa tsakar gidan kallo ganin yanda akayi kace kace dashi, yansu dake daki duk anfito musu dashi waje, wasu gardawan samarine suketa fito musu da kayan suna wula kanci dashi, gefe kuwa ta hangi matar abbanta wacce ake kira da Mami, waro ido tayi sosai dan ta tabbatarda abunda idonta yake gani gskyne ko karya, tabbas bakarya bn, mami ce daga nise tsaye ta hade hanu akirji se wani jijjiga take tana hararo Nisha tana fadin,
" in kingama kallon banzan naki sekizo kifara kwashe muku komatsan kayan naku kifara muku gaba dashi kusan inda dare yamuku dan wlh bazaku kara kwana gd nanba, Zama yakare muku daga yau,,"
da sauri Nisha takarisa inda mamin take tana faɗin,
" wai mai kike fadane ? incede nan gdn gdn mune halak malak bafa haya muke ba gdn mahaifinane to meyasa zamu bar gdn kuma,? ina mukedashi wanda yafi nan " cikin kuka Nisha tafadi kasa tareda kama kafafuwan mami tana fadin,
" dan Allah inda wasa kike kidena yanzu haka umma tana asibiti batada lapia kuma haryanzu banga idon abba,...bata kaiga karisa maganartaba taji ta fincikota ta dauketa da mari tass,
" lallai fa yarinyar wato nine namiki wasan, to ki kalli cikin idona ko kinga wasa acikinsa, bawasa nakeba inma kina wannan tunanin gwara kidena, nan gdn gda nane bana mahaifin kiva, au dama ku amarkinku keda uwar taki nan din gdnkune,? To zaifi muku kyau kutashi daga wannan mummunan mafarkin, mahaifin ki ya dade da mallakamin wannan gdn kungako gdn nan mallakinane, kudena tunanin zakuci gadonsa, domin kuwa bazaku taba ciba, matsawa tayi kadan saitin kunnen Nisha tasuma fadin,
" Hashim ya muku nisa daga yaudin nan bazaku sake sashi aidanun kuba keda uwar taki har abada kuwa kunyi bye bye daga yau, tunda mami tasuma zan tukanta Nisha takasa cewa komai se kallo kawai datake bin mami dashi se idanuwanta da keta ambaliyan ruwan bakinciki, da ker ta iya bude baki tasuma fadin,
" mekike nufi da haka,? nacewa bazamu sake sa abba adunmuba kwata kwata nakasa gane inda maganarki ta dosa" dan ja dabaya mami tayi tana faɗin
" yo ai dama ke yarinya ce bazaki fahimceni ba amma inkika sanar da ita uwar zata gane ta fahimta , tana fadin haka taja hanun Nisha tayi waje da ita tareda kayan nasu gaba daya, kuma kulle gdn tayi gaba abunta, hankali Nisha ba karamin tashi yayiba gaba daya ta kidime,
' to yau ina nasan zan shiga taredani da kayan nawa, oh allah wannan tani irin rayuwace'
matsawa tayi tasuma lalumar wayarta cikin wata back, takoyi sa'a tasameta sede glass din wayan tadan tsage sbd buguwar da yayi, makotansu tashiga tayi mata bayanin abunda yafaru cewa antashesu daga gdnsu, ta taimaka ta ajiye mata wasu kayanta tunda taga kamar akwai space dinda za'a ayi killace kayan tunda bawani yawane dasuba, matar bataja maganarba tabi nisha suka suka kwaso kayan wayanda bazasu iyaba suka nemi taimakon samari aka killace kayan, bayan gama Nisha tacewa matar bari taje ta dawo yanzu,
"to " kawai matar tace mata, Nisha tasa kai tafice, tana fita tasa hanu tazaro phone dinta tayi dealing wani number kamal ya baiyana screen phone din wayar batayi wani ranging sosae ba aka dauka,
"hey babe how are you today antunu dani kenan, I hope de kina lapia?"
"balafiya" Nisha tafaɗa,
" so what happened, cikin sanyin murya nisha tace," fadamin inda kake nazo nasameka but in kana nan "
" alright ina nan but jiya nadawo inda bukatar yiyuwar zuwana senazo ba matsala yafaɗi,
"aa ba damuwa nizanzo,"
"okay ina masaukin bakin Daddy I hope baki mance gurin but zan turo miki da address abunda yafaɗa kenan yakatse wayar, bada bata time yasake hankado mata da address din inda yake, wani goron numfashi Nisha taja daga bisani ta tattara nutsuwanta tasamu daman tsaida mai adaidaita tamasa bayanin inda zai kaita, basu dau wani dugun lokaci ba mai adaidaita ya direta gefen wani gd dan madedeci gdn ya hadu kuma ya tsaro duk dacewa bayida wani girma , sallamar mai adaidaita tayi, sannan matsa tana dan waige waige kamar mara gsky, bakowa wajan shiru yake, hanu tasa ta tura kofar geat din takuwa jita abude, gabantane yafidi hangenshi datayi daga kofar parlourn yana kaiwa da kawowa da alamar ita yake jiran isuwarta,
wani murmushi yasakar mata yayinda take kokarin karisuwa harta kariso kallonta yake yana murmushi, tsayawa tayi itama tana binshi da wani kallo, daga bisani tasunkuyar da kai kasa tana kokarin suma yin magana, shiiiii taji yakatseta dacewa,
" mushiga ciki yana kokarin bude kofar parlourn danufin shiga, cikin hanzari Nisha ta katseshi da cewa,"
"aa kar kadamu maganar ba mai tsayi bace zata yiyo muyita anan" dan hade gira yayi yana faɗin,
" ni bazan iya tsauwa ananba, idan maganar is very important ne kya shigo daga ciki" yana faɗin haka yajuya yashige ciki abunsa, lumshe ido tayi tanajin wani abu aranta jitayima kamar tajuya ta tafi abunta,
"hey you fita nakesonyi ana jirana outside" yana gama faɗi hakan yajuya yakoma, cikin sauri tabi bayanshi ta tura kofar tashiga,
azaune tasameshi yana zaune yana amsa call, hakan yabata daman tsayawa tana kallosa har yagama wayan yamaida kallonsa gareta, have a seat mn yafadi, batareda wani musuba Nisha tazauna,
"I'm hearing you so what happened"
kamal ya tambaya, cikin rawar murya Nisha tasuma magana,
" dama umma tace batada lapia shine nakaita asibiti, to shikenan akace se ammata aiki, sekuma tadanyi shiru ta dago tana kallonsa wanda shima haryanzu ita yake kallo yayinda take maganar, dan gyara zama yayi yana faɗin,
" subhanallah meya sameta, nanfa Nisha takora masa bayanin abunda doctor yace dakuma kudin da akeda bukata" daga bisani tasunkuyar da kai akunyace, cikeda tausayawa ya tasu daga inda yake zaune yakuma kusa da inda take yana fadin,
" naji duk bayaninki karki damu ki kwantar da hankalinki, nadau duk wani nauyi da duk wani abunda akeda bukata, cikin hanzari da murna ta dago takalle shi tana faɗin,
" nagode kamal allah yasaka maka da mafificin alkhari,"
" ameen" kawai yace yamike ya nufi bedroom ya tattaro duk wani kudaden dake cikin dakin ya tusasu cikin wata back , kaida kaga kudin kasan bana nigeria bane , cikin hanzari yadawo parlourn ya tattara da Nisha inda yabarta , yana isowa inda take ya kalleta yana faɗin,
" let's go " cikin hsnzari Nisha tasuma faɗin,
" bakace jiranka akeba? baseka min rakiya ba kabarshi karka wahalar da kanka wajan rakaniba zanje da kaina, hakan ma nine da godiya,
" aa tare zamuje nima inaso naga jikin umman naki yafaɗa tareda shigewa gaba yana kokarin bude door din, koda budewarshi yaja yatsaya yana bin yarinyar dake tsaye bakin door din tana kallonsa , kyakykyawar yarinyar ce duguwa kala larabawa siririya mara jiki, tana sanye cikin wani duguwar riga black abaya tayi mata kyau sosai, tayi rolling din kanta da gyale, murmushi tayi masa yayinda take kokarin karisuwa ciki,
" yadai kake kallona kamar baka taba ganinaba? tafaɗi yayinda idonta yasauka kan Nisha dake bayansa tana zazzare ido kamar mara gsky, shiru yarinyar tayi tana karewa Nisha kallo, wannan kuma wayece Kamal yarinyar ta tambaya tana nuna Nisha, shiru yayi baice mata komaiba yamaida kallonsa ga Nisha wacce itama shi take kallo, bataji mai zaiceba ta amshi jakar hanunsa tawuce dasauri, juyawa yayi yamaida kallonsa ga yarinyar da tayi masa zuro tana kallonsa hawaye fal idonta, waje tasamu tazauna tana wani huci na takaici da bakin ciki, shima jiki ba kwari yanemi gu yazauna kusa da kujeran da take,
"Nabilah meya kawoki kuma wayafa miki ina nan?
"Hajiya ce " abunda tafada kenan tayi shiru, shima shirun yayi baicemata Kala ba, kallonsa tayi tana fadin,
" ya Kamal wata yarinyace tafi yanzu kuma mai tazoyi,? nabilah ta watso masa tambaya,
" taimako tazu namata abunda yace kenan ya mike,
" wani irin taimakone wanda baza iyashi awajeba se anshigo ciki, kunkillace kanku, ?
"Kee ! mekike nufi ne, mekike son cewa? ya tambaya cikin daga murya,
"ya Kamal kasan ina sonka ina kuma kishinka bayanda za'ayi nazo na tarar dakai da wata raina yamin Dadi, kai bazaka taba canzawa bane, katunafa iyayenmu suna kokarin hada auranne nida kai nan da yan wani lokaci, inasonka kaima kuma nasan kana sona but hakan bazaisa kadena kula wasuba, induk baka duba wannan yakamata kasan mahimmanci alkawari, kayiwa Daddy da su Hajiya alkawari kadena abunda kake katuba ba laifinka bane , hakan yasa big bro yasa atsaida ranar bikinmu , amma sekuma kazo kasaba alkawari, kazo kadauko wata yar iska kuzu kuna cin,. am..tass taji yawanketa da mari seda taga wasu taurari, wani ihu tasa tareda zubewa saman capet,
" ni dan kine da zakizo kinamin magana son ranki, kina faɗamin duk abunda yazo bakinki, let me tell you something baki fini sanin abunda zanyiba kuma bake zaki faɗamin abunda yadace nayiba, kitashi ki tafi kikoma inda kika fito, inyaso sekije kibasu labarin abunda kika gani cewa kinganni da wata yafaɗi tareda fizgota yarakota har bakin kofa yamaida kofar yarufe, kuka takuma fashewa tareda rugawa da gudu tayi waje tashiga motar ta taimata key,..
tunda Nisha tabar gurin kamal ba inda tazame se asibiti akokarinta nashiga wayarta tayi kara, nan taduba screen din wayan taga friend dintane Salma dazuma taga miss call dinta bata daukaba tacigaba da tafiya, direct office din doctor tanufa batakaiga karisa waba ta hangoshi yafito daga wani room, seda takarisa inda yake tasuma mika masa kudin, cikin hanzari ya dakatar da ita tareda faɗin,
" biyoni office wucewa gaba ta kuwa tarufa masa baya, suna shiga yamika mata wani takarda yace tasa hanu, bada wani jinkiriba Nisha ta karba ta sanya hanu, daga bisani Doctor ya karbi jakar hanunta suka fita,
" zan iya ganin ummata Nisha ta tambaya Doctor?,
" Eh zaki iya ganinta but har yanzu bata farfaduba, amma munasa rain kafin gobe da izinin Allah zata iya farkawa kishiga ki dubata, to Nisha tace daga bisani ta dangana room din da umma take kwance,
Ahankali takarisa gadon da umma take kwance zama tayi kusa da ita tareda daukan hanunta ta daura saman nata, cikin kallo da tunanin halinda mahaifiyarta take ciki
" Allah sarki ummana allah yabaki lapia, ke kade kika ragemin aduniyar nan, ke kade nake kalla naji dadi hankalina ya kwanta, bakya bari nazubda kwalla balle har ta kaini ga kuka, amma yau nawuni cikin kuka da hawaye, nayi kukun da bantaba irinsaba, but narasa mai lallashina, yau narasa inda zan shiga naji dadi, kuka ta fashe dashi kasa kasa gwanin ban tausayi, seda tayi kukan ya isheta harta suma jin ciwon kai, sabuluwa tayi daga saman gadon tazauna kujera ta kifa kanta jikin gadon tana maida ajiyar zuciya, tafi mintuna ahaka jin shigowar nurse ne yasa ta daga kai tana bin nurse din da kallo yayinda take karawa mahaifiyarta ruwa, murmushi nurse ɗin tayi tana kallon Nisha tana faɗin,
" yadai sis? ummna zata bude ido tasamu sauki? Nisha ta tsinci kanta da yiwa nurse ɗin tambayar ,
" mai zai hana za ayi aiki tasamu sauki karki damu kanki zata warke takoma garau kamar ma bata taba ciyoba, don't worry barinaje nabarki lapia " nurse ɗin tafaɗi cike dayiwa Nisha murmushi tafice, tabbas maganar da nurse din taimata ya dan kwantar mata da hankali, kiran sallan magarib daya ratsa kunnowan tane yasa ta mike tanufi toilet alwala tayiyo tafito tana yarfe ruwan fiskarta, to damema zanyi sallanne bayan ban dauko komaiba ta tmbayi kanta, kode naje gdnsu salma nayi sallahn na dawone, shiru tayi se kuma tafito daga room din tanufi dakin da ke gefensu sallama tayi hade da tura kofar tashiga,.
. tsayawa tayi tana bin matar da kallo , babbar matace tsuhowa fara tass kalar larabawa tana sanye glass aidonta waya take shiya sanya Nisha tsagai tawa, wai me kuke nufine kunbarni da yaro kuma gashi haryanzu baku lekoba, ku komai naku nasaibi, ganin yarinya tsaye daga gefe shiya sanya hajiyar dakatawa da wayar da take, ta tsaya kallon yarinyar yayinda take kokarin karisuwa,
" sannu Hajiya " Nisha tace yayinda tamaida kallonta ga yaron dake kwance gefenta an daure kafarsa da bandage da alma karayace,
"yauwa sannu " Hajiya ta amsa tana kallon yarinyar,
"ya maijiki"
Nisha takuma faɗi tana kallon kyakykyawar yaron game da tausayawa,
" Alhamdulillah " hajiar ta kuma amsawa daga nan Nisha tashiga tambayar taimakon sallaya zatayi sallah because basu tahu da komaiba,
" lah bakomai gashin nan Hajiya ta dauka ta mika mata cike da fara'a da sakin fiska, cikin hanzari Nisha ta amshi sallayar ta shimfida ta tada sallah, tunda tafara sallahn Hajiyar taketa binta da kallo, yarinyar tashiga ran Hajiyar dagani yarinyar akwai hankali da nutsuwa gata kyakykyawa da ita, hajiar na tsaka da maganar zuci tajiyu sallama, wasu kyawawan yan matanne guda biyu suke tafe da alamu ko jikokintane, hannunsu dauke da basket din abinci daya nabin daya suka shigo suka zauna, sannu Hajiyarmu kinsha zamafa, bata cemusu komaiba, se binsu da kallo da takeyi, bayansu wata matashiyar matace ke tafe da kaganta kaga wayewa da karatu, fiskarta babu annuri ta karisu ta zauna kusa da yaron dake kwance time din ya bude ido,
"Oh my baby boy yajikin naka tafaɗa tana shafa gefen fiskar yaron, ,
" uhm uhm mommy kikiramin papa, dafa shoulder dinshi tayi tana faɗin,"
What happened kake neman papanka kasan baza asameshi Wannan time din ba so what do you want,
"mommy ciyon zafi " yafaɗa cikin sigan kuka,
"oh sorry dear zai dena kajiko, gyada mata kai yayi yana matse ido, so inzuba maka food abunda kakeso nadafa maka,"
" eh " kawai yace nan tasumu zuba masa abincin, kallonta kawai Hajiya keyi tashigo but ko kallon ta batayiba balle sannu ko madallah, hmmm Allah yakauta, muryan nisha nisha sukaji tana fadin,
" Hajiya ga sallayan nagode,
"lah bakomai yata, se yanzu hankalisu ya dawo kan Nisha da tun shigowar su bawai sun lura da ita bane, zuba mata ido sukayi suna kallon ta, itama Nishan kallonsu take tareda gaishesu, yan matan ne suka samu daman amsawa, but ita dayan Nisha ko kallo bata ishetaba balle tasa ran amsa gaisuwan ta, kokarin fita Nisha tasunayi, Hajiya tayi saurin faɗin,
" tsaya ki karba muku abinci mana tunda naji kamar kince baku taho da komaiba,
" lah Hajiya kibarshi kawai nagode zanje na dauko agd" Nisha nafaɗin haka tajuya da sauri tafita daga dakin tanufi dakinsu, waje tasamu tazauna tana tunanin kirki irin na Hajiyar, wata zuciyar cewa tayi
'dama kin tsaya kinkarbi abincin ko kya kori yunwar dake tare dake, amma kikace zakije gd kidauko ko dakin wata uwar zaki dauko oho'
sallama taji anbudu kofa azatunta doctor ne, setaga wayan nan yan matan ne suka shigo daya nabin daya tareda basket din abinci hanunsu, daga gefe suka tsaya suna kallon mahaifiyar Nisha cikin tausayawa , kallon Nisha sukayi suna murmushi tareda tambayar ya mai jikin, Nisha ta amsa musu dacewa
"da sauki "tana kallonsu irin tsan tsar kyau dake tareda yan matan kamar ba yan kasarba,"
"hajiyace tace mubiyoki da abincin nan tunda kinki karba acan "daya daga cikinsu tafaɗi,
"Ayya nagode sosae Nisha tace tana dan murmushi, ajiye mata basket din abincin sukayi tareda kokarin juyawa sufita, dasauri daya daga cikinsu tajiyu tana fadin,
"munyi mantuwa baki fada mana sunan kiba" jiyuwa sukayi gaba dayansu suna kallon Nisha suna jiran amsa,
"sunana Aisha ko kice anisha amma anfi kirana da nisha, wow nice name nikuma,
" fareeda but ana kirana da reeda sisterna kuma fadeela nice to meet you suka Faɗi,
" nima haka " nisha tafaɗi tareda musu godiya, daga nan suka mata sallama suka fita, Nisha najin fitarsu da sauri tadauki plate tafara kokarin zuba abinci, bude food flas din abincin tayi koda budewa wani dadda dan kamshi ya buwayi hancinta, kuskusne yaji hadi gami da kayan lambu anyanka hanta kana na kana na, se zuba kamshi yake yawunta yawunta ba karamin tsinkewa yayiba, dayan kulan kuwa papper chicken ne yaji albasa se zuba kamshi yake shima, nan ta diba tasuma ci, tunda tagara ci take santi saboda dadin abincin, seda taci takore yunwar cikinta daga bisani takai hanu ta tsiyayi sassanyar lemon juice yayi sanyi dadin shaa, tana tsaka dashan lemon ta tsinkaya muryan umma tana fadin," zatasha ruwa, azabure Nisha tamike tayi kan umma,
Nisha tsayawa tayi kan umma dake kwance tana kokarin bude ido, da sauri Nisha tashiga tallafo umma tana faɗin
"Umma kibude idonki kinganni tafada cikin sigana kukan farin ciki,
" ruwa ! umma tasake faɗi karo nabiyu, da sauri Nisha ta tashi tadauki ruban ruwanda su reeda suka hadu mata cikin basket tashiga zubawa cikin cup tanufi umma tareda tallafo ta takai mata setin bakinta jikake makot makot tana shan ruwan, wani dadine ya lullube nisha zuciyar ta nayin wani sanyi, tana kammala bata ruwan tashiga kokarin gyara mata zama tasanya mata filo abayanta yanda zataji dadin zaman, umma bari naje na kira doctor Nisha tafadi tareda ficewa da sauri,
Ba adadeba suka shigo tareda likita, doctor seda ya duba umma sosae yakalli Nisha yana faɗin,"
Masha Allah akwai alamun nasara inshallah, "sede kuma naga bata bude ido ba Nisha ta tambaya,"
"wannan ba wani matsala bane zata bude ahankali," allura yamata yasanar da nisha cewa koda yaushe zata iya farkawa, kuma anemi ruwan zafi kokadanne tasha, wani ruwa yakuma daura mata daga bisani yafice, wayanta ta laluba ta dannawa salma kira, aikuwa kamar jira take carab ta daga,
"Yar duniya tunyaushe nake kiranki kinki picking, ko bakiga miss call dina bn, salma ta tambaya, "
"Ke nagani bana yanayin da zan iya dagawane, nisha tafadi cikin damuwa,
"What happened,? salma takuma tambaya,"
"Ummace ba lapia muna hospital,"
" kai amma bakida mutunci umma ba lapia shine koh labarin, wani asibiti ne yanzu zan gayawa ummy zamuzo ,"
"nan Nisha tafada mata hospital din dasuke daga bisani Nisha ta sanar da salma tana da bukatan ruwan dumi, salma tace ba matsala semunzu,
"inkun iso please you can call me, okay salma tace daga nan ta katse wayar, juyuwar da zatayi suka hada ido da umma, gaban tane yafaɗi yayinda bakinta yayi hanzarin faɗan,
" umma!, hade da fadawa jikinta tasaki wani sabon kuka,
"Nisha aina muke" umma ta tambaya cikin raunin murya na marasa lapia,
"muna hospital ne nisha ta bata amsa tana kallonta,"
Ina mahaifinki, ? daguwa nisha tayi tana kallon mahaifiyar tata, abba kuma,?
"Baizoba baima san awani hali mukeba, kuma ba inda banje nemansaba amma ban sameshiba, umma meye kike nemansa bayan ganinan kusa dake , what do you want tell me nizan miki, kurawa nisha ido umma tayi kafin tace,
"fushi kike da Abban nakine,?" hawaye nisha ta shigayi Shar shar kafin tace
," umma Abba ya dena sanmu yanzu ko inda muke baya son zuwa, tun yaushe rabonmu da musashi a ido, kwata kwata yanzu bai damu da muba balle yasan halinda muke ciki, ayanzu hankalisa ya koma kan mami yafi sonta harma.... kuka ne yaci karfinta nan ta sunkuyarda kai sotake ta sanar da umma abunda ke faruwa mami ta tashesu da gdnsu because acewar ta abbane ya mallaka mata, but se kuma ta fasa saboda halinda umma ke ciki bai kamata ta sanar da ita ba, muryan umma taji tana fadin,
"Ki kwantar da hankalinki, karkiyiwa mahaifinki irin wannan kallon, duk abunda kikaga yanayi bawai cikin hankalinsa yakeba, baisan yanayiba kuma ba laifinsa, ninasan halin mijina, nizan bada labarin abunda zaiyi da kuma abunda bazai aikata ba, inaso kisani ko bayan raina ban yadda kinisan ceshiba, duk duniyar nan bakida wani gata da yawuce shi, haka shima kafa daniyar ba abunda yafiso kamarki, kuma kema shaidane ba karamin abubane zaisa mahaifinki ya nisan cemu lokaci daya ba tareda wani dalili ba, dan haka, kinemesa aduk inda yake kinuwa duniya ke diyarsace, mahaifinki makiyane akewaye dashi duk inda yake suna nan biye dashi, kidinga masa addu'a akoda yaushe, zanyi alfahari dake kobayan raina"kuka nisha tarushe dashi tana faɗin,
"Umma kidena irin wannan maganan " ta gama tsinkawa Nisha zuciyar, hanu Nisha tasa tashare hawayenta hadeda dagowa takalli umma tana fadin,
" naji maganar ki kuma inshallah zan kasance mai biyayyawa maganarki, plate tadauka tashiga zubawa umma abincin tareda dire plate din abinci gabanta tana faɗin,
"Umma kici abincin kafin salma sutaho da ruwan zafin, cikin kosawa da magana umma tace,
"bana bukatan abinci ayanzu" tafaɗi tareda ture plate din gefe, wayan Nisha ne yashiga kara, dan dubawa tayi taga salmace hakan yasa tamike tsaye tana faɗin,
"bari naje na shigo dasu salma, gyada kai kawai umma tayi Nisha tasa kai tafice, bata dadeba suka shigo tareda su salma hanunsu rike da kayan bukatu, waje suka samu suka zauna salmace tasuma magana dacewa,
" sannu umma yajiki,
Jiki alhmdllh salma umma tafaɗi fiskarta daukeda murmushi, daga bisani ummyn salma ta karbi gaisuwan dacewa,
" sannu ashe bakiji dadi ba, ,"
"Wlh kuwa, "
"ayya yajikin,?
"Jiki da sauki allhamdullah,
"to allah ubangiji yakara sauki,
" ameen ya Allah"
Salma zungurin kan Nisha tayi tana fadin," umma ba lapia shine ko kisanar damu kiketa dawainiya ke kadai kirkinki yayi kadan gsky,
"Keyanda nake cikin tashin hankali ina tunanina zaikai nan, bakisan damuwar danashiga yau bane, Nisha tafaɗi tareda daukan cup tashiga hadawa umma tea, nisha nagama hadawa ta mikawa umma cup takarba tasuma shaa, to nisha bari muje munbar gd bakowa ga dare yayi, allah yakara sauki gobe zamu dawo, ummyn salma tafadi tareda mikewa,
" to mungode Allah yasaka umma tafadi yayinda ta dire cup din tea gefe, seda Nisha ta rakasu har bakin geat sannan ta dawo, Nisha na karisa shigo tayi gefe da cup din tea din tasamu daman zama kusa da umma tana kallonta, itama umma kallon Nisha take tana faɗin,
" sallah nakeson nayi, kallon ruwanda aka daurawa umma nisha tayi tana faɗin,
" ruwanma yakusa karewa bari nakira doctor yacire miki inyaso sekiyi sallan, nisha na faɗin haka tajuya tafita, ba adadeba suka shigo tareda likita yacire mata ruwan yana mai tambayan ta ko akwai wani damuwa ko matsala, nan umma ta sheda masa ba wani damuwa,"
"To masha Allah haka akeso inkinyi sallan anjima za azo asake daura miki wani ruwan,"
" to ' kawai umma tace, doctor yafice, Nisha matsowa tayi ta taimakawa umma ta sakko daga gadon ta rakata har toilet, adaddafe umma tayi alwala kasance wa jikin bawani kwari sosae yayiba taurin zuciyane irin na umma, seda takammala alwala tafito Nisha na ganin fitowar ta yasa tashiga taimaka mata wajan fitowar ta maida ta gado tareda sanya mata hijab, azaune tayi sallanta yayinda Nisha kuma ta kura mata ido tana kallonta, tana jin wani dadi yana ziyartar zuciyar ta, bayan umma ta idar da sallah tamaida kallonta ga nisha data tsareta da ido ta fada kogin tunani, murmushi umma tasake ganin yanda nisha ke kallonta, tasuwa nisha tayi tazauna kusa da umma tana murmushi, awannan dare Nisha sunyi hira da umma sosae kamar baza arabuba, haka har bacci barawo yasacesu, can cikin dare nurse tashigo takarawa umma ruwa, kallon su nurse din take gwanin shaawa hannayensu cikin najuna se sharar baccinsu suke hankali kwance, seda ta kammala abunda take tajuya tafita,
__________________________________
wajan 6:30 nisha tafarka tabude ido gari yayi haske hakan yabata daman mikewa tana kallon ruwanda aka daurawa umma , ahankali yake tafiya bayida alamar karewa yanxu, toilet tanufa tayi alwala tafito, tashin fida sallayan da salma takawo musu, ba karamin tai mako salma tayiba da yanzu haka zata sake fita aron sallaya har ace kwadayi ke kaita, gabatar da sallanta tayi, bayan ta idar tacigaba da lazimi tana addu'a, tana kammala wa, ta ninke sallayan tamike tanufi gurin umma tazauna daga gefe, tayi tunani tashin umma tayi sallah se wata zuciyar ta hanata hakan, tsagaita wa tayi taga ko umma zata farka amma shiru babu alamar zata farka, ganin haka yasa Nisha tashiga tashin umma tana fadin,"
Umma! Umma!! Kitashi garifa ya waye, gabantane yafidi ganin ba alamar zata bude ido duk da jijjigata da takeyi, nan tashiga kokarin dagota but seji tayi ta dagota asandare, hanu tasa ta dago na umma, se kuma tasake da sauri tana bin umma da kallo, shigowar nurse din ne yasa Nisha tamike dasauri tanufi nurse din tana faɗin,
" please kidumin umma na ki tabbatar min da hasashena karyane ba gaskiya ba tafada cikin sigan kuka, jin abunda Nisha ke faɗi yasa nurse din tayi saurin matsawa gadon umma tashiga dubata, babu alamar motsi ko numfashi atareda ita idonta kuma dama arufe yake, to itamade bazata iya cewa komai ba seta kira doctor, dan haka ta kalli nisha dake ta sharbar kuka tace,"
I'm sorry..... bata jira mai nurse ɗin zata sake fadɗa ba tasake wani kukan tana faɗin,
"Innalillahi wa'inailaihi raju'un tafadi tareda kokarin fita waje, nurse dince taja hanun ta tana kokarin lallashinta da ta kwantarda hankali amma inaa tafizge hanunta tayi waje da gudu bakinta nafadin,"
Doctor
*****____________'_''''''________________*****
Tafiya yake cikin natsuwa warsa na setin kunnansa da alama amsa kira yake, kyakykyawa matashi maijin kanshi inka soma kalloshi bazaka so dauke ido kanshiba, yana sanye cikin kyakykyawar shire mai daukan hankali, ahankali yake mutsa pink lips dinshi yayin maganar ko wanda ke kusa dashi ba lalle yaji abunda yake faɗi ba, because slowly yake maganar kansa na kasa baiyi auneba gab yaji sunyi karo da mutum, cikin hanzari ya rikota ganin tana kokarin faduwa, hankali ya ware sexy eyes dinshi yasuma bin yarinyar dake rike da ita da kallo, itama waro idonta tayi dasuka kankance sun kumbura saboda kuka, cikin rawar jiki tasuma janye jikinta daga nashi tana kokarin yin baya,
shikuwa jin tana kokarin zamewa yasashi sake rikota da kyau, jitake numfashinta na sama sama zuciyar ta se wani irin bugu take, shi kanshi yana jiyu yanda heart beat dinta ke bugawa da sauri sauri, gani yayi ta bude baki da nufin magana, se kuma yaga tarufe ido ta sake masa nauyin jikinta, alamar da tabashi tabbacin suma tayi, nurse din data biyo bayanta ne takariso da sauri ta suma kokarin tallafo ta, su Hajiya dake ciki suka jiyu ihu yasa suka fito da hanzari dan suga abunda ke faruwa, reedace ta taimakawa nurse din suka ciccibi nisha akayi wani room da ita, suma su hajiyan suka rufa musu baya domin jin ba asin ihunda take,
tsayawa yayi yana ganin ikon Allah danshi atunanin shi yarinyar tabin hankali gareta jin yanda take ihu, kamar mai tabin hankali, duk tabi tacikawa mutane hospital da ihu, wani guntun tsaki yaja yana binsu Hajiya da kallo dasuka rufa musu baya sunata rawar jiki, tabe baki yayi tareda shigewa cikin room din da dansa yake kwance, akwance yaron yake saman cinyar mom dinsa ganin papanshi yasa kokarin mikewa zaune Yana washe baki, karisawa yayi kusa da son din nasa yayi tareda sakin murmushi wacce takarawa face din nasa kyau, yana faɗin,"
My little boss ya jikin naka,? I hope everything is going well ,? gyada kai yaron yayi cike da farin cikin ganin papanshi,
"Alright do you need something? papan nashi yakuma tambayarshii yana kallon dan nasa,
"no papah "
"Okay " abunda yace kenan yamaida kansa ga wayarsa yashiga matsawa, tunda yashigo yazauna suka suma magana da son ɗin nashi baidago kai ya kalletaba kamar baisan da zaman mutu awayan ba, kamar tayi maganaba sekuma tamike tana fadin,
" tunda ka iso bari nasamu natafi gd nayi wanka nawuce office , kazauna dashi kafin wadancan su dawo daga gulmar da suka tafi" wani banzan kallo ya wurgeta dashi yana fadin,"you well not going anywhere
seat down and care him nan kuma yamaida kallonsa ga yaron yana faɗin,
" zan tafi but letter I'm come back gyada masa kai yaron yayi yana faɗin
"To papah" ko kallon ta batayiba yajuya yafita abunsa, itama wani guntun tsaki taja tareda neman seat tazauna, *******Nisha*************
bangaran Nisha suma take tana farfaduwa tana surutai tana kiran sunan umma, su Hajiya kuwa kallonta suke cike da tausayawa, Nisha gaba daya bata cikin hankalinta, cikin asibitin akayiwa umma sitira aka mikata gdnta nagaskiya, Hajiya ce tasa aka shirya komai, kwanan Nisha biyu bata san inda kanta yakeba, se surutai taketa faman yi kamar wacce tayi karamin hauka, tunda doctor yashigo yamata allura bata sake tashiba se washe, se gurin yamma tasuma kokarin bude ido, ahankali take bude idon harta budeshi tar bin kowannesu da kallo Nisha keyi tana dan zazzare ido tana kuma maibin dakin da kallo, jitake kamar abun a mafarki, wai dagaske umma tafiya tayi tabarni, ? ido suka zuba mata cikin tausayawa jin sun batunda take, salmace takarisu tarike hannayenta tana faɗin
"kiyi hakuri Nisha duk mairai mamacine muma wata rana bama raye addu'a take bukata agareki ba kuka ba, please kiyi hakuri" Nisha binta tayi daga kallo sekuma tafashe da kuka tareda fadawa saman cinyar salma tana faɗin,
"salma wai dagaske umma rasuwa tayi salma jiyafa kwana mukayi da umma muna fira, yanzu awayi gari babu ita, salma kikaini gurin umma doctor yasake dubata bata mutuba nasan umma bazata tafi tabarni ba" tafaɗa cikin sigan kuka maiban tausayi, kokarin turo kofar da akayine yasa Nisha tamike dasauri tanufi kofar tana fadin,
" doctor um.ma . , sekuma tabi ta tsaya cak kafarta yadau bari kamar mazari, tana neman faduwa, ganin haka yasa hajiya tamike da kanta ta janyo Nisha jikinta takwantar, bin yarinyar yayi da kallo da bakaramin kuluwa yasumayi da yarinyar ba, duk yanda akayi brain dinta da matsala, dan karamin tsaki yaja tareda maida kallonsa ga dansa aheel dake kwance cinyar fareeda ganin yayan nasu yasa tazame aheel daga cinyarta takoma gefe indasu Hajiya suke,
matsawa yayi yamaida aheel nasa cinyar yana mai shafo gashin kansa yayinda yake baccinsa, shawaran Hajiya da tabukaci hada aheel da Nisha room daya because Nisha ba kowa kusa da ita dan haka ahadasu tare kodan susamu daman kula dasu duka,
"Hajiya anbamu sallama so zamu iya tafiya, yafaɗi batareda yakalli indasu keba,"
" eh haka nasani sunake yarinyar nan tadan koma dede inyaso mutafi da ita, kasanfa batada kowa kusa da ita mahaifiyar ta tarasu kar kewa yamata yawa, " sake baki yayi yana kallon karfin hali irin na kakar tasu, daman yasan za arina hakan duba da yanda suke wani shishshige mata,
' basusun yarinyar daga ina takeba basusan komai akantaba kuma ace za adauketa akawota cikin family' girgiza kai yayi ba tareda yasa yace komai ba yacigaba da abunda ke gabanshi gamida tabe baki ba tare da daya sake cewa komai ba, maida kallonsa yayi ga ɗan nasa Aheel da haryanzu baccinsa yake, mikewa yayi yasuma kokarin fita daidai lokacin da salma tashigo da Doctor dumin duba nisha cike da tabe baki yawuce yayi gaba abunsa,
Dubata yayi sosae yasanar dasu zata iya farkawa koda yaushe, dan haka za aiya sallamansu bawata matsala, bayan farkawarta kamar yanda doctor yafada suka shiga tattara kayansu dan komawa gd, AJMAL kam tuni yayi gaba da dansa dan haka suma suka shiga shirye shiryen bin bayansu, Nisha kam ba abunda take se kuka, duk inda akayi da ita nan takebi domin kuwa batada inda zata rabe, Hajiyace tarokota tashigarda ita mota, salma nata faman bata baki da tabar kukan haka tayi hakuri tabar komai agurin Allah, tamika lamurnta gareshi, sai da ta tabbatarda tarage kukan sannan sukayi sallama tareda alkawarta mata gobe zatazo inda take, sunyi musayar number da fareeda zata kirata,
Wani kuka Nisha tashiga yi ahaka suka rabu da salma, gaba daya jikin salma yayi sanyi duk taji babu dadi allah sarki umma mutuwa meraba tsakanin da da uwa, tafiya suke yayinda Hajiya tareke Nisha tsam ajikinta yarinyar tashiga ranta ga tausayi na rashin uwa, tabbas karasa duk wata madafa arayuwa, tanajin yarinyar kwarai ajikinta ba ita kadaibama hattasu reeda domin kuwa Nisha yarinyace maishiga zuciya, motarsuce ta kunna kai cikin wani gd na alfarma, nagani Nafada, hon dinda akayine yasa mai gadi yaye geat din gdn, shiga sukayi tareda yin parking ainda ake adana motocin, fito da ita Hajiya tayi ta dangana da ita izuwa cikin gdn, tunda suka shigo nisha taketa karewa gdn kallo masha Allah gdn ya hadu sosae gawasu shuke shuke masu daukan ido da jan hankali 😌 kaida kaga gdn kasan ba irin tsarin gdnmu na nigeria bane, gaba daya kirjinta sewani irin bugu yake, murmushi Hajiyan ke bin Nisha dashi yayinda take karewa gdn kallo, parlour suka nufa yayinda su fareeda ke biye dasu, wani lallausan capet data taka yasata lumshe ido hadeda bin parlourn da kallo, ya Salam aljanar duniya parlourn ya hadu iya hadu kuma ya tsaro, gaskiya an narkawa gdn kudi sosai ba karya , zaunar da ita tayi a lallausar kujeran sannan ta kallisu fadeela tace,
" kukaita bedroom ta watsa ruwa ta huta, basu jira takarisa maganar ba kamar jira suke fareeda taja hanunta sukayi ciki, toilet ta nuna mata hade da mika mata towel nan ta karba tareda shigewa tamaida kofar tarufe, kallon toilet din tafarayi tana bin ko ina da kallo, toilet ma kaide aka barka dashi abun kallone, to ni yanxu ta ina nasan zan fara, wasu ma dannai kurawa wajan ido tayi sekuma tasa hanu ta danna daya daga cikin madannin , shaa kaji ruwa me bala'in sanyi yazubu mata, bakaramin kidima da tsoro tayiba, hakan yasa tafito dagudu tana salati, juyowa sukayi gaba dayansu suna kallonta, jikinta se rawa yake ruwa se diga yake daga fiskarta, reeda ne tamatso tana tambayanta lapia kuwa,? shiru Nisha taimata , jin karan ruwa nazuba hakan yabawa reeda daman lekawa toilet din tagani, shower ta kuna ga power ruwa se zuba yake, sekuma tamaida kallonta ga nisha taketa wutsi wutsi da eyes cike da kunya, murmushi reeda tayi tareda jan hanun Nisha , nuna mata tayi duk yanda abubuwan toilet dinsuke da yanda zatayi amfani dasu,
" nagode" abunda Nisha tace kenan, fitowa tayi domin bawa Nisha waje tayi wankan, wanka tayi sosae taji dadin jikinta tana jin wani nutsuwa na ziyartar ta wanka rahamane, fitowa tayi daga toilet din ga mamakinta bata gakowa adakinba alaman sunfita daga dakin kenan, wani duguwar riga tagani asaman bed din da alamar ita aka ajiyewa dan tasan batazo da wani kaya in gantacceba, dan haka ko inda mai yake bata nemaba tashiga sa kayan, ya zauna damas ajikinta sede dan matseta da yayi kadan kasan cewan tadan fisu jiki kadan , kallon kanta tayi amadubi kayan ya amshi jikinta yayi mata kyau sosai abunka da kyakykyawar mace, waje tasamu daga bakin gadon tana karewa dakin kallo, shiru tadanyi na wani lokaci se kuma tunanin umma ya fado mata , kuka tafashe shi tareda nitsa kanta afilo tana kuka tana fadin," ina ma ace marki take duk abubuwan dasuke faruwa ayanzu mafarkine ba gaskiya ba,
***** Wacece Nisha da kuma labarinta*******
Aishatu Hashim yarima
Yace ga Alh Hashim yan asalin kasar sudan mahaifinta da mahaifiyar ta tushensu kenan, kasuwanci ya kawoshi nigeria yankin adamawa, cikin garin adamawa aka haifi Nisha, ita kadai Allah ya mallaka musu matsayin ya, dan haka suka dauki son duniya suka daura mata, sunsata makaranta mai inganci boko da arabic, suna kulawa da ita sosae ba abunda ta nema tarasa, duk abunda takeso shi akeyi, har Allah yasa kasuwancinsa yakara bun kasa yazama babban dan kasuwa, yazama babban mutum Allah yarufa masa asiri ya daukakashi, kasan cewan shikaru gaba suke girma na kara bayyana, Alh Hashim ya damu da rashin haihuwar matarshi Hajiya Zainab mahaifiyar nisha da batayiba, tun haihuwar Nisha bata sake ku bariba, tabbas ba abunda yafi bukata ayanzu da yawuce haihuwa, kuma da namiji atunanishi yasamu magaji wajan kasuwanci, saboda kullum shekaru ja suke girma na karuwa, Alh Hashim mutumne maison tara zuri'a sunyi addu'a sunyi magani gd da asibiti amma shiru ku alaman batan wata babu, shikuwa kullum maganar da bata wuce na haihuwa, abun harya fara bawa Hajiya Zainab haushi da ita take bawa kanta haihuwa da tabasu, gdnsu se yacika da yara amma abun na allahne ba yadda zasuyi, nanfa yafara neman shawaran abokan arziki to abunka da shawaran namiji bai wuce aureba, tabbas baiyi niyan kara aureba kuma bayida ra ayin karawa to amma ba yanda zaiyi tunda yana da bukatan yara, koda aka bashi shawaran kara auran ya kasa tin karar matar sa da maganar, to abunka da mace mai tunani tuni tagane inda yadosa, dan haka tasamishi da maganar dacewa,
" idanaure yakeson yi ya sanar da ita ba hanashi zatayiba, allah yabashi ikon auran mata 4 ita bata isa ta hanshi abunda allah ya halasta masa, yadena wani buye buye, amma abunda takeso ya fahimta shine karin auransa bashine zaisa yasamu abunda yake bukata ikon Allah ne, inda ya daya rubuta zamu rayu tofa wanda ya isa yacanza hakan"
Tudae Alh Hashim yayi auransa kamar yanda tabashi dama, ya auri Hajiya Fatima zan kadedeyar bazawa gogagiya mai idanu atsakarka, bazama yakawotaba zaman jiri taxoyi kamar yadda tasaba ga sauran gdn da tafito, da zaran tasamu abunda takeso zata cikawa rigarta iska, to dan haka ba kansa farauba balle takare kansa, yanzu shekaransu wajan biyu knn, amma babu alamar ciki, itadae inbanda cin kudi ba abunda tasa gaba domin Alh Hashim bakaramin sake mata bakin aljuhu yayiba domin shi mutumne da hanunsa asake yake, amma ganin Hajiya Fatima babu alamar ciki atareda ita nanfa yafara mitarsa yanda yasaba akan haihuwa, tana jinsa zai karaci surutun sa bazata tamka masaba, dan ita tasan zamanda take dan ita tariga da tasan bazata sake haihuwa ba, ma haifartama ba aiki takeba, ita atunanin ta arziki tazuci ba haihuwa ba, dan haka yafara sheda mata shi aure zai kara tunda ita bata haihuwa,
Tunda taga haka tasawa ranta ba wacce zatazo ta tayata cin dukiyar nan , matarsa tafarkoma bayanda ta iya tazu ta sametane, amma itama tasan yanda zatayi da ita , da kafar Alh Hashim akace yaje gdn matarsa Zainab bazai iyaba, kawarta takira ta sanar da ita abunda yake wakana, tace mata karta damu zatazo akwai inda zasuje inda bukatansu zata biya, tana zuwa ta dauketa ba inda ta zame da ita se wajan boka wanda itama Hajiya Fatima bokan ba wani bako bane agurinta,
"me kukeso amuku dan nasan abunda ke tafe daku kafin zuwanku naji bayanin komai kasheta kukeson ayi,?
"Aa boka kawai sunake su wulakanta ma ana banaso Alh Hashim yakara tuna yanda wata mata kowata ya aduniyar nan, nikawai nakeso yagani nazama abar tunawarsa, duk duniya yaji baya son wata mace inbaniba, kuma wannan zance na aure yafita abakinsa ya manta maganar,"
"Angama bukatarki tabiya, duk wasu kasuwanci dayake da wasu kadaruri duk zasu koma hanunki, seyanda kikayi dashi, mai kikace yayi darawar jiki zai mikishi, "
"godiya nake boka,"
" to ammafa kafin aiki yacika zaki kawo gurguwar sauro da jan taure,"
" kai boka ina zamu samu wayan nan kuma"
"Sai ku ka wo kudi boka dan kundalo zaisiyo se ayi aikin, "
kudi masu kauri Hajiya Fatima tabayar suka tafi,
Dan adam da saurin yadda tabbas abunda sukayi yayi tasiri dan tundaga wannan ranar Alh Hashim bai kara taka indasu Nisha sukeba, baya zuwa balle ya aiko muda wani abu, mami dadi kamar matsata mutuba, duk abunda ya mallaka aduniya seda tasa ya mallaka mata shi, rashin zuwan Alh Hashim tun baya damun Hajiya Zainab harya fara damunta, dan haka seta fara tura Nisha gdn mami tadubu matashi, amma kullum Nisha taje se ace mata baya nan, shirun yayi yawa dan haka tasa Nisha agaba har gdn mami amma abunda tacewa Nisha shita sake maimaitawa Hajiya Zainab, to wai ina yake zuwane ko lekomu bayayi umma ta tambaya, mami hararo Zainab tayi tana fadin
," to ni ina zan sani, ki nemeshi kitan bayeshi mana , koku tsaya kujira yadawo, " mami tafada tareda juyawa tayi daki tabarsu awajen suna tsaye, daga cikin dakin suka jiyu muryanta tana fadin,
" in kungaji da tsayuwar se ku seta hanya kuma karku sake kutafi kubarmin kofa ashigo amin barna," komawa gda sukayi kowa jiki babu dadi, tundaga wannan ranar umma ta kwanta ciyo da kuma tunanin mijinta, haka umma ke kwance yau da lapia gobe babu, duk wani kayan abincinsu seda ya kare, wani lokacin salma ke kawo musu abinci daga gdnsu, ga rashin lapia kullum gaba yake, ta dau tsawon lokaci tana ciyo Amma wannan karan ciyon baizuwa umma da wasaba balle susa ran samun sauki, Nisha ba yanda batayiba da umma batun zuwa asibiti tunda kullum ciyon gaba gaba yake har yaci karfinta amma inaa umma taki itade damuwarta tasa mijinta aidonta, dan haka kallum maganar umma Nisha ta nemu mata abba,
"yauma kamar kullum sassafe Nisha tayi gdn mami dan ganin abbanta, azatunta zata sameshi tunda yau tayi sammako, amma sam yauma batayi sa'a ba, dan kuwa bata sameshiba,
"to waini ina abba ke zuwane kullum baya nan Nisha ke tambayar mami, cikida fusata mami tace,
" to ko zaki matse baki nane inyaso sena fada miki inda yake zuwa,"
" Allah yabaki hkr ummace ba lapia inaso nakaita asibiti, kuma ba komai ahanunmu yanxu, "
"to shine meye kina fadaminne koni zan bata lapia,? ko alhakin kaita asibiti awuyana yake,"
" Aa abba nake nema infada masa abunda yake faruwa, "
""to sekije kinemesa aduniya",
"zan zauna na jirasa komai dare zai dawo ae" Nisha tafada tareda neman guri daga gefe ta zuguna,
" mara kunyar yarinya seki zauna kijirashi ae iskane yake wahalarda mai kayan kara, "Nisha binta tayi da kallo yayinda mamin ke shiga daki tana mai bushewa da dariya , tana shiga dakin tazari phone dinta tanufi toilet can ciki tashiga tadanna layin kawarta takira, dagawa tayi tana fadin,
" yade Hajiya fty shekewa da dariya mami tayi tana fadin,
" gsky aikin boka na kyaufa",
"aidama nafada miki boka baya wasa, meyafaru najiki cikin farin cikine,"
" ke yanzu Nisha tazu tana neman mahaifinta wai ummanta ba lapia," cikin shekewa da dariyan mugunta tace
"yanxu haka tana cikin tsakanin rayuwa da mutuwa ," dariya kawar ta fashe dashi tana fadin,
"haka akeso ae suta mutuwa suna bamu waje, to yanzu ba tsayawa zakiyiba, buriki bai gama cigaba, kinsanfa Alh Hashim ya mallaka miki gdnsu dasuke zaune, dan haka kiyi gaggawan karban gdnki, kafin su saida kayan ciki suyi kudin magani",
"kumafa hakane kawata kin kawo shawara mami tafada tana jimami, shiyasa nakeyinki bakya wasa,"
" ato tsaya kallon ruwa kwado yamiki kafa, to yanzu ina Nishan take, "cikin yamutsa fiska mami tace,
" gatacan wai tana jiran abbanta yadawo,"
" aiko bazata ganshiba kibarta kawai inta gaji zata tafi dan kanta, dan bazata taba hada ido dashi ba, har abada, kuma kema karki sake da haka kinsan abunda boka yafada," cikin jan numfashi mami tace
"hakanefa ai bazan taba barin hakan tafaruba, to yanzu kibari inta tafi kibi bayanta kiyi hayan kartan maza kuje dasu ku kwashe kayansu tas ku cillasu titi, susan inda dare yamusu, "
"kai haka za aiyi kawata nagode sosae," da haka sukayi sallama farin ciki fal Hajiya fty,
**Nisha
tun safe haryanzu yamma lis amma sam babu alamar zaidawo, ga tunanin umma wani hali take ciki, gawani hadari da ya lullube garin har ansuma yayyafi, dan haka ta tashi tafita, daga window mami tabi bayan Nisha da kallo tana dariya, mtswww yan wahala zaku gaji kubari, to atakaice dai wannan ciyo da yamatsan tawa umma da rashin ganin mijinta shiya kaita ga kwanciya asibiti har Allah yakarbi rayuwarta, wannan kenan
Cigaban labarin, seda tayi kukan ya isheta sannan ta mike ta wanko fiskarta, fitowa parlourn tayi itama nanma ba kowa parlourn kallon parlourn take gwanin shaawa, jin motsi cikin parlourn yasa tajuya inda taji motsin, wata matace dagani tadan manyanta tafito daga kitchen hanunta dauke da filet din abinci tana jeresu a dining table ganin Nisha yasa matan tasaki murmushi tareda karisowa inda Nisha ke tsaye, tana fadin," yade yata akwai abunda kikesone,? cikin tsoro Nisha tace," am ., banga kowa a parlourn bane, ko su fadeela kike nema,? cikin hanzari Nisha tace,"eh , suna part din Hajiya muje innuna miki inda suke, har bangaran Hajiyar ta rakata tabude mata kofar sannan tajuya, shiga Nisha tayi hade da sallama, fadeela ne ta taso tana fadin," lah mundauka bacci zakiyi da kikayi wankan shiyasa muka fito muka baki guri kihuta, cikin wani irin murmushi nisha tace," nakwanta baccinne baizoba, murmushi Hajiya tayi tana adin," matsunan kizauna kusa dani yaranne se ahankali suntafi sunbarki kikade
murmushi nisha tayi tareda da matsawa inda Hajiya tamata nuni, hira suka cigaba da yayi suna janta da tadi amma sam bata wani sake sosae ba, hjy duk tana kula da yanayinta ba karamin tausayin yarinyar takeba, yarinyar irin wannan da rashin uwa bawani makusanci kusa da ita, itadae Nisha gaba daya hankalinta ya tattara ga aheel dake kwance yana bacci, kyakykyawa kamar bababsa haka kawai takejin yaron cikin ranta, kiran sallan magarib ne ya dakatar dasu daga firan dasuke, duk suka mike toilet din hajja mama kowannesu ya nufa yayi alwala, itama tashi tayi tanufi toilet din tayi alwalan koda tafito bataga su fareedan ba, da alamu sun nufi part dinsu sallah, .
hajja mama ce daga gefe kan sallaya tana gabatar da sallah hakan yabawa Nisha daman matsawa inda taga an ajiye mata lufaya da sallaya, gefe da hajja mama nisha ta shimfida sallayan tashiga gabatar da nata sallan, bayan kammalawar hajja mama tashiga lazimi tana jan jarbi, yayinda idonta kekan Nisha dake gabatar da sallah cikeda nitsuwa murmushi Hajiya tayi yayinda tamai hankalinta ga abunda takeyi, bayan idarwa nisha tajima tanayiwa umma addu'a da ftn alkhari da samun rahama ga ubangijinta, tareda mahaifin nata dan shima ako ina yake yana bukatar addu'an ta gareshi, tana kammalawa tamike tareda ninke sallayan , mike hajja mma tayi daga zaman da take tana fadin,
" bari naje na dubo baba Barka ko ta kammala dinner dan yuwa nakeji sosae gyada mata kai kawai Nisha tayi hakan yabawa hajja mma Daman ficewa, aheel dake kwance saman capet anmasa matashi da pillow Nisha takurawa ido tana kallonsa, sam bata gajiya da kallonsa, yaro so beautiful wani dan larabawa, gsky family din Allah yabasu kyau masha Allah, murza idonshi yashigayi alamar farkawa daga bisani yabude idon gaba 2 , ya saukeshi akan Nisha da ta kura masa ido kamar zata hadiyeshi, kallon rashin sani yafara mata, cikin wara ido da tsoro yake fadin,' who.., who are you yafada cikin muryan bacci, Nisha kasa mayarmasa da amsa tayi dan ita kanta ba san mezata ce masa ba, maryan shi tasakeji yana fadin
"Zansha ruwa "
zamuwa tayi daga kujeran da take tasa hanu ta dauki ruwan dake gefensa tareda cup din tashiga tsiyaya masa ruwan ta mika masa , ganin ya miko mata hanun hagu because dayan hanunsa da matsala hakan yasa ta tallafo shi tashiga bashi da hanunta , karba yayi yasuma sha seda ta tabbatar ya koshi ta zame cup din daga bakinsa tareda sakar masa marshi, shima washe mata baki yayi yana fadin,
" thanks you" baki Nisha tabude da nufin magana jin shigowar fadeela ya tahadiye talk dinta, ganin su zaune saman capet sunyi zuru suna kallota hakan yabata daman karisuwa inda suke, murmushi tasakar musu tareda mayar da kallonta,
" my little baby katashine " gyada mata kai yayi yana fadin',
" aunty I'm feeling hungry ,
"okay don't worry zan turo baba Barka tazo tayi feeding dinka kajiko to kawai yace nan tamaida kallonta ga Nisha tareda jan hanunta tana fadin,
" muje muci abinci dama ke nazo kira , sunkuyar dakai nisha tayi tareda cewa,
" bana jin yunwa, cikin hanzari fadeela tace,
" Allah baki isaba taya zakice bakya jin yunwa, dagaske kwata kwata babu yunwa atare dani, kodae bakyason cin abincin damune, mudakefa munriga munzama daya fadeela tafada tareda jan hanun Nisha harsun kai kofa Nisha taja ta tsaya takalli dayayi abun tausayi yana binsu da kallo sekuma takalli fadeela tace,
" please to kikawomin nan semu zauna tareda shi kar abarshi shikadai,
" nafahimci kifi bukatan Zama nan , alright bari na turo muku Barka, " tafada tareda juyawa tafita, murmushi tabi bayan fadeela dashi, gefe kuma tamaida kallonta ga aheel, kumawa tayi tamatsa kusa dashi tazauna, tana maibinsa da murmushi jin yaron take sosae ajikinta, sekace wanda suka fito ciki daya, Nisha uwar yaya tana mutukar son yara dan koda suke gd faruk kanin salma tare suke wuni tana manne dashi darene kawai ke maidashi gdnsu, ita kade Allah yabawa mahaifanta batada yaya ko kani, shiyasa Allah yadaura mata jaraban son yaya, shima aheel din murmushi yaketa zuba mata kamar gonar auduga, yaron akwai fara' a sosae shiyasa yakeda shiga rai,
ba adadeba Barka tashigo hanunta dauke da tiredin abinci zubawa Nisha tayi afilet tamika mata, tuwone miyan egusi yaji kifi da nama kaca kaca , aheel kuwa irish da akwai aka suya mishi nan baba Barka tazana tana kokarin feeding din shi, lah da kimbarshi zan tayaki bashi kije ki huta kema, nisha tafada yayinda take kokarin dakatarda ita, aa yata karki damu bawani hutawan da zanyi aheel mutuminane gwara na sallameshi, daker Nisha ta lallabeta ta tashi tafita, filet din abincinta ta ture gefe ta kamo na aheel tasuma bashi, seda ta tabbatar da yaci sosae ya koshi sannan ta kyaleshi ta tsaya tana kallonshi ko abinci takasa ci, kwata kwata abinci baya ranta, muryan aheel taji yana fadin,
" aunty ke bakici abincin nakiba, am. banajin yunwane, to aunty kici kokadan because baba Barka ta iya abinci kema nasan zai miki Dadi, gyada masa kai tayi yayinda taja filet din abinci gabanta, nan tafara tsikaran abinci tanaci ba dan tana jin dadinsaba, sam bata ma gane dadinsaba, nan tunanin umma yafado mata nanfa hawaye yashiga wanke mata fiska jitake kamar ta fashe da ihu, sunnar da kanta tayi kasa dan kar aheel yagane halinda take ciki, guge hawayen tareda sake kasa da kanta tana cigaba da tsikaran abincin,
," aunty meye sunanki , da guwa tayi tana kallon aheel dayayi mata tambayar, murmushi yasakar masa tana fadin
" NEESHA Aunty nisha? yafada yana kallonta gyada masa kai , ina Zaki zauna damu anan koh kuma baza kitafiba tunda mummy na bata sun zama dani kezaki dinga feeling dina kimin wanka kishiryani cikin uniform natafi school? yafada yana washe baki, yaron akwai surutu balaifi kallonsa take yaro irin wannan da bai wuce 7 year's ba amma se surutai wani radio, a ido inka ganshi bazakace yana da surutu hakaba, koda yake Aunty's din nasama ba bayaba wajan magana, karka damu muna tare duk abunda kakeso zan maka kajiko tafada tareda da ture filet din abincin gefe, tareda yiwa aheel matashi da cinyarta, aheel hira tacigaba da yimata kamar dama can yasanta, kodama can aheel na saurin sabo da mutane, labarin papansa yashiga yimata, irin sonsa da yakeyi da kayan wasan da yake siyo masa , da wajan wasa da yake kaishi,
itadae Nisha kallon yaron take yayinda yaketa zuba makar fanfon da ya lalace, hira yake sekaceba majin yaciba, sam bakinsa bai mutuba, jin motsin shigowarsu hajja mma ne yasa Nisha daguwa suna binsu da kallo yayinda suke karisuwa , fareeda ne takariso wajansu tana fadin,
" yauwa yanata zuba sutun nasa daya saba ko wani labarin yake baki naketa jiyo sautin muryan sa daga waje ,
"lallai baki yabude sauki yasamu, washewa sukayi da dariya dukansu nanfa hira ya farke aka cigaba da tadi, tadi suke sosae wanda sundau tsawon lokaci suna yinsa , yanzu kam Nisha ta dan sake sosae anyi firan da ita, hajja mma data fahimci hakan ba karamin dadi tajiba, Hajiya bata wani dadi sosae ba wajan hiran ta mike taimusu seda safe domin kuwa bakaramin gajiya tayiba zaman asibiti ga ba bacci mai Dadi, gakuma dawainiyar aheel, sallama sukayi ta tafi tayi kwanciyarta, ba adadeba fareeda ma tamike saka makon wayanta dake ringing itama seda safe taimusu ta tafi, sunyi tadi sosai da fadeela sewajan karfe 10:30 lokacin bacci yafara cinye idon fadeela itama mikewa tayi tana fadin,
" Nisha kitashi muje mukwanta wlh bacci nakeji sosae, aheel baiyi bacci ba karmutafi mubarshi shikadai, rabu dashi papanshi zezo ya daukeshi ae ,
" aa kije kawai zan biyoki dan nima banajin baccin yanzu zamu danyi hira kadan, murmushi fadeela tayi tana fadin,
"naga kamar zama da aheel yana miki Dadi koh,
"hmm zaki gajima inde yaron nane surutain sama kadae ya isheki,
"aa nikam bawani isata dazaiyi, alright se kinshigo to, tafada tareda juyawa tafita, maida kallonta ga aheel tayi da ya tsura mata ido dan bayason ta tafi tabarshi,
"Aunty zanyi fitsari kikaini toilet , taimaka mishi tayi takaishi yayi fitsarin, ta dawo dashi tagyara masa kwanciyar tamasa matashi da cinyarta, suka cigaba da hirarsu wajen karfe 11: lokacin sunyi laushi daga shi har Nishan, domin kuwa bacci yafara cinye idon su, tuni aheel yasuma baccinsa nanfa itama tafara gyan gyadawa,
Motarsace ta kunno kai gdn , jin hon yasa mai gadi yaye geat din gdn, nan ya tako motar ya kariso haraban gdn yayinda yayi parking, mitowa yayi yayi da mai gadi yakarisu da hanzari yana mai kwasan gaisuwa, amsawa yayi tareda tafiya yakarisa ga part dinsa , nan yatura kofar yashiga back din hanusa yacillar kan kujeran, direct bedroom dinshi yanufa kokarin cire kayan jikinsa yasuma yi seda yacire yarege daga shi se dan short dress daga bisani ya dauke lallausan towel dinsa yanufi toilet, wanka yashiga yi sosae dan yau ba karamin gajiya yayiba , fitowa yayi jikinsa daure da towel iya gwiwa, kallon inda mai yake bai kalleba because wani kasala yakeji gakuma gajiya gaba daya yagama yin laushi, jallabiyarsa yazura tareda fitowa yanufi kitchen tareda hadu coffee yasamu gu daga dining yasamu waje yazauna yana sha, seda ya kammala yamike ya koma bedroom domin kwanciya ya hutawa ransa, kashe wutan dakin yayi tareda kwanciya saman bed din hade da janyo blanket yarufu, wayarsace tayi kara hakan yabashi daman lalubu phone din dan yaga waye meshirin shiga hakinsa acikin night haka, dago phone din yayi yana kallon screen din wayan , matarsace raheela ke tafaman kiransa komai zatace masa oho, wani tsaki yaja da kamar bai daukaba sekuma ya daga batareda yace komai ba,
" hey my baby yau nayi dare sosae gashi but ina ta missing dinka gakuma wani accident din da aka kawo yanzu, so bazan samu dawowa ba se zuwa tommorow, baijira takarisa maganar ba yakatse wayar tareda cillata gefe namaijan tsaki,
" stupid dama yau kika saba kwana hospital koba wani issue zakice akwai meye problem dina da hakan yafada tareda sake lullube jikinsa hade da rufe ido yana maida numfashi slowly, firgit yatashi yazauna se yanzu ya tunada aheel, gaba daya gajiya tasa ya mata dashi, da sauri yatashi yanufi hanyar waje, bangaran Hajiya yanufa tareda murda handle din kofar yajita abude take yakutsa kai, dauke da sallama, turus yayi yayinda yakarisa shigowa ciki, binsu yayi da kallo duk sunyi bacci Nisha ma baccin barawo yasaceta, kan aheel na cinyar ta , itakuwa ta jingina bayanta da jikin kujera, tanata sheka bacci, haunsu cikin najuna, Nisha tareke hanunshi gam, wani abu yaji yatukare masa makoshi , gaba daya haushin yarinyar yagama kamashi , datasan haushita dayakeji bata fara gigin kusantu dansaba, matsawa yayi ahankali yafara kokarin jan hanun aheel tareda cire hanunsa acikin na Nisha,
cikin bacci Nisha taji aheel na kokarin zare hanunsa hakan yasa takara rike hanun gam , kamar wani zai kwaceshi, gaba daya jiyayi ransa yafara bacci gani irin rikon da tayiwa dansa, hunsa yasa akan na Nisha yana yamutsa fiska, daya hanun kuma ana aheel yana kokarin raba han nayensu, jin tarike gam yasa afusace yafincike da karfi wanda yasa aheel mutsawa yana fadin,
" ah. Aunty hanuna yafada cikin nan nauyan bacci, yacigaba da bacci yana surutai, itakuwa jin aheel ya janya hanunsa yasa tasake jayo hanunsa ta rungume akirji, waro ido yayi yana bin hanusa da takamu takai kirji tanamai cigaba da baccinta, nanfa yafara kokarin jaye hanunsa jin haka yasa Nisha kokarin bude ido dayan hanunta tasa tana murza idonta, karfa idonta ya sauka akansa dake kokarin kwace hanusa daga nata kyansa ta zubawa ido wanda ta gagara dauke idon akansa, lumshe ido tayi tabude still tana rike da hand dinsa taki sakewa, ,
" hey madam samu dama kisakarmin hand na dauki dana yafada tareda hade gira, cikin hanzari takalli hand dinshi da tarike Gam sakuma tasake dasauri tana fadin,
" I'm sorry ta fad'i tareda mikewa tsaye , kauda kai yayi tareda daukan aheel yadaurashi saman shoulder dinsa suka nufi part dinsu, bayansa tabi da kallo jikinta se mazari yake sekace wanda taga wani dodo, cikin hantsari tabi bayanshi ta nufi bangaran su itama, tana shiga ta samu su fareeda duk sunyi nisa da bacci itama samun waje tayi takwanta dan idonta tuni yamata nauyi,**********
washe gari da asuba suka tashi sukayi sallah su farida suka koma bacci abunsu, qur'an Nisha ta dauka tasuma karatu kasa kasa take gudun karta shiga hakkinsu suna bacci ta dade tana karatu daga bisani ta dakata, addu'a tashigayi wa mahaifanta ita kanta sannan tashafa takoma tayi kwanciyar ta,
,sewajan karfe9:40 Nisha tafarka ganin babu kowa ita kade aka bari tanata sharar baccinta hakan yasa ta sakko daga bed din ahankali takarisa sakkowa, itama waje tanufa a parlour ta iskesu suna zaune, ahankali takarisa inda hajja mma take hadeda gaisheta amsawa tayi cike da fara'a tana fadin ,
"anishatu harkin koshi da baccinne tafada tareda kokarin dagata daga durkusawan datayi , cikin tsukuna fareeda tace,
" oh mubaza akulamuba hajja mma kawai aka sani, bude baki tayi daniyar magana nanfa hajja mma tace da ala kyalesu zumuje muci abinci ke muke jira daman tafada tareda jan hanun Nisha suka nufi dining table, time din baba Barka takammala komai ta ajiye inda yadace, fareeda ne ta bude abincin tashiga zubamusu, seda ta zubawa ko sannan ta koma tazauna domin fara ci, kuwa yashiga cin nasa banda Nisha datasa plate agaba tana juya spoon, tanason sake sa aheel aidonta, hajja mma duk tana duk tana kallon abunda take, yade nisha tunanin mekike,? cikin hanzari Nisha tadagu tana fadin,
" bakomai tana fadan haka tashiga tsikaran abincin tana ci, wayan fareeda ne yayi kara ta dauka cikin hanzari ganin mekiran , karawa tayi akunne tareda fadin,
" hello ammi ina kwana, daga daya ban garan ammi ta amsa da lapia, ya gd yasu Hajiya, qlu suke sede gd ba dadi muna miss dinki gsky fareeda tafada cike da shagwaba, fisge wayar fadeela tayi takara akunne tana fadin,
" ammi yaushe zaku dawo , ina daddy ,? kibashi wayan , daddyn ku baya kusa don't worry nanda 2 days zamu dawo, ammi tafa cikin sigan lallashi, yau to kuyi suri kidawo kiga new baby girl da muka miki fareeda ne ta kwace wayar dacewa,
" kuma ammi so beautiful inkika ganta zakiyi happy, ammi batayi mamakin maganar suba domin ta dade da jin labarin gurin Hajiya daga ita har Daddy sunsan zancen, to shikenan se mundawo din, daga Nisha har hajja mma kallonsu suke suna murmushi, sunyi fira sosai da amminsu daga bisani sukayi sallama yakatse wayar farin ciki fal zuciyoyinsu, suna kammala cin abincin suka koma cikin parlourn suka cigaba da firansu, sundau time suna hirarn daga bisani hajja mma takatse kiran dacewa,
" kun fasa fita shopping dine ko se rana tayi? cikin hanzari fadeela tace,"lah mun mance fira tayi dadi, lallai kam hira tayi dadi kutashi muje mushirya mutafi cewar fareeda duk suka mike, ganin ba alamar mikewar nisha yasa reeda taja hanunta tana fadin,
" dake zamu ae tashi mutafi tafada tareda jan hanunta izuwa ciki, hajja mma kam kallo kawai tabi bayansu dashi tareda mikewa tanufi bangaran ta , ba adadeba suka fito cikin shirinsu mekyau but koda suka fito basu tararda hajja mma a parlourn ba, hakan yasa suka bi bayanta domin yimata sallama, Nisha kam bata samu daman bin bayansuba daga waje tatsaya tana bin part din dataga AJEEMAL ya nufa da aheel tana karewa benen kallo , juyawa tayi danufin shiga part din Hajiya jin muryan aheel yasata dakatawa, da sauri ta daga kai takalli inda take jiyo muryan aheel, daga saman benan yake kwala mata Kira, Aunty see me yafada yayinda yake dago mata hanu yana dariya, washe masa baki tashigayi yayinda take daga masa nata hand din, daga sama take jiyoshi yana fadin,
" Aunty ina zakije,? kizu muyi tadi irin najiya yafada yana washe baki kamar gunar auduga, bata kaiga bashi amsaba su fareeda suka fito bada wani bata lokaciba fadeela taja hanun Nisha tana kokarin kutsata mota ganin haka yasa Nisha tayi hanzarin dagawa aheel hand batareda kowa ya luraba, shima hanun ya dagamata har suka bar harabar gdn aheel yna yiwa motar bye bye har seda mai gadi ya maida geat yarufe sannan ya tsagai ta, tafiya suke suna dan hiransu har suka su deden wani big plaza, shiga sukayi suka suma siyayyansu, nan sukashiga zagayawa domin zaban abunda yamusu tareda fadawa Nisha itama tashiga ta duba abunda yamata, amma sam itakam duk inda sukayi nan takeyi, ganin haka yasa suka shiga dauka mata duk wani abunda yadace na bukata, kama daga kayan sawa manya da kana , mayuka turare masu kamshi hada da kayan kwalliya shoes da sauransu, suyi shopping abubuwa da yawa reeda tabiya kudin suka tafi, kan hanyarsu na kumawa gd, Nisha ta sanar dasu akwai wasu kayanta datake da mukatan daukosu agdn da tabari, dake reedace driving dinsu tana tajiya kana motar Nisha tafada musu anguwar tareda bayani inda zatayi hanya yabulle dasu, ba dau time ba hanya takawosu anguwar,
nan sukayi parking daga gefe tareda fituwa daga motar suka nufi cikin gdn, azaune suka samu matar kusa da kofar dakinta tana tsintar shinkafa, dukawa sukayi tareda gaisheta cike da ladabi, amsawa tayi tana binsu da kallo dan ba wanda tasani acikinsu, se Nisha kadae, kallonsu tashiga yi daya bayan daya sannan ta sauke kanta akan Nisha tana fadin,
" Nisha kece, murmushi nisha tayi tana fadin," maman husna, ayya yakike ya karin hakuri kuma narashinda mukayi tunda samau labarin gurin ummyn salma ba karamin alhini muka shigaba, allahde yajikan Hajiya Zainab, ameen Nisha tafada tana maijin wani irin azuciyarta, nan Nisha tashiga zaiyanu mata dalilin zuwansu, bada wani bata lokaciba maman husna tamike suka nufi dakin da aka kallace kayan, nisha tashiga duba abuwanda yakeda bukata dakuma na ummanta wayanada zatana gani tana tunawa da ita, sanan Nisha ta fadawa maman husna data dauki sauran kayan intanada bukata tabar mata because batada ra' ayin, ba karamin murna tayi ba sbd taji dadi sosae, tashiga zubawa Nisha godiya hade da rakasu bakin kofa tajiyo,
nan sukuma suka shiga mota suka dauki hanyar gd, suna isowa mai gadi yaye geat din gdn suka shigo da motar sukayi parking, suka fito tareda kokarin shaga parlourn, tunda ga door din parlourn suka fahimci, sunyi bako, suna shiga ciki wa Nisha zata gani, Salam ce zaune bisa kujera tana sakar mata murmushi gefe kuwa hajja mama ce zaune tana kallon shigowar su, ledar hanunta tasake cikin murna tayi kana salma dagu tafada cikinta, nanda nan tafashe da kuka, cikin hanzari salma ta dagata nata fadin,
"uhm za afara sanar koh ? Wlh yanzu zakisa natashi natafi inda nafito dan ni banzu dan naji kukankiba, ciki hanzari Nisha tadago takallita hadeda bugeta kadan tana fadin,
" sorry bansan sanda kukan yazu bane tafada tana kokarin goge hawayenta tana tura baki kamar wata baby, dariya salma tayi tareda maida kallonta gasu fadeela da suke ta washe mata baki,
" ina kukaje haka naketa jiranku? Reeda tace wani dan shopping mukaje, to allah yasa anhadu da nawa shopping salma tafada tana dariya,
" tashi muje kigani, nan suka tashi suka bedroom dukansu sukabar hajja mma tana ta binsu da kallo gwanin shaawa, suna shiga dakin saman bed suka shigayi dad daya da kayan dasuka siyo suna nunawa salma,
" masha Allah kaya sunyi kyau sosai ga tsada, hakalin salma ba karamin kwantawa yayiba ganin Nisha tashiga hanun mutane kirki masu son mutane ba kyama balle girman kai, nan tashiga karewa dakin kallo gsky Nisha ba karamin sa' a tayiba ba karamin taya Nisha Happ tayiba ko bakomai damuwarta na rashin umma zai dan ragu,
salma kiga wata riga da aunty fareeda tazabamin, salma bin rigar tayi da kallo duguwar riga ce ash colour da rintsin baki baki, rigan ba karamin haduwa tayiba dagani zatayi tsada, gsky tayi kyau sosai fadan salma, reeda ne tayi yaddariya tace," ae dama ni na iya zaban abun mai kyau ba irin fadeela mezaben shirmeba tafada cike da tsukana, kallon fadeela sukayi da ta tura baki gaba tana kallon reeda yayinda take maganar dariya suka shiga mata, Salma tace," lallai kin iya kam dan gsky rigan tayi kyau sosai , thanks reeda tace tana fari da ido, sunyi fira sosai, kiran sallan azaharne ya dakatar dasu daga hiran kowannesu ya nufi toilet yin alwala, nan suka shinfida sallaya sukayi sallah, bayan sun idar , fadeela taja hanun Nisha suka nufi kitchen suna zuwa suka sami baba Barka takammala komai dan kwata kwata batar bata da ganda ga sauri wajan aiki nan da nan, fadeela ne tashiga shirya musu abincin seda ta kammala ta kalli baba Barka tace," yau a bedroom dinmu zamuyi lunch dan haka ki kaiwa Hajiya nata sa shinta, cikin hanzari baba Barka tace," to shikenan za akai mata, muje fadeela tafada tana kallon Nisha, itama Nisha kallonta tayi tana fadin, kije zanzo , gyada mata kai fadeela tayi tareda ficewa ta tafi, kallon Barka Nisha tayi tace ," ki hadamin abinci Hajiya nakai mata, " lah yata da kin bari yanzun nan zan hada nakai mata bada wani bata lokaciba, aa karki damu inaso nakai mata ne da kaina, bata mata wani musuba tashiga shirya mata abincin tareda mika mata, amsa Nisha tayi tajuya tafita, bangaran Hajiya tanufi ta murda handle din kofar tashiga, bata tarar da ita a parlour ba hakan ya tabbatar mata tana bedroom dinta, dire abincin tayi a table din dake parlourn, tanufi hanya dakin, murda handle din door din tayi hade da sallama kasa kasa, jin shiru yasa talekawa ahankali ta hango ta kwance saman sallaya hanunta rikeda carbi, da alama bacci ta sumayi, kamar ta ta suta sekuma tafasa tareda maida door din tarufe tanufi hanyar fita, tana fitowa harta nufi hanyar part dinsu, karaf ta hangi AJEEMAL dake kokarin fita jikinsa sayi da kana nan kaya sun amshi jikinsa sosai, ganin yanufi hayar geat mai gadi yabude masa yafita, wani hamdala tayi dan yau da son ganin yaron ta tashi duk da tasan cewa papansa ba nisa yayiba ganin bai dauki motaba, hakan yabata daman sidadewa bangaransa, takunna kaiciki, da sallama kasa kasa takarisa shiga ciki tana dan zazzare ido, akujera ta hango aheel na zaune ya tusa tv agaba yana kallo abincine gabansa amma wasa yake dashi hankalisa nakan kallon cartoon, yana ganinta yashiga washe mata baki yana kokarin tashi, karisuwa tayi kusa da kujeran sa ta rungume shi tana murmushi tareda sauke ajiyar zuciya, daguwa yayi yana kallonta ciki da dariya yana fadin," Aunty dazu ina kukaje kedasu Aunty farida, aheel shopping mugaje, papana yaganku ae, gabantane yadan fadi , hakan yasata mikewa tana fadin," bari natafi su fadeela suna jirana, letter are well come back, ga mamakinta yaro yasuma kokarin kuka yana make shoulder yana fadin," karta tafi tabarshi, ita kuma tsonta kar papanshi yashigo ya tarar da ita dan ta fahimci ba nisa yayi ba, jin kukan yake da gsk yasata matsawa tazauna tana fadin," shikenan bazan tafiba, nan tasuma bashi abincin abaki hanunta se bari yake, kallon shi tayi tana fadin," ina mom dinka, dazu mummy na tafita kuma bazata dawo ba se dare time din nayi bacci, cin shagwaba irin na yara yace,"Aunty mummy na bata son zama gd kusa dani, papa nane yake son zama dani har office dinsa yana zuwa dani, bakaramin tausayi yaron yaba Nisha ba , rashin kulawar mom disa atareda shi, da alama bata wani damu dashiba, muryan aheel taji yana fadin," papane yakemin wanka ya samin kaya yadafamin abinci, kallonsa kawai take yayinda yake zuba surutu, to kayi shiru ya isa haka ka karisa cin abincin, yanzu papanka zai dawo nima kuma ana jirana bari naje nan ta lallabe shi tafada tareda mikewa tayi tanufi hanyar fita, yayi daidai da time din da AJEEMAL ya kunno kai yana kokarin tura door din, idonsane ya sauka akan na Nisha hakan yasashi dakatawa yana binta da wani kallo, itama ganinshi datayi tsaye yasa taji kamar tasake fitsari awajan, tsabar tsorita, wani kallo yadinga binta dashi wanda yasa duk ilahirin jikinta ke bari, shikuwa bawata kallo bace da tawuce nacinda takewa dansa da shishshige masa datake wanda ba kaunar hakan yakeba, takaicine duk ya isheshi yarasama bakin magana, ita kuwa tarasa meyasa inta ganshi take nuna masa tsoronta afili kamar mara gsky, duk yanda takaiga danne tsoronta indan taganshi but takasa, because wani irin kwarjin yake mata, dukansu kowa ya gagara bawa dan uwansa hanya yashige, ita tana bakin door din shima haka, Nishane jitayi kafarta yamata nauyi tagagara ko mutsawa , muryan aheel ta tsin kaya dacewa,
" papa yace zaikaini wasa anjima zamuje tareko zaki rakamu.,? jiyowa tayi tana kallonsa tagagara basa amsa sedariyan yakenda bata san tana yinsaba maida kallonta ga AJMAL tayi da haryanzu wannan kallon yake binta dashi, still kuma yaki bata hanya tashige, daker ta iya matsawa baya kadan kanta sunkuye, wani harara ya wurga mata tareda jan karamin tsaki , shima tsayawar da yayi soyake yaga karshen rashin kunyarta na rashin kauce masa daga hanya da batayiba, ganin yashiga yasa tasamu damana fita cikin hanzari, aheel bin mahaifin tashi yayi da kallo, yanda ya hade gira yabata fiska, AJEEMAL kokarin shige aheel yayi daniyar shiga bedroom muryan dansane yatseshi dacewa,
" papa nagama cin abincin yafada yana kallon mahaifin nasa, cikin hanzari tajiyo batareda ya cemasa koamiba ya dauke plate din yakai kitchen yadawo yakalli aheel yana fadin,
" zanje nakwanta akwai abunda kakeso,? yafada cikin tsare gd, papa nima zanyi bacci kusa dakai, kamar zai daukeshi sekuma yafasa, yajawo hanun dan nasa yasauko daga kujeran , ahankali yake dingisa kafar hasuka isa bedroom, kwantar dashi yayi shima ya kwanta, domin yasamawa kansa saukin bacin randa yakeji, allah yagani kwata kwata bayaso Nisha ta kusanci aheel, gaba daya ransa baci yake inya gansu tare, gashi allah yayi dansa mai bala'in wayo da surutu allah kadae yasan mai yake gayamata insuna tare, gaba daya bakin aheel ba ba control, maida kallonsa yayi ga aheel daya tsura masa ido yana kallonsa, yaron magana yakesonyi but ganin mahaifinsa fiskarshi babu annuri yasa shi yin shuru, shikuwa AJEEMAL kallonda aheel yake masane yasa yace,
" bazakayi baccin bane kake kallona, lumshe ido aheel yayi daga bisani papansa yaja musu blanket yarufasu,
Nisha kuwa tana shiga part dinsu tasamu ita suke jira dan haka tasamu gu tazauna sukashiga fara cin abincin suna dan hiransu cikin nishadi, bayan la'asar salma tafara kokarin shirn tafiya gd, nan fareeda tasanar da ita wani birthday party dazasuje nawata friend dinsu , dan haka ta tsaya sutafi tare daga bisani sesu sauketa agd, haka kuwa akayi nan suka shiga shiri cikin riga da wando saman kuwa suka daura bakar riga, itama Nisha hakan suka sata tayi, fareeda taimata light makeup tafito tas da ita tayi kyau sosai, salma se kallonsu take yanda sukayi kyau dasu musamman Nisha kamar ba itaba, da itama kamar zatasa duguwar riganda reeda taba sekuma tafasa because seta nunawa ummynta, part din Hajiya suka nufa domin mata sallama, a parlour suka sameta zaune tanacin abincin da Nisha tazo ta ajiye mata, binso tayi da kallo daya bayan daya tana kare musu kallo, yan matan daddy sunyi kyau sosai, too wannan kwalliyarfa se ina, waje suka samu suka zauna suna kallonta , ina tambayar ku se ina, sun kuyar da kai nisha tayi tana jiran taji mai zasuce, cikin susa kai reeda tace
" am gdnsu fauziyya zamu yau take birthday, ba ranar munfada miki zatayi birthday ba ko kin mantane, aa ban saniba amma kusantu dazu kunfita da safe , AJMAL yanajin fitarku agdn nan haka yazo yasamene yana fadin fitarku yayi yawa kuncika yawo duk inda kukace zaku ninake barinku su ammi basusan shiga da fitar kuba, to kunga atakaice dai ninake daure muku gindi kenan ko,? to tunkafin ku saka ranku afitar nan gwara ku hakuri shi zaifi dan nasan zaku iya gamuwa dashi, kuma ba wanda zaije yayi mitar seni gwara ahakura da kitarnan kawai, parlourn ne yadau shiro kamar bakowa daga bisani fadeela tace,
" amma ko fauzee bazataji dadiba fareeda tace gskykam tafada tana kallon Hajj mama, kuma ae fitanda mukayi dazu ammi ne ta turo da kudi tace muje muyiwa Nisha shopping, to komade mainene kukirata kubata hakuri baza kusami zuwaba , kai bazai yiyuba shi waya takura masa haka damu zai takuramu reeda tafada tareda mikewa tsaye, cikin hanzari hajja mma tace,
" to rashin kunya zakimin, ko zaki ketare abunda tacene iyye, sbd kin isa ko shakararriya, jitayi kamar tayi kuka because sunsa ransu zuwa party nan, part dinsu tanufa suma suka rufa mata baya, yau murna ya komaciki, gaba dayansu samun waje sukayi suka zauna bawanda ya iya cewa da dan uwansa kala, salma kadan yarage dariya ta kubcemata, yanda take kallonsu fadeela bakinsu kamar zai taba bango, jin ana kokarin bude geat fareeda tamike cikin hanzari yayi labuleh window tana lekawa, AJEEMAL ne yafito hand dinsa cikin na aheel suka shiga mota mai gadi yamude masa geat yafita, wani wawan tsalle reeda tabuga cikeda murna tace,
" kaikuzu mutafi yanzu ya AJEEMAL yafita, part din Hajiya suka koma suka sanar da ita yayansu yafita hutawa dan Allah suma tabarsu suje su shakata, ganin yanda suka damu da fitar yasa ta kyalesu, da sharadin lallai su dawo kafin dawowarsa in har yadawo yafahimci basa nan tofa ba ruwanta, dan sunfita sanin koshi waye kuma sunsan halinsa, cin yanayi na murna da nisha di sukace inshallah allahu ma zai dawo ya tarar dasu agd, nan suka mata sallama sukayi gaba, tafiya suke suna hiransu cikeda nishadi, tsayawa sukayi daidai wani katon plaza suka shiga suka siya mata wani birthday cake mai hawa uku cake din yayi kyau sosai gwanin shaawa, suka hada mata da wani turare na kwali mekyau da kamshi ga kuma tsada, suka shige mata dashi, koda suka iso wajen sukayi parking motarsu a compound din wajan, tundaga arian wajan kakejin sautin kifa natashi koda suka karisa shiga Hall din, salma da Nisha suke karewa wajan kallo wajan ba karamin haduwa yayiba kaikace biki ake, ganin su farida da fauzee tayi yasa tayi kansu da gudu ta rungume su, ta mikawa salma da Nisha hand suka gaisa, ga fara'a ga kyau yarinyar balaifi, aina dauka baza kuzuba danaga time yaja da harnayi fushi, fauzee tafada tana kallonsu, kema kinsan ba abunda zai hanamu zuwa ae suka fada suna dariya, waje ta sama musu suka zauna daga bisani suka mika mata gift dinda suka taho mata dashi cikin murna da farin ciki ta karba tana fadin,
" thanks, kowani table ankewaye da kayan ciye ciye da makulashe, mazansu da matansu se shashewa ake ganin haka yasa fadeela da reeda suka mike suka shiga cikin yan rawar because yawanci classmates dinsune awajan, can Nisha taji bazata iya jure zama wajanba, ga wasu maza da suka zuba musu ido suna kallonsu musamman Nisha, ganin haka yasa Nisha tamike tana kokarin fita , yanaga kin mike salma tafada tana kallon Nisha, nagaji da zaman nan dinne ga kuma karan balonda yake fashewa, jirani nima salma tafada tareda rufa mata baya, su reeda kam basuma kula da fitansuba, hankalinsu yayi gaba, waje suka samu daga gefen Hall din suka zauna, suna ganin masu shiga da fita na wajan , ke dama inaso na tambayeki dama haka ya AJEEMAL din nasu yake, mekike ganin Nisha ta tambaya, yanada miskilanci kuma masifaffene, dariya Nisha ta tintsire da dariya tana fadin,
" gsky baki fahimce shiba mutumne da yatsa akasa masa abaki bazai cizaba, yanda kikasan kurmafa haka yake gsky banaje yacika surutu bama balle masifa dakikace, baeshida miskilanci de, amma de bansan mekika ganiba kikace hakan, to nide abunda idona yagani kenan kuma yayi agabana nagani, domin dazu danazo ban samekuba kunfita muna zaune da Hajiya yashigo yana surfa bala'in, wai ina kukaje, wlh mutumin nan kamar bazai amsaba nina daukama bai jinibane ashe yaji se masifa yake nida farkoma na dauka ko baban sune amma yanda nagansu zankada zankadan yan mata nace kai wannan bai kai ya haifesuba, allah seda nayi nadamar gaisheshi, dariya Nisha tashigayi tana fadin,
"tab waneshi ya haifi kamar wadan nan, boy dinsa daya aheel shima daya yakare dashi, nimade shinagani ganin masifar tayi yawane shiyasa nayi tunanin hakan salma tafada tareda sake fadin,
" ke tashi mukoma ciki kar su nememu surasa, mtswww wlh banason komawa cikin nan bare barensu yayi yawa Nisha tafara tana tsuke baki, daurewa zakiyi ae munkusa tafiya salma tafadi, harsun tashi zasu shiga me idonta rahila da wani matashin saurayi sunfito daga mota suna kokarin shiga cikin hotel din, idonta tarufe takuma budewa da sauri tareda murza idon da kyau tana binsu da kallo, salma ce ta dan bugeta kadan tana fadin,
" ke lafiyanki kuwa meye hakan,? kinta bin bayin allah da kallo kinsansune dakike kallonsu hk, ke nasanta mummyn aheel cefa dawani sekuma tayi shiru ko ba ita bace kam Nisha ke tambayan kanta, to mema zai kawota nan ita da take gun aiki, inga kamane ko nasaba gani, gsky kam kinsaba gani kam dan banga mezai kawo matar aure nanba, to meye ma naki aciki in itace mutafi muyi abunda ke gabanmu salma ta Fadi, tabbas abun yabawa Nisha mamaki dama ace batasan rahila bace se ace kama tagani ko kuskusne ganine, dan haka bawani batun kama itance,.
"kukuma mekukeyi anan munata nemanku aciki, please kudawo ciki fareeda tafada tareda juyawa, rufa mata baya Nisha da salma sumayi suka shiga ciki, , anci ansha yanda yakamata anyi rawa sosae gari yarufa magarib ya gabato kai, yanda suke ciki bawanda zaiyi tunanin magrib yayi, kowa dake wajan seda fauziyya ta taimasa kyauta mai kauri daga bisani akashiga watsewa, fituwar su fareeda keda wuya, sukaga gari yayi duhu, lokacin fadeela takalli agogon hanunta karfe 6:45 , ga miss call din hajja mma kaca kaca, nan suka shiga mota suka nufi hanyar gd , seda suka suke salma agd sukayi sallama, sannan suka wuce suma, reeda ta dannawa mai gadi hon, yabude musu suka shigo, tundaga nisa suka hango motar yayansu, dan haka sukayi parking motar suka fito, kota kan Hajiya basuyiba suka wuce part dinsu asukwane, kowannesu ahankali atashe banda Nisha da ahankali ta akwance yake, dan haka tanufi toilet tayi alwala tafito tayi sallah abunta, ganin haka yasa suma suka tashi sukayiyo alwalan sukayi sallah, bayan idar wansu kowa yasamu gu yazauna , kowannesu da abunda yake sakawa cikin ranshi, tunda suke basu taba kai dare awani wajeba se yau, duk fitanda suke arayuwar su, da zaran yamma tayi zasu nemi hanyar gd, sede infita yakama na family to shine ahankalinsu kwance, gashi yau sanadin fauziyya sunyi dare,
Nisha kam yau gaba daya abun kallo su reeda suka dawo mata, duk yanda suke da surutu amma yau shiru kamar basuba, ko wacce se zare ido take kamar tayi karya, jin ana turo door yasa suka kurawa kofar ido a tunanin su Hajiya kokuma yayansu, ganin Barka ce yasasu sauke wani goron numfashi, kufito kuci abinci anshirya komai baba Barka tafadi, dukansu bamaijin yunwa, dan ba karamin ciye ciye sukayiba awajan partyn, duk da nisha bawani cin abu tayi sosaeba, itama ba yunwar atareda ita, nan suka sanar mata ba maijin yunwa acikinsu ma'ana yau baza sufito cin abinci ba, bata tambayi daliliba tajuya tafita daga dakin, itama Hajj mama cewa tayi takai takai mata nata bangaran ta, sunayi Isha kowa tanemigu ta kwanta yau bawani Hira, juyi suka dingayi dake suka samu bacci ya daukesu, da suba Nisha ne ta tashesu sukayi sallah daganan suka nemi guri suka kwanta, Nisha kuwa seda ta dan taba karatun Qur'an data saba, sannan ta kuma ta kwanta itama,
se wajan karfe 10:30 , Barka tazu ta tashesu tasanar dasu ana jiransu a parlour, wanke bakinsu sukayi sannan suka fito, angama shirya komai kan table Hajj mama zaune harta fara cin abincin ta, karisowa dining din sukayi suka shiga daga mata gaisuwa bata kallesuba tamaida kallonta ga nisha tareda amsa nata gaisuwan, ganin haka yasa suka sake gaisheta karo nabiyu , murya can ciki ta amsa musu, sannan suka nemigu suka zauna tareda diban abinci suka suma ci, suna tsaka daci, AJEEMAL ya kunno parlourn hade da sallama jikinsa sanye da kana nan kaya wayanda suka amshi jikinsa , abunka da kyakykyawar namiji sede ace shiyayiwa kayan kyau, hand dinsa daukeda na aheel, fiska ba yabo ba fallasa, ya nemigu daga parlourn yazauna remote ya dauka ya kunawa aheel cartoon amma sam aheel hankalisa baya gun, yana kan Auntyn sa se washe mata baki yake yana kokarin tashi yaje gunta ganin yanda papansa yarike hand dinsa gam yasa yakalli papan nashi , koda yaga hankalisa nakan wayarshi yasa shi dole yakura yakoma ya zauna,
Nisha duk tana ganin abunda AJEEMAL keyi wato bayason aheel yazu gunta shiyasa ya hanashi tashi, su reeda kam tunda yayansu yashigo suka dakata da cin abincin kirjinsu se dukan uku uku yake, Hajj mama mikewa tayi tareda riko hand din nisha suka nufo parlour, ganin Hajiya ta tasu yasashi zamewa daga zamar da yake still yana rikeda hanun aheel, gaisheta yayi ta amsa da fara'a tareda neman guri tazauna, shima kujeran ya koma tazauna yashiga latsa wayarsa , Nisha kamar bazata gaishe shiba, sekuma tace,
" ina kwana, shima shiri yayi kamar baijiba, sekuma yace lapia, tareda maida kansa ga wayarsa, jin muryan aheel yakira sunan Auntyn sa yasashi AJEEMAL saurin kallonsa sekuma yamaida kallonsa ga Nisha da tamikowa aheel ahannu alamar yazu, ganin Hajiya na kallonsu yasa AJEEMAL yasaki hand din aheel fiska murtuke yakebin aheel da kallo ganin irin tacinsa dashi da Auntyn tasa dayake Fadi, ahankali aheel ya dingisa yakarisa gun Nisha tareda fadawa cinyarta yana dari itama Nisha dariyar take tana fadin,
" my baby yakake, I'm fine aheel yafada yana washe baki, duk akunne AJEEMAL surutun dasuke, aunty shine bakizo kika karamu wasanba koh baruwana dake aheel yafada yana shagwabe fiska, daram taji kirjinta yabuga ba ita kadaiba hattasu reeda dake zaune haryanzu sun kasa tashi daga wajan dasuke,kaikace ba kowa awajan, ko mutsi basayi, se yanzu AJEEMAL ya dago yamaida kallonsa ga su fadeela daga inda suke zaune yana fadin," yau kunfi karfin zuwa kugaishenine toni bari nazo nagaisheku yafa yana kokarin mikewa, cin hanzari harsuna gwaral , cikin rawan jiki suka karisu tareda zubewa saman capet suna gaishe shi, cin sake fiska ya amsa musu yana murmushi, nan hajja mma da AJEEMAL suka buge da fira wanda yasa su fareeda tunanin komai yawuce, fadeela "
go and call me Barka AJEEMAL yafadi, okay kawai tace tanufi gun baba Barka dan kiranta, ba adadeba suka taho tare, seda suka gaisa da barka daga bisani yasheda mata cewa yau yana bukatar tahuta kartayi aikin komai gdn nan, girki ko shara kowani wanke wanke tabarwasu reeda ,zasuyi komai in akwa wajen datake da bukatan tafiya zata iya zuwa, tansan halin AJEEMAL niya fadi magana baya canzawa kuma ba atamka masa , dan haka batayi musuba tajuya tatafi, amma gsky ba karamin mugunta yashirya musuba, suma kansu da jikinsu yasaba da wahala ya suke karewa da aikin gdn, balle su yaran gdn da basusan komaiba se hutawa da kwanciyar gado,
gaba daya parlourn yadau shiru hajja mma da Nisha kallon su fareeda suke da tausayawa, sukuwa ido raurau kamar masu shirin yin kuka, wannan wani rin punishment yayansu kesunyi musu, am sekutashi kuje tabaku wani aikin kufara kafun naje nadawo,
"I think yau su Daddy zasu dawo yafada yana kallon Hajiya, eh yau sukace suna hanya, alright bunda yace kenan yamaida kallonsa gasu reeda yana fadin," so kunga yau seku farantawa ammi rai da special cook nasan zatayi happy sosai, zanfita naje nasiyo wadansu kayan abincin seku hada akai, yafada tareda mikewa yana murmushi, kallo sukabi bayansa dashi, tareda mikewa suka nufi hanyar kitchen kamar yanda ya umarcesu, Hajiya ce tabisu da kallo tana fadin,
" lallai kam za aci girki mai dadi agdn nan yo inbanda abun AJEEMAL mesu fareeda suka sani agirki banda indomie wayan nan kam se Barka tasa musu hanu dole, inba hakaba shirmensu kawai zasuyi zanga ya zakuyi inkunje gdn maza jenku ae bakowane yakecin abinci yar aikiba irin yayanku, bakaramin mamaki nisha tayiba jin basu iya girkiba, muryan Hajiya taji tana fadin," nikam bari naje bedroom nadan mike zuwa anjima tafada tareda mikewa, tafiya zakiyi aheel yafada yana kallon Hajj mama, eh zanje nadan kwanta kadan ga Auntynka katayata Hira, kozamuje can din Hajiya tafada tana kallon Nisha, aa zamu zauna anan karmuje mudameki da yawa, dariya Hajiya tayi tana fadin,
" to shikenan bari naje tana fadin haka tajuya tafita, ganin haka yasa Nisha takalli aheel tace
," jirani bari nazo tafada tareda gyara masa zama akujeran, kitchen tabisu fadeela, tundaga shigowar ta , tasan lallai kitchen yayi baki, Barka tsaye akansu tana dariya tana kallonsu, kaida kaga yanda suke aikin kasan babu alamar sabo a taredasu, daga bakin door din kitchen Nisha tatsaya tana kallon su gaba daya yanda suke wanke wanke ba tsari, gaba daya guri ya hargitse, ga fiska babu annuri, ko wacce baki kamar zai taba bango, kai yayan nan, kukawo nan natayaku gaba daya kun bata jikinku kubarshi kawai zanyi cewar Barka, amma sam basu kalataba balle sumatsa yanda ta bukata, juyawa nisha tayi takoma parlourn gaba daya sun bata dariya da tausayi, nan ta zauna kusa da aheel suka cigaba da tadibsu, yana bata labarin school dinsu papa yace ranar Monday zai cigaba da zuwa school tunda yaji sauki, se wajan azahar suka fito daga kitchen din sukayi iya abunda zasu iya suka barwa Barka sauran, suna fitowa suka nufi dakinsu gaba daya sunyi laushi,
seda suka gyara dakin nasu suka share tas mai yayi need sannan suka fi suka haura sama dakin ammi dana, ganin aheel yayi bacci yasa Nisha tazameshi daga cinyarta ta gyara masa kwanciyar, daga bisani tanufi inda taga su fareeda sukayi, nan ta tayasu suka share suka goge ko ina duk dacewa dakin bawani faci yayiba, suka kuna turaren wuta mai bala'in kamshi da kama daki, nada nan gd yadau kamshi, haka suka shiga bangaran Daddy shima suka gyara shi need suna kammala wa suka nufi dakinsu sukayi wanka tareda alwala sukayi sallah, gada nan suka nemi gu suka kwanta dansu sake gajiya, Nisha kuwa tana gama shiryawa tanufi parlour ganin tabar aheel shikade yana bacci, zama tayi tasake masa matashi da cinyarta tana kallon kyakykyawar fiskar shi yayinda yake bacci, lumshe ido tayi tana sakawa da kuncewa cikin zuciyar ta, nan kuma tabude idon ta saukeshi an aheel dake kwance cinyarta, hawaye ne , yashiga wanke fiskarta, ta tuna lokacinda take kwance cinyar umman ta, itama lokacin da suke tareda umma bata rabuwa da cinyarta, kullum insuna zaune se yakasance kan Nisha a cinyar umma,
" oo rayuwa kenan allah kajikan ummana, allah ka kai haske kabarinki, yaushe zansake samun farinciki irin wanda nake acikin mahaifana, ya Allah na rokeka ka baiyanamin ma haifina, iduk inda yake kasa yana cikin koshin lapia, ubangiji ka karkatu hankalisa gareni, ahankali tasa hanu tashare hawayenta, hadeda maida kanta jikin kujera,gd yayi tsit kamar ba kowa su reeda sun dade da bacci banda Nisha datakasa rintsawa ta zauna ta tsunduma kogin tunani,
Motar AJEEMAL ne yakunno kai cikin gdn, mai gadi yabude masa geat, yashigo yayi parking, yafito tareda kiran mai gadin cikin rawar jiki maigadi yakariso yana fadin
," ah yallabo sannu da zuwa, yauwa sannu AJEEMAL yafada tareda mika masa ledojin hanusa yana fadin yakai ciki, yana fadin haka yajuya yanufi part dinsa, nan mai gadi yanufi parlourn da aikenda aka bashi, nisha yatar a parlourn yamika mata yace inji yallaboi AJEEMAL, nan ta amshi sakon tai kitchen dashi ta direwa Barka, tanufi bedroom ta tasu su fareeda daga bacci ta fada musu sakon yayansu ya ISO, seda sukayi sallahn la'asar daga bisani suka nufi kitchen suka suma aiki ba kama kafar yaro, duk abunda suka san da Daddy da ammi naso shi suka daura, Barka basa musu hanu tana nuna musu yanda zasuyi, karsu tafka shirme, duk da nisha itakam ba bayaba, wajan girki, dan lokacinda suke gda da umma ita take komai bata barin umma tayi ko hanyar kitchen sede tazama yar kallo kawai, dan haka ta zage sosai wajan nuna musu nata bajintar,
aheel ne yatashi daga bacci ya dingisu kitchen inda yake jin muryan su , Nisha naganin shi tazame hanunta daga abunda take tanufi gurinsa tana fadin,
" baby katashine, gyada masa kai yayi yana tambayar papansa bai dawoba, ya dawo muje nakaika tafada tareda jan hanunsa suka fito daga kitchen din, har part dinsu tarakashi tareda murda handle din kofar lokacin AJEEMAL yake kokarin fitowa shima cikin wani shirin mai kyau da alamar fita zai sakeyi, Nisha tsawa tayi tana kallon kyakykyawar fiskar hade da lumshi ido tana shakar daddan kamshin turarensa mai wayar mancewa dan ko zama yayi agu yatashi se ka kwana 2 kina jin kamshin wannan turaren, hankali take sakebin kamshin jikinsa tareda matsuwa ahankali, sake baki yayi yana kallonta ganin yanda ta lumshe ido tana matsushi, baya yayi da sauri yana fadin ,
" ke lapiyarki meye hakan yafada cikin da ga murya ya na mai hade gira yana kallonta arazane tabude ido se yanzu nutsuwarta ya dawo gaba daya ta rude jin tsawar da ya buga mata, shikansa aheel seda yatsorata yanda yaji papan shi, ya dagawa Auntyn sa murya, bin mahaifin nashi yayi da kallo tareda matsawa kusa shi yana fadin," papa ina zakaje nima zan bika yafada yana jan hand dinsa, ✍️ .
Page 11, cikin bacin rai ya kalli nisha sekuma yamaida kallonsa ga aheel yace,
" zanje nadauko su Daddy daga airport ne yanzu zanje nadawo, sekuma ya daga kai tareda hararota Nisha da ke kokarin fita daga parlourn wanda kanshin turaransa yajawota ciki, cikin kaushin murya yace
," ke tsaya, cak tsaya tana kallonshi jin mai zaifada seta ga yamaida idonsa ga aheel yana fadin,
" kabita kukoma inda kukafito sena dawo, abunda yace kenan yasa kai yafice tareda shigewa mota yafita, cikin sanyin jiki Nisha tariko hanun aheel nanfa yaro yanuke tareda yin rau rau da ido yana shirin kuka,
" ni yaunwa nakeji nan taga ya zame hanusa daga nata ya dingisa cikin daki, bai dadeba yafito hanunsa daukeda cheeseburger yana ci nan ya mika mata haunu tajashi suka fita, zuwa yanzu gd ya dumame da kamshin abinci kota ina, nanda nan suka kammala komai suka jereshi a dining table , daga bisani suka tattara izuwa part din Hajiya nan suka baje kolinsu na hira, nan sukaita hiransu har gorin goshin magarib, motar AJEEMAL ne yakunno kai mai gadi yabude masa geat, jin ana kokarin bude geat ne ya tabbatar musu dacewa su ammi sun isu, nan suka fito tareda watsawa aguje kamar wasu babies suka nufi motar,
AJEEMAL nayin parking suka karisu suna washe baki, reeda ne tabude kofar baya ammi ta fito fiskarta daukeda murmushi, nan sukayi kanta tareda rungume cikin kewa da murna, Daddy ne yafito daga gdn gaba shima suka shiga rungumarsa suna fadin sunyi kewarsa tareda karban karamin jakar hanunsa, okay nikam ba wanda yayi Miss dinako shiyasa ba akalli inda nakebama, juyowa sukayi cikin hanzari suna fadin,
" lah ya kamal ashe kaima kadawo, aa mantani akayi acan yafada yana tura musu baki, nan suka nufushi suna dariya tareda rungumarsa, suna jan hanunsa, to nikam kukyaleni karku yadani, sewani jana kukeyi, dariya sukayi gaba dayansu tareda karisawa parlourn mai gadi na biye dasu da suran ma aikatan gdn dauke da sauran kayansu, suna zuwa parlourn suka dire kayan tareda karamusu bangaji sukafi, su reeda suka dauki jakan kayan suka karisa musu dashi bedroom dinsu, farin ciki fal zuciyoyinsu, AJEEMAL kama tunda yadiresu yanufi part dinsa yayi alwala yanufi masallaci,
haka kamal ko wanka bai tsaya yiba shima alwalan yayi yafito, yana fitowa yayi karo Daddy shima zaitafi, nan yanufa masa baya suka wuce, aban garan ammi kuwa wanka tashiga yi sosae daga bisani tayi alwala tafito, kaya mara nauyi tanema tasa tadauki hijabi ta tada sallah, bayan ta idar tayi kasa parlourn shiru bakowa nan tafito tanufi parlourn hajja mma tasan baza arasasu canba, tunkafin ta katisa shiga takejin sautin muryoyinsu, dan haka takarisa tareda tura door din tashi dauke da sallama abakinta, kallo tabisu dashi yayinda suketa hiransu, suna ganin shigowar ta su fadeela sukatashi tareda nufuta suna fadin," ammi Miss u so much wlh, da bakwa nan gd ba Dadi, gd yakoma shiru, oh dama da muke nan mukesa gd yayi hayaniya koh ,? Ammi tafadi, dariya sukayi reeda tace," ammi bafa haka muke nufiba, hakane mn, tukunna ma kunyi sallahne da kuka zauna kuna hiranan, eh munyi dazunan muka idar , okay ammi tace yayinda yamaida kallonta ga nisha da aheel yayi matashi da cinyarta yana bacci, mazawa tayi kusa da ita tayi tazauna,
cikin hanzari Nisha sannu da Hajiya tafada tareda kokarin tazame aheel daga cinyarta, ganin haka yasa ammi tayi saurin cewa," zauna abinki, tafada yayinda take kallon Nisha, sunkuyar da kai nisha tayi tana fadin," ya hanya andawo lapia, lapia kalau alhmdllh, ya gdn I hope yana mike dadi, kuma ba matsalan komai , eh Hajiya , karna sake jin Hajiya nan call me ammi kamar yanda kikaji su fadeela suna kirana, kema yatace yar ta gaban goshima tabada tana dafa shoulder dinta, dariya su reeda suka shigayi jin abinda amminsu tafada nisha ta gaban goshine, cikin wasa ammi ta hararo su reeda dake dariya tacigaba da hira da Nisha tana fadin," kisake jikinki damu nan gdnkune, to Nisha tace tana sunkuyar dakai tana murmushi, yadae ina Hajj mama ne banji mutsintaba, ammi ta fada tana kallon reeda, dazunan tashiga bedroom sallah tode haryanzu bata fito. .,
batakaiga karisa maganar ba, Hajj mama tafito fiska dauke da fara'a tana fadin," ah mutanan US har hutun yakare , tafada yayinda take kokarin samun waje tazauna" wlh fa hutu yakare ni harna gaji da kasarma ammi tafadi, yo ae dama duk wanda yabar gd tofa gd yabarshi Hajiya tafada gami da dariya, gsky kam nan ammi tashiga gaida Hajiya, seda suka gama gaisuwan, Hajj mama tace," to kingafa new babynki, tafada tana nuna Nisha, eh naganta har mun gaisa ae, ," ayya ina mai gidana koshi bai shirya dawowa kun barshi acan dan naga yafi kaunar can abunsa, aa tare mukazu inaga yana masallaci da daddynsa , nasan yana dawowa ke zai fara nema kinsan mutumin naki ae, dariya Hajiya tayi tana fadin," eh wannan haka yake nafi kowa sanin kayana, dariya sukayi duka tareda cigaba da hirarsu, nan ammi take basu labarin irin kayanda sukayi order na bikin kamal da nabeela, su fadeela murna biki zai tashi agdnsu za ayi bikinda ba ayiba baya, dan ko bikin AJEEMAL baiyi wani gagaramin bikiba, dan haka zasu rama abunda basuyi abayaba suyishi yanzu, ana kiran isha kowa yawatse yanufi yin sallah, Hajj mama takuma bedroom sallah, haka ammi ma tanufi bangaran ta dan yin nata ibadar,
su fadeela da Nisha suka rufa mata baya hanunta dauke da aheel gudun kar abarshi shikadai suka nufi nasu dakin, kwantar dashi tayi saman bed tanufiyin alwala tayi sallah, su fareeda suna idarwa suka nufi parlour yau rawar kai se abunda yakaro ammi tadawo, zama sukayi a parlourn suna jiran sakko won ammin, Daddy ne yashigo bayansa dauke da AJEEMAL tareda kamal, shigowar su gwanin shaawa, cikin happy suka isa gareshe suna masa welcome, yayi daidai da sakkowan ammi fiskarta daukeda murmushi, tana bin yayanta damijinta da kallo gwanin burgewa tana mutukar alfahari da wannan family nata gaku wani garin da allah yabasu Nisha, karisowa tayi gunsu ahankali dauke da murmushi nan nata, tana fadin,
" gwara da kuka shigo yanzu dan yunwa nakeji gaba daya bana gane kaina, dama kekam gwanar jin yunwace Daddy yafada cike da tsokana tareda karisawa dining suma suka rufa masa baya suna dariya, waje suka samu suka zauna banda AJEEMAL da kamal dasuke tsaye ammi ne ta kallesu tana fadin,
" kufa dakuke tsaye kuzauna muci abincin mana, kamal ne yafara magana yanacewa, ni banjin cin abinci for now because ni wankama nakeson nayi, gaba daya agajiye nake, kallon reeda yayi yana fadin,
" please in kin kammala ki kawomin nawa bedroom dina, to tace masa daga bisani yajuya yafita, kaikumafa Daddy yafada yana kallon AJEEMAL dake tsaye yakama kugu kazu muci abincin mana, a no akoshe nake, yafada can kasa, wul wul ga ido yayi yana su yatambayi aheel amma yasan bazai wuce suna tareda waccan yarinyar ba tunda bai ganshi a parlourn ba , guntun tsaki yaja ahankali tareda sakai yafice daga parlourn, bayanshi sukabi dakallo kawa tareda cigaba da cin abincin su, ammine tadan bugi reeda abayanta,ashhh ammi meyafaru mekuma nayi, saboda mun dawo har kun mata da kanwar taku koh,? to maza kutsaida cin abincin nan kuje kukirata tazo taci abinci, cikin hanzari fadeela ta tashi reeda tabi bayanta,
zaune suka sameta cinyarta dauke da kan aheel tana shafa kansa, reedane ta karisu tareda dauke kan aheel daga cinyarta takwantar dashi gefe tareda jan hanunta Nisha batareda tace mata komaiba suka fito parlour, seda takaita har dining ta zaunar da ita tana fadin," to ammi ga shalelen babyn taki, ganin Daddy da Nisha tayine yasa tazame wa ta gaisheshi, cikin fara'a ya amsawar tata , yana fadin," ina kika shiga kowa ya halarci wajan cin abinci amma banda ke, kefa ba bakowa bace, as from now dazaran time din cin abincin yayi to naganki awajan, kuma duk abunda kikaga wani yayi agdn matukar mai kyaune kema kiyishi, duk abunda kikeso ko kike bukata gani ga madam kitambaya batareda shakka ko tsoroba, muma iyayenkine kinjiko, cikin sanyi murya nisha tace,"to inshallah, to baza kici abincin fadin ammi yayinda ta dire mata plate din abinci gabanta, nan sukaci gaba da cin abinci suna hira cikin raha da nishadi, Nisha taci abinci sosae kuma ta sake dasu sosae ,
seda suka kammala suka dawo parlourn suka cigaba da hirarsu, yayinda Barka tazu ta kwashe abubuwan da akayi amfani dasu tayi kitchen, nikam kaje gurin Hajiya kuwa,? Ammi ke tambayan Daddy," eh na leka mun gaisa dawowana daga masallaci muka biya, okay to ae shikenan, wayan fadeela ne yayi kara taduba screen din wayan taga kamal ne ke Kira, cikin sauri tamike tana fadin," oh my God, na manta daya kammala yace nakawo mishi abinci, cikin hanzari ta tashi tanufi kitchen domin hada masa abinci," hira yayi dadi kin manta da batunsa zaku hadu ae ammi tafadi tana dariya , Nisha kam tunda fadeela ta furta sunan kamal gabanta yafadi, kwata kwata tamanta dame irin sunansama, ya ilahi wannan wani irin rayuwace, mutumin da yabata makudan kudi dan ta cece rayuwar mahaifiyar ta, shine tayi saurin matawa dashi haka, se yanzu yafado mata ko daran da umma zata rasu taga miss call dinsa, still tasake ganin kiransa bayan zuwanta gdn nan , kin karbi kudinsa kin kuma manta dashi balle kisan duniyar dayake, nashiga uku tafadi afili wanda ita kanta batasan maganar yafitoba,
cikin hanzari tasa hanu tarufe bakinta tanabin yan parlourn da kallo, jin yarda ta tashi azaburene yasa duk suka nufota suna tambayar lapiya, yanda taga sundamu suna tambayar ta yasa tace," bakomai jinayi gabana yafadi, ammine tajawota jikinta tana fadin," ba nashiga uku zakiceba, idan kinji irin haka nan gaba cewa zakiyi ina'lilla hi wa inna ilahi raju'un, bana shiga ukuna kinjiko, gyada mata kai tayi, to maza kije ki kwanta kuma kiyi addu'a kafin kwantan kinjiko, cikin sanyin jiki Nisha tace,"to, tareda juyawa tayi daki , gaba daya suka bita da kallon tausayawa, daga ammi har Daddy ba wanda Nisha bata kwanta masa araiba, duk da dama Nisha yarinyace mai shiga zuci, ga hankali da nitsuwa, tana shiga daki tafada saman bed kusa da aheel, hanu tasa ta lalubo yar karamar phone dinta, tabinciko numbern kamal tayi dealing koda takira tajita switch off takira yakai sau uku but abu daya ake mai maita mata, ritsa ido tayi cikin zuciyarta tana fadin,
" please kamal ka gafarceni kai ba irin mutumin da za ayi saurin mancewa dashi bane kayi hakuri da wauta irintawa, hawaye tashigayi shar shar gashi bata san yaushe zata sake sashi a ido ba, dama yata fada mata shi bai cika zama kasanar ba, because shi foodbollas ne, gsky baki kyauta wa kankiba, hakade tacigaba da tunane har bacci barawo yasaceta, su ammi sunyi hira sosae, daddy kam tuni yayi gaba yaje yayi kwanciyar shi dan bazai iya dugun hiraba, sukuwa sundau time suna hiran daga bisani wajan karfe 10 itama taimusu seda safe tabi bayan mijinta, suma kuma taimusu umarni dasuje sukwanta, dan haka suka nufi bedroom dinsu, shiguwan sune yatada nisha daga baccinda take, dasuri Nisha tamike tana kallon aheel da yafarka shima yana dan wul wul ga ido, katashine Nisha tafadi, gyada mata kai yayi yana fadin,
" kikaini gun pahpahna, please kikaishi wajan babanshi Nisha tafa tana kallon fadeela, what tab kikaishi de kokuma kisashi ahanya ko kibarshi anan papanshi zaizo ya daukeshi tafada tareda neman guri takwanta, mai yasa baza kikaishiba to Nisha tafada tana bin fadeela da kallo , bama zuwa part dinsa abunda tace kawai taja blanket yarufu, reeda kam tuni tayi kwanciyar ta, tanajin maganar dasuke amma bata kulaba tayi mukus kamar mai bacci, sake baki Nisha tayi tana kallon fadeela, wani irin magana ne wannan mutum da dan uwansa but ace baya zuwa inda yake Nisha tahau maganar zuci, muryan aheel taji yana fadin,
" akaishi papanshi yana shirin kuka, ahankali ta zamu daga bed din tareda jan hanunsa suka fito, har part dinsu ta rakashi ta tura masa kofar tana fadin,"to kashiga seda safe tafada tareda juyawa, gd yayi shiru, se hasken wuta gaba daya Nisha atsorace take, kamar ace mata shiiii tagudu, jiyuwar da zatayi taji aheel nafadin," Aunty tsoro nakeji dakin da duhu bazan iya shigaba, cikin hanzari tamatso tana fadin," duhu kuma, tabbas dakin da duhu da alamar ankashe light din parlourn, gashi bantahu da phone balle na haska maka, ko mukoma can mukwana da safe sena dawo dakai tafada cikin lallashisa, kuka yafara kokarin mata yana fadin," shigurin papansa zeje, jan hanunsa tayi suka kutsa cikin parlourn, cikin sanda, bata san inda makun nan sukeba balle takuna,
jin muryan aheel dake kwadawa papansa kira ciki muryan kuka, bcuz matso rajin duhune bawaso duhu kwata kwata, sede wajan bacci nanma dan yanajiki papansa, AJEEMAL na kwance saman bed yarufu duk da ba bacci yakeba, jin sautin muryan aheel yasashi mikewa tareda lalubar wayansa, sakko wa yayi daga bed jikinsa dagashi se best da dan gajeren wando fari mai laushi, kunna light phone din wayarsa yanufo parlour, yana isa parlourn direct yanufi kuna wutar, nan da nan haske mai kyau da inganci yabai yana, yayinda idon Nisha dana aheel suka sauka kasansa, idon Nisha ne suka fito waje ganin yanayida AJEEMAL yafito, duk ilahirin jikinta yadau bari, amma ta gagara dauke ido akansa, tana karewa kyakykyawan surorinsa kallo, aheel ne yaje da gudu yafada jikinsa, jin aheel yazame hand dinsa daga nata yasa tayi saurin watsawa dagu tabar dakin cikin yanayi natsoro da kidima, daga aheel har babansa binta sukayi da kallo, shi kansa AJEEMAL yaji kunyar ganinsa datayi ahaka but baiyi tsammanin ganinsu a wannan time dinba, muryan aheel yaji yana fadin,
" papa I'm feeling hungry, okay zauna anan kajira AJEEMAL yafada tareda tufan kitchen yadauko cup tareda hada masa tea tareda sandwich and fried chicken a plate yamika masa, nanko aheel yakarba yasuma ci yana shan tea din, seda ya kammala AJEEMAL ya dauki plate da cup din ya daura table daga bisani ya daukesa suka nufi dakinsu, ba ajimaba bacci ya daukesu dagashi har dan nasan, itama Nisha tana isa bedroom dinsu tasamu kowa yayi bacci hakan yasa itama ta kwanta kirjinta se wani bugu yake, da zaran tarufe ido AJEEMAL take tunawa cikin yanayinda taganshi, ahaka tadinga juyi har bacci ya dauke ta, washe gari, washe gari da asuba ammi da kanta tazo ta tashesu dukda bawani sabon abu bane kafin tafiyarsu ita take zuwa ta tashesu, idan itama ta makara Daddy ke tashinta, nan suka tashi sukayi alwala sukayi sallah, suka koma suka kwanta, tun tashin ammi daga tayi sallah bata komaba tashiga kitchen ta kamawa Barka wasu aikin sukayi tare ,
kasan cewan Daddy nada fita office nanda nan suka kammala komai, a takaice de seda ammi ta sallami Daddy itama tayi nata breakfast din takoma takwanta dan tahuta gajiya sosae, 10am, sannan suka nisha suka tashi sukayi wanka tareda wanke bakinsu daga bisani sukashirya suka fito, a dining suka tarar da nasu breakfast din, fareeda ta kwalawa baba Barka Kira, nan da nan ta isu tana tambayar ba asin kiran, ammi bata fito break bane, sunyi nakaiwa Hajiya nata, ammi kuma tare sukayi da mai gdn har tashiga bacci, okay ya kamal reeda tasake tmby, shima nakai masa har yafita gun aiki, alright you can go, fareeda tafada tareda zama bisa kujeran, suma suka zauna suka shiga yin break, seda suka kammala suka tashi gani cewa ammi na bacci yasa suka nufi inda sukafi kauri majalisarsu ban garan Hajiya,,,
Dawowan su ammi yakarawa gdn armashi sosai dan ba karamin sakewa nisha tayiba, ganin yanda ammi takara janta ajiki, duk wani tunanin ko rashin sakewa ya kaurawa Nisha, tasake da gdn sosae hakan ba karamin dadi yayiwa su ammiba, dan haka suka zage dantse wajan kulawa da ita yanda yakamata, duk wani abunda suka san zai kawar mata da damuwa ko tunani shisukeyi, ba abunda Nisha zata nema agdn tarasa, damuwarta daya shine yanda gidan keda tsauri wajan fita, ba ma'abota son fita bane, koda yaushe zaman gd se mkrnt, atuna ninta taya zatasan halinda mahifinta yakeciki, bugu da kari idonta naso tayi tuzali dana kamal, shiyasa take allah allah time din zana jam yayi itama tayi kamar yanda ammi ta sheda mata tasamu allah yabata sa'a taci tafara zuwa makaranta nan kota samu wata dama, ,yau weekend kowa na gd,
tunda sukayi break suka dawo parlour suka yada zango, hira suka shigayi suna kyakyatawa, cikin raha da kwanciyar hankali, suna tsaka da hiran AJEEMAL yashigo bakinsa dauke da sallama, hanusa dauke da na aheel, bayansu kuwa rahilace ketafe cikin isa ita kadanta se yamutsa fiska take, AJEEMAL samun guri yayi kusa da Hajj mama kasan carpet yazauna tareda daura aheel acinyarsa, ita kuwa rahilace waje tasamu daga nesa tazauna tana karewa yan parlourn kallo, AJEEMAL ne yafar isar da gaisuwanshi gasu ammi suka amsa cikin fara'a, su fareeda ma suka gaishe da yayan nasu, batareda sun kalli inda Aunty heelan tasu takeba, bacce ko sun gaisheta tama ba lalle ta amsasuba, murya can kasa ya amsa gaisuwan kannen nasa tareda maida kallonsa ga heela tareda sakar mata wani harara, tsuke baki tayi tareda dan zamewa tana gaishesu, fiska ba yabo ba fallasa suka amsa mata gaisuwar, ammi ne takalli AJEEMAL MUDIBBO kaikam kayi wuyar gani daga kai har matar taka, allah yagani ammice ke kiransa da wannan sunan amma bayaso bade yanda ya iyane itadinma tana kirane dan tsokana dan tasan baya son sunan, Daddy ne yakarbi maganar dacewa,
" banda abunki kinsa hukuma se ahankali basuga ta zamaba, to itama matar tasa jami' ar lapiya ce, bata dawani time yau night gobe morning, se ana musu uzuri, gsky kam se ahankali Hajj mama tafa tana kallon Daddy, itadae ammi batace komaiba, tasan wannan ba hujja bace yade fadane kawai, nan taja bakinta tayi shiru, shima AJEEMAL kansa sunkuye yana wasa da yan yatsun aheel, itama heela hankali ta nakan wayarta, dakinne yadau shiru nawani lokaci, fareeda da fadeela se hararo Auntyn nasu suke, wacce batama san sunayiba, gaba daya tagama fita musu arai, basuki yayansu yasaketaba ko yakaru aure dan kwata kwata batada hali mai kyau, ga isa da gadara shi kuma batada kunya kokadan✍️
Ina Auntyna take bangantana,? Aheel yafada tareda zamewa daga cinyar papansa yanufi su fadeela yana tambayar su,
daga AJEEMAL har rahila su ammi bin aheel sukayi da kallo
Daddyne yakamo hanunsa yana fadin,"bagasu nan kana kallonsuba yafa yana murmushi yana nuna masa su farida , cin hanzari reeda tace,"
Daddy bafa mu yake nufiba, mutumiyar sa, nisha yake tambaya, Daddy ai inkaga aheel yashigo parlourn nan bai tambayi Nisha ba to ae ba lapia,
Gskykam Nisha mutumiyar sace, inbai gantaba ba zaman lapia kaje dazunan tashiga daki , sedefa kar ka dameta da surutu dayawa inkashiga kajiko, Hajj mama tafada tana dariya.
gaba daya dariyan sukayi banda rahila data sake baki tana bin aheel da kallo,"
yau kajimin shermen banza wai Aunty, yanada wani Auntyne bayan wayanda yagani zaune agabansa yana kallonsu,
azahiri kuwa wani guntun tsaki taja wanda yafito fili wanda yasa yan parlourn suka karkatu hankalisu gareta, ganin yanda suka tsura mata ido suna kallonta yasa tamike tana yamutsa fiska tafita,
AJEEMAL naganin fitan ta yatashi shima yabita, ikon Allah ammi tafada tareda bin dan nata da kallo, murmushi Daddy kawai yayi tareda tashi yamu sallama ya haura sama abunsa,
Mtsw dama na fada miki ammi rahila bata da kunya da kike ganinta, fareeda tafada tana tabe baki, sekuma tasake cewa kinma san meyafaru bayan tafiyar ki,..,fuf taji ammi ta buge mata baki,
banason maganar banza da kananun magana, dib reeda tarufe bakinta tana kallon ammin nasu, tana kokarin sake cewa wani abu, ganin ammi ta tashi tahaura sama tabi bayan daddy yasa tayin shiru, zuciyar ta namata wani irin suya,
Kema da kinyi shiru yanzu gashi kinja ta buge miki baki fadeela tafada tana kallon reeda,
To shiru yana da amfanine ae seta dauka ko tsoronta akeji reeda tafada tana tura baki, bawani tsoro inkikaga haka mutum yana abu ana masa shiru to akwai darajan da yakeci ne bawai tsoro ba, Hajj mama tafadi yayinda idonta ke kan reeda da fadeela,
To ae naga daga zuwanta tanaso tashiga tsakanin mu da yayanmu kuma mu bashiga harkanta mukeyiba ita kuma tanaso tashiga namu, reeda tafadi,
to seku kauda kai kuyi kamar baku san tanayiba, kuma ina baku shawara kudinga kauda ido akan duk wani abunda kuka gani kudena yawan magana akwai shine mafi alkhari,
Bakowa yakeso adinga kawo masa kana nun magan ganuba, kekam kinga zahiri ae Hajj mama tafada tana kallo reeda da ta tura baki kamar zai taba bango,
gimtse fiska fareeda tayi tana kallon kakar tasu , jin dariya kasa kasa yasa taimada kallonta ga fadeela dake dariya kasa kasa cikin hanzari reeda takalli Hajj mama tana fadin,"
wlh Hajiya kiyiwa fadeela magana dariya fa takemin, ato gulmarki taja miki Hajiya tafadi,
nan fadeela tasake bushewa da dariya , pillow reeda ta dauka tabugawa fadeela, itama fadeela tadauka tajefa mata, Hajiya kam kallon su take tana dariya,
Aban garan Nisha kuwa tunda tayi breakfast bata zauna adakinba takoma tayi kwanciyar ta
Daga daki takejin hayaniyarsu amma takasa fitowa, saboda kanta dake dan sara mata,
Shigowar aheel ne yasata dole ta tashi tazauna ta saurari shirmensu da yasaba, Aunty gobe Monday zan koma school zakirakani koh Muje kiga school dinmu, school dinmu yanada kyau sosai, Ai nataba baki labarin koh ,
Eh kataba bani lbr yana da kyau nisha tafadi, yau zamuje tare koh , eh tace masa dan yau kwata kwata batajin yanayin surutu,
muryan aheel taji yana sake fadin," yau mummyna tana gd bata fitaba, baki taba ganin mummyna ba koh, nataba mana , cikin zaro ido yana fadin," a ina to, ? murmushi tasakar masa tace," lokacin da kake kwance asibiti,
lah ashe kintaba ganinta yafada yana washe baki, murmushi tamasa batareda tace komaiba, su fareeda dane suka shigo yayinda suka gama hiransu kowa yakama nashi guri, yauwa aku sarkin surutu yana nan yana miki surutun nasa da yasaba koh, fadeela tafa yayinda suke karisuwa ,
kallonsu nisha tayi tana fadin,"har kungama firan , eh mungama anyi bake, cikin sauke numfashi Nisha tace,"to yazanyi naso fitowa ayi hiran dani amma ciyo kan nan ya matsamin , oh sorry kinsha magani kuwa, fareeda ta tambaya," aa base nashaba nasuma jin sauki, aheel ne yazame daga bed din yana fadin," Aunty zanje gurin papana zan dawo anjima , to kawai tace tareda bin bayansa da kallo har yafita,
Wani dugun numfashi tasauke tareda maida kallonta gasu fadeela da suka kwanta suna danna phones dinsu, ahankali tazame daga gadon tanufi hanyar fita, domin kuwa ta gaji da kwanciyar, parlour tanufa tanemi kujera daga gefe ta zauna tvn parlourn akunne yake dan haka tashiga kurawa tv ido,amma hakalin ta kwata kwata baya wajan , da alamar ta lula wani dunyar tunani,
Kamal ne yashigo parlourn hand dinsa daukeda hairbrush yana taje kansa, idonsa ne yasauka kan Nisha dake zaune takurawa tv ido, da alama batama sanda shigowar sa ba,
ahankali yamatsa tsakiyar parlourn yana karewa Nisha kallo da mamaki, kallonta kawai yake bakinsa tagagara furta komai,
ita kuwa jin kamar ana tsaye kanta yasa ta daga idonta kadan, dantaga waye, daram gabanta yafadi kamal tagani tsaye kanta yana kallonta,
azabure tamike tayi baya tana kallon shi cikin zare ido, shima haryanzu kallonta yake," NEESHA kece,?:kml yafadi yana sake dubanta da kyau, ita kuwa baki se bari yake takasa cewa komai, hakan yasa tajuya tareda watsawa da gudu tayi daki,
shikuwa baki bude yake binta da kallo harta shige dakin, abun yayi matukar bashi mamaki meye Nisha taxoyi gdnsu, to kodae gizo tamasa,
kaiwan nan ba gizo bane tabbas nisha ce yabawa kansa amsa, yana cikin wannan tunanin ya tsinkayi muryan ammi dacewa,"
kai kumafa seyanzu, hanzarce ya kalli ammin tasu cikin sosa kai yana fadin," eh wlh , wani irin bacci kake haka, kayi break kuwa ammi ta tambaya, eh nayi Barka takaimin seda nayi ma nakoma baccin, okay to ae shikenan ammi tafada tareda take kokarin juyawa tayi kitchen, cikin hanzari kml yace,"
am bakowa mukayine, cikin tsareshi da ido tace," bakowa kuma aina ammi ta tambaya, eh yanzu naga tashiga bedroom dinsu fadeela, murmushi ammi tayi tana fadin," kodae Nisha kagani,?
Eh to ina ganin ita dince kamal yabata amsa,
baku taba haduba se yau kenan, eh kawai kml yace yayinda yake kallonta yanaso karin bayani, okay yanzu ina dan saurine in nasamu time zan maka explain daga baya kajiko, okay yace batareda yasake cewa komaiba, nan ammi tajuya tashiga kitchen abunta, ganin haka shima yajuya yafita daga parlourn,
Nisha kuwa tunda tashiga daki tanemigu ta kwanta, lokacin ta tarar su reeda duk sunyi bacci, nan ta nitsa kanta cikin pillow tana jin zuciyar ta yanda yake mata dukan uku uku, yanzu ta tabbatar da zarginta dama shine ya kml dinda su fadeela suke fadi, atunanin ta wani kamal dine da ban ashe kamal din da tasanine,
tundaga wannan lokaci Nisha tasumu sara daga sungama breakfast sun koma parlour Hira zata zame tayi daki tayi zamanta because kunyar hada ido da kamal takeji,
dukansu sun lura da hakan atunaninsu rashin sabu dasune wanda kuwa ba haka bane,
haduwa da kamal ne bata sonyi, wani lokaci ahar tunani take akan wace irin kaddarace ta kawota gdnsu kml
inama bata biyusu Hajiya ba tayi wani wajan daban, duniya da fadi ae bazata rasa wajan fakewa ba,
aban garan kml kuwa tunda idanunsa sukayi tuzali dana Nisha yakeson sake ganinta but hakan yakasa samuwa because duk wani hanyar dazaisa su hadu Nisha ta tusheshi ko haraba gdn ta daina fita, balle yazuba ido wajan shiga da fitar ta,
Abunda yasani shine zasu hadu komai daran dadewa tunda gd daya suke dole wani dalili zai hadasu,
yau hutun so fareeda na makaranta yakare komai ya dawo mata sabo kewa yasake dawo mata, domin kuwa su reeda sun koma makaranta,
dama hutu suke yanzu kuma hutu yakare,
shima kuma aheel mutumin ta yakuma school kuma wuni yake acan, gaba kidaya abokan surutun nata basa nan gd yakoma shiru, hatta itama ammin tana zuwa office, dan haka intaji kewan yamata yawa, seta tattara takoma sashin Hajiya tazauna suita hiransu, har yamma kafin su fadeela sudawo,
bikin kml da nabeela se karatuwa yake yau bai wace saura month ba, gd se shirye shiryen biki ake kaikace next week ne bikin, su fadeela har ankai dinki na event din bikin, duk da kamal yasheda musu shiba wani bidi'a zaiyi a bikinba,
atunanin shi wannan bawani bikin da za'ayi wani shagali bane because bikin bawani shiga heat dinsa yayi harcan ba,
nishane kwance bisa gado yayinda idonta ke kallon sama kamar mai nazarin wani abu, phone dinta ne yashiga ringing akwai kamar jira take akirata dama, salmace kan laye, hanunta har bari yake wajan dagawa,
Karawa tayi akunne ta tareda yin sallma, salma bata amsa sallamar taba tashiga watso mata tambaya, " wai nikam qlu kike kuwa, salma tafadi,cikin hanzari Nisha tace," mekika gani meyafaru,? tafada yayinda take kokarin gyara zama, ✍️
Bansan meyake damunkiba, tunda nabar gdnku baki sake daukar waya ki kiraniba, kuma kince zakizo gd shima kuma kin gagara, shine nace bari nakira naji har rayuwa tai miki dadinda zaki manta dani koh,
jikin Nisha ne yayi sanyi dan tasan bata kyauta ba , gaba daya tarasa meke damunta, cikin sanyin murya nisha tace,"
Nama rasa bakin magana amma kiyi hakuri nasan ban keutaba, ke kwata ce kuma aminiyata aduniyar nan banida kawar datakaiki, hasalima in inada wata damuwa nakanzo nasanar dake ko ummata wani damuta bata sani kamar da ke kika sani , salma yanxu haka ina cikin damuwa amma maganar bazaiyiyu awayaba, gashi gdn nan ba afita daga gd se mkrnt, kwata kwata ba afita salma,
naji ba afita amma yanzu dole kisamu hanyar fita domin kuwa ankawo kayan lefena, salma tafada tana tura baki duk da Nisha ba ganinta takeba,
cikin farin ciki nisha ta wantsalo daga gadon tahau rawar murna kaikace ita aka kawo kayan, daga bisani tadan dakata da rawan tana fadin," amma kuma shine baki sanar daniba kafin akawo kayan,
dama nazuba miki idone inga ko zaki kirani, amma baki kiraba kirkinki yayi kadan, gashi nina damu dake nakiraki, kuma na sanar dake, yanxu de sena jiki kuma ina zuba ido, to kawai Nisha tace daga bisani suka kayi sallama, salma takatse wayan, zama nisha tayi abakin gadon tareda zamewa ta kwanta farin ciki fal zuciyar ta, jitake kamar ta bace ta tafi gdnsu salma,
aheel ne yashigo dagudu dakin tareda hawa bed yafada jikin nisha Yana washe baki yana fadin," Aunty
ta tsorata sosae ganin bata san da shigowar shiba, cikin tsoro tana zaro ido ta dago aheel tana fadin," amma kai wannan yaro koh tafada tareda jan kumatun sa , gabani tsorofa,
washe mata baki yayi yana fadin, "Aunty wai tsorita kikayi, eh mn, waima mai ya hanaka zuwa school yau, Nisha ke tambayan sa,
lah yaufa weekend kin manta ba school , oh haka na manta , suna cikin hiran tasu su fareeda suka shigo daya nabin daya, suka karisu suka zauna, hanun fadeela dauke da chocolate suna sha, fadeela ne ta ajiyewa Nisha ledar acinyarta tana fadin," ga chocolate kisha, nan sha ta bude ledar tadauki daya tabare tasuma sha har wani lumshe ido take aikin dadi, nisha na kaunar chocolate sosai,
Nan Nisha takalli aheel dake kallonta shima tana fadin," kaima kadauka kasha mana, nan yakai hanu zai dauka reeda tabuge hanunsa tana fadin," mai zakayi, Aunty nima sha zanyi yafada tareda marairaice fiska, fadeela ne ta amshi maganar da cewa" saboda kaine mai bakin kwadayi koh,? to muma ya kml ne yasammana kaima kaje yabaka yanadashi dayawa,
cikin hanzari aheel kuwa yazame daga bed din yana fadin," nima bari naje yabani, yafada tareda yin waje dagudu,
Da kinbarshi muma ba iya shanyewa zamuyiba, Nisha tafada tana kallon su reeda, ke kyaleshi yaje zamu iya shanyewa tunda muka dibo, Nisha bata kuma cewa komaiba sukaci gaba da hirarsu, wunin yau kam yamata dadi sosae because abokan hiran suna nan,
sede damuwarta dayane shine sanar da ammi batun fita, dan haka da batun takwana aranta,
Washe gari da suba suka tashi sukayi wanka tareda alwala suka yi sallah kamar yanda suka saba, su fareeda suka suma shirye shiryen tafiya skull domin kuwa 7 a mkrnt yake musu, dan haka basu tsaya wani dugun breakfast ba coffee kawai sukasha suka wuce,
nisha kuwa tana kammala karatun Qur'an da tasaba ta koma takwanta, batayi wani wacci mai tsayiba sbd atunanin ta ammi 10 ma baya mata a gd,
wajan 8:45 Nisha tasamu daman farkawa, dan haka ta sakko daga gadon tanufi hanyar parlour takoyi sa'a can dining ta hangi ammi na break dan haka tasamu daman karisawa dan su gaisa,
cikin fara'a da nuna kulawa ammi ke kallon nisha tana fadin,"har kin tashi, cikin murmushi nisha tace,"eh ammi natashi, ae na dauka se 10 kamar yanda kuka saba ammi tafadi tana dariya, murmushi nisha tayi batare da tace komaiba,
to maza kizauna kiyi break ammi tafadi tareda turawa Nisha kan abinci gabanta, hanu Nisha takai ta hada tea tafara sha, daga bisani tadauki pancake tana ci tana mai satar kallon ammi yayinda take karyawa,
bari natashi nashirya karna makara ammi tafada yayinda take mikewa ta haura sama tanufi bedroom dinta,
Seda nisha tagama karyawa sannan ta tashi tareda komawa parlour tazauna tana jiran sakkowan ammi, ba a wani dade ba , ammi ta sakko cikin shirinta mai kyau gwanin shaawa,
ido Nisha ta tsurawa ammi yayinda bakinta me bari tana kokarin cewa wani abu, ganin kallon da Nisha ta tsare ammi dashi yasa ammi fadin," lapia kuwa Nisha akwai abunda kikeson cewane ammi tafa yayinda take shafo gefen fiskar nisha,
kifadamin inkinda bukatan wani abu tafada cikin yanayi na kwarin gwiwa, dama kawata salma aka kawo kayan aure shine nakeson naje nagani nisha tafadi tareda sunnar da kanta kasa tana wasa da yan yaysunta,
murmushi ammi tayi na Fadi,"shine kuma baki fada tun jiyaba, gashi ina sauri da na ajiyeki, amma bakomai yanzu kiyi sauri kije kishirya sena saukeki, ammi bazansa ki makaraba, tafada tana kallo ammi, a no ba damuwa da sauran time, kije kishirya ammafa karki bata lokaci ammi ta fada yayinda tasamu gu tazauna,
cikin rawar jiki da murna Nisha tashiga daki dan shir yawa, kamal ne yashigo parlourn ya tarar da ammi zaune bisa kujera yayinda hanunta ke latsa wayarta, sallma yayi tareda kokarin karisuwa kusa da ita,
nan ya zauna ya gaisheta ta amsa fiskarta daukeda murmushi, kallonsa tayi tana fadin," lapia kuwa naganka cikin jallabiya, ina shirin office din, ,? dan wani guntun tsaki yaja yana fadin," kai nifa ammi yau banajin zuwa office dinnan, why ammi ta tambaya, yau banajin dadin jikinane sosae shiyasa,
maganar ammi keda wuya Nisha tafito cikin shirnta mai kyau, fiskarta daukeda murmushi, amma ganin kamal murmushi da annashuwar dake fiskarta dip yadauke, gani fitowar nisha yasa ammi tana fadin," yauwa kin fito ko to semu samu mutafi dan nakusa makara, ahankali neesha take daga kafarta sbd yanda taji kafarta yamata nauyi,
yayinda idon kamal kuwa ke kanta, ammi ina kuma zakuje nazaci office Zaki, kokema yau zaki hutane, kamal ya tambaya, no yanzu zan wuce nisha nakeso nasauke gdnsu friend dinta salma, cikin tare ammi da magana kamal yace,"
haba ammi keda zakitafi office maizai kaiki da wani biye biye, aiseki makara kisa driver yakaita mana, ko kibari nina sauketa, yafada yana satan kallon Nisha,
wow da kate makeni domin kuwa nakusa makaran please ka tai maka kasauke min ita , ni bari na wuce tana fadin haka tayiwa nisha sallama tayi fice warta,
Nisha kam kamar wacce aka dasa agun batayi gaba ba batayi bayaba, jitayi kamar tafasa fitan, har kamal yafita yakoma dakinsa yacanza kaya ya dawo Nisha na tsaye inda yabarta,
jin inuwar mutum kusa da ita yasa tadago takalleshi tareda dan zaro ido waje, kallonshi take sosae cikin shiri maikyau, yayi kyau dashi kamar kasaceshi kagudu, kamarsu ya kara fitowa sosai da brothern shi AJMAL, sedan haske da AJMAL yafishi danshi yaynsu ba inda yabar mahaifinsu, mujeko abunda kamal yace kenan yana dan murmusawa juyawa yayi yafice, itama bayanshi tabi .
ahankali take tafiyan kamar wacce kwai yafashewa aciki har ta karisu jikin motar, kamal duk yana kula da yanayinta, bude mata motar yayi ganin tashiga yasashi maida kofar motar yarufe, nan shima ya zagaya yashiga motar tareda sawa motar key,
tunda suka hau titi suka suma tafiya bawanda yacewa da uwansa kala, kamalne ke sauraren sautin wakanda yakunna yana mai bin mamin din wakar, yana satar kallon Nisha wacce kanta ke gefe tana kallon hanya,
baki fadamin inda zakijeba, ko mucigaba datafiya se inda mai dinmu yakare, kamal ya watsawa Nisha tambaya, dan jiyuwa nisha tayi tana fadin," nasarawa, bansan wajanba kamal yafada yana mai cigaba da kallon titi, zuro taimasa da ido ganin cewa komaiba still kuma tacigaba da tuki, tama kauda kai gefe tayi tana mai maganar zuci,"
dama kaida ba dan gariba taya zatasan gari, shiru tayi tareda zubawa sarautar allah ido, amma ga mamakinta segasu a anguwar, yana tsaka da tukin ya dan jiyu yakalleta yana Fadin," sekuma ina zamuyi,
yo kuma kace bakasan unguwar ba yanzu waya kawomu ,?Nisha tafada cikin zuciyarta, kinyi shiru kamal yafada yana mai kokarin tsaida motar,
dan tsuke fiska Nisha tayi daga bisani tashiga masa kwancen ida zasuyi har suka karisu kofar gdnsu salma,
daga gefe ya tsaida motar yayi parking, hakan yabawa Nisha daman fitowa daga motar, tafara kokarin maida kofar tarufe, jin muryan kamal nafadin," karki bata time yasa taja tatsaya tana fadin," nifa zan kai yamma, aina kenan kamal ya tambaya, nan Nisha tafada tana mai tura baki,
ina tunanin baki da labarin gdn ALH ABUBAKAR MODIBBO BATURE ba afita yawo balle asa ran za awuni kuma kema yanzu kina daya daga cikinmu, dan haka ki hanzarta inajira yafada tareda maida kansa ga wayarsa,
jiki ba kwari tamaida kofar motar tarufe tajuya tashiga gdnsu salma, da sallama tashiga cikin gdn tana dan wul wul ga ido,
salma ce tafito daga dakin, ganin Nisha tsaye cikin gdnsu yasa tazura da gudu tayi kan Nisha ta rungume ta, cike da murna da zumudi, yar halak ashe kina tafe, tafada tana washe baki,
bakowa gdnne ina ummyn naji gidan shiru, ummy bata nan faruk kuma yana makaranta tareda tareda jan hanun Nisha suka shiga ciki,
daga nakin gadon salma nisha tasamu tazauna tana kallon salma wacce itama Nisha take kallo, kawata kinga yanda kika kara kyau kike glowing har wani kumatu kikayifa, salma tafada tana jan kumatun nisha
Murmushi nisha keyi yayinda take kallon salma tana fadin," amaryanmuba mrs bello to akawomin lefen nima nabawa idona abinci, ko anrufe gani, Nisha tafada cikin tsokana, yo ko anrufe gani dole abude kigani tafada tareda jan hanun Nisha suka fita daga dakin,
dakin ummynsu takai nisha domin adakin ummy kan suke, nan salma tashiga nunawa nisha kayan arzikin da abun kaunar ta, ya aiko mata, masha Allah kawata kaya sunyi kyau sosai kawata tayi gishi nisha tafa tana zungorin goshin salma,
to yaushene bikin ko ba asa ranaba nisha ta tambaya, ba asa ranaba tukun kin kin matsu akaini koh, gsky kam namatsu shima kansa uban gayyan amatse yake Nisha tafada tana tabe baki, salma ce takaiwa nisha bugu tana fadin," kefa bakida m to karya akayine nisha tafada tana dariya,
.
sun dau dugun lokaci suna fira daga bisani Nisha tamike tsulum tana dan zazzare ido, sam ta manta da kamal dake jiranta awaje, salma bari naje gd ba kowa muku ana jirana awaje, salma tace," dawuri hk nadauka wuni zamuyi, zan sake dawowa nisha tafada cikin hanzari,
to bari na tattara kayan nan nazo na rakaki, to kawai Nisha tace tashiga tayata suka maida kayan, mayafi salma tadauka suka nufi hanyar fita,
fitowar su keda wuya gaban Nisha yafadi, ganin ba motar akofar gdn, wul wul ga ido tashigayi nan ta hangi motan daga can gefe yayi parking,
nanfa Nisha taja wani goron numfashi tareda kokarin yiwa salma sallama, to to ina motar da take jiran nakin salma ta tambaya, da hannu Nisha tayiwa salma nunin inda motar take a pake, yo inbanda abun driver meyena kai motar can kuma salon yasaki tafiya, dariya Nisha tayi tana fadin,"
maybe ya gyara parkine bari naje se munyi waya, to kawata nagode kigaida su Hajiya dasu reeda nima zanzo inna samu time insha allahu, to shikenan senaganki nan sukayi sallama sannan salma tajuya tashiga gdnsu, hakan yabawa Nisha daman barin kofar gdnsu salma tanufi inda ta hangi motan kamal,
tana karisawa tasa hanu tabude murfin kofar tashiga tamaida kofar yarufe, akife ta sameshi ya kife kansa kan siterin motar da alama bacci yafara daukansa,
jin motsin shigowarta Nisha yasashi daga kai yana binta da kallo da rinannun idanunsa da sukayi jawur dasu, harara ya watsa mata yana mai hade gira wanda yasa Nisha sunkuyar da kai kasa,
baicemata Kala ba yaja motar da wani irin gudu kamar mai shirin tashi sama, wanda hakan bakaramin bawa Nisha tsoro yayiba,✍️
🥀🥀 IG AJEEMAL 🥀🥀
Story and writing by Oum AmReesh ♥️
Free book 🥰 ga masoyana ina alfahari daku ina kuma godiya da fatan alkharin ku agareni
Page14, tunda suka hau titi suka suma tafiya bawanda yacewa da dan uwansa kala, har Allah yabasu da man karisowa gdn, jin karan hon kamar zai daga gdn yasa mai gadi yaye geat din gdn, nanfa yataka motar ya isa inda sauran motocin suke yayi parking,
nan Nisha tafada kokarin bude murfin kofar tafito, kicewa barka ta kawo min food, abunda kawai yace kenan, yafita daga motar cike da kasala kamar ka karba masa tafir yanda yake tafiyan kamar mara laka, itama fitowa tayi tanufi bangaran su,
bedroom dinsu tanufa tanemi gu ta kwanta, tana maida ajiyar zuciya, wani kewa taji yana ziyartar ta, duba da basu fadeela ba aheel abokin surutun nata, se Hajiya kawai,
hakan yabata daman mikewa tanufi hanyar kitchen tasanar da baba Barka sakon kamal, nan tajuya ta koma dakinsu,
tube kayan jikinta tayi tareda daukan towel tanufi toilet, wanka tayi tafito tana goge jikinta dawani karamin towel din, komai bata nemaba tanemi yar duguwar riga red color wanda su fadeela suka zaba mata lokacin da sukaje shopping,
rigar tayi matukar yimata kyau sosai, hula tasa akanta tanufi hanyar waje, bangaran Hajiya tanufa, tana zuwa ta tura kofar hadeda sallma abakinta, duguwar kujera ta hangi hajiya ta kishinfida da alman bacci tadumayi, jin motsin shigowar Nisha yasa tamike daga kwanciyar da take tana sakar mata murmushi,
Nisha karisowa tayi tareda samun guri ta zauna tana fadin," Hajiya sannu da hutawa, yauwa sannu Nisha, kindawo dazu nashiga ae natayaki fira Barka tace kunfita da kamal,
Eh gdnsu salma naje kallon lefen ta, ayya masha Allah kice salma kaya ya iso, kai Allah de ya sanya alkhari Hajiya tafadi, ameen Nisha tace, tanan suka shiga hiransu har wajan la'asar, daga bisani Nisha tamike tanufi sashinsu domin gudanar da sallah,
Hajiya ma tanufi bedroom dinta, Nisha tana shiga bedroom din toilet tanufa tayi alwala tafito tayi sallah , bayan idar wanta kamar kullum tashiga yiwa umma da abbanta addu'a da fatan alkhari,
tana kammala tamike tareda samun guri daga bakin gadon tazauna yunwa takeji sosae because tunsafe rabonta da tasawa cikinta wani abu kuma bata san cin abinci ita kade, tasaba ci tareda su fadeela, dan haka tazauna zaman jiransu,
jin hon din mota tashigo haraban gdn yasa Nisha mikewa, tanufi window domin lekawa taga waye, ganin cewa su fareeda suka dawo tasaki wani murmushi jin dadi, Allah kadai yasan miss dinsu datayi agdn yau,
nan takoma tazauna tana jiran shigowar su, ba adadeba sekasu sunshigo kamar yanda aka jefosu daya nabin daya,
washewa Nisha baki suka shiga yi yayinda suke karisa shigowa, reeda ce tasuma magana tana cewa," sannu da gd sis da alamar yau gdn nan bai miki nice ba, fareeda ne takarbi maganar dacewa,"
inafa zai mata dadi bama nan tafara cike da zulaya, don't worry kinkusa dena missing kema yayinda tamike saman bed tana sauke gajiya,
I'm feeling hungry wlh reeda ta fada tana shafa cikinta, nima yunwan nakeji fadeela tafada tareda mikewa tana kallon Nisha daketa faman zuba musu murmushi,
Ke kinci abincinne ko bakijin yunwane , aa dama kunake jira banajin dadinci nikadai, alright bari naje na kawo mana abincin, fadeela tafada yayinda tanufi hanyar waje,
tana zuwa kitchen tasamu baba Barka ta tsaka da aiki, ganin fadeela ne yasa ta tsagaita da aikin datake, tashiga washe fadeela baki tana fadin," yan matan daddy andawo, " wlh baba Barka kuma gashi yau mun dawo da yunwa,
shine nace bari nazo na daukar mana abincin, lah ae ai dakin koma abunki yanzun nan zan kawo muku, a no karki damu, bari nadauka dakaina, tana fadin haka takai hanu ta dauki food flas din abincin tareda plate din abinci, tafita tareda komawa bedroom dinsu, tana shiga ta baje musu kayan abincin saman capet,
nan ta tadauki plate tashiga saka musu abincin nan suka sakko daga bed din suka suma cin abincin, sunci suna dan hiransu , seda suka kammala Nisha da reeda suka shiga tattara kayan da sukayi amfani dasu suka maida kitchen,
bikin kml yanata kara matsuwa yau saura 2 weeks, yau gd yayi baban bakowa Hajiya rabi,
kamar kullum dasuka saba banyan gama breakfast dinsu sukan dawo parlour suzauna su dan taba hira, ammi yau bata fita office ba kasan cewa weekend ne ba aiki, Hajiya sesu fadeela, Nisha yau bata jin dadi maranta naciyo saka makon bakunta na wata,
ammi ta bata magani tasha sannan tasheda mata da ta kwanta tayi baccin ta tahuta, hira suke sosae cikin nisha di, jin sallmar da ake yasa suka zubawa kofar parlourn ido dan ganin mai shigowa,
gaggo rabice kanwar dadinsu ketafe hanunta dake da jakarta, cikin shirinta mekyau fiskarta ta dauke da murmushi yayinda take karisuwa ciki, bayanta dauke da mai gadi yana tafe da akwatin kayanta,
su fadeela ne suka tashi dasuri sukayi kanta suna fadin," oyo oyo gaggo sannu da zuwa, cikin farin ciki ta rungume yayan nata tana fadin," my daughter's kune kuka kara girma haka masha allah ashe nakusa na auradda yayan nawa mekukeci haka gaba daya kun dawo wasu broilers daku, tafada cikeda zulaya tana dariya,
cikin sunnar da kai alamar kunya suka shiga yimata dariya tareda kokarin karbar jakar hanunta, karisuwa tayi kusa da Hajj mama tazauna tana sakar musu murmushi,
Mutan kd irin wannan zuwan bazata haka, ammi tafadi tana kama haba, dariya goggo rabi tayi tana fadin," wlh kuwa dama cewa nayi zuwan bazata zan muku, Daddy ne kadai yasan da zuwana shima kuma na kwabeshi nace kar ya sanar daku,
carab Hajj mama takarbi zancen da cewa," a lallai kin sham macemu, ina mutumin nawa shima kwana biyu shiru kamar baya nan ku leko mutane bayayi,
dariya goggo rabi tayi tana fadin," muhaiseem wai , shifa Hajiya tafadi, yana uganda, yakusa dawowa ae shima zai zo bikin kml goggo, hmm Allah yasa nasan halin mutumin da kalula,
dariya sukayi daga bisani ammi tace," Allah yasa hutun da yawa akazo amana, dan kema kin dade rabunki danan,
kede bari ae yanzu se kungaji da ganin, dan har bayan auran kamal ina nan kusuda uwata dan tayi kewanta so much, tafada tareda kwanciya shouldern Hajj mama,
dariya sukayi Hajj mama nafadin," kede rabi bansan yaushe zaki girmaba har yanzu wani abu kike kamar yarinya , yo ba dole ba yar uwatan Hajiya guda ammi ta fada na dariya, ato nima shi nagani goggo rabi tafadi tana wani sake nukewa,
lah namance bamu gaisaba natsaya surutu tafadi tana dariya, nan tashiga gaishesu suka amsa cikin fara'a da muna suna tambayar ta ya hanya tace alhmdllh,
nan suka cigaba da hiransu cikin raha da nishadi, kiran sallan azaharne ya dakatar dasu daga hiran, daga bisani goggo rabi takalli su fareeda tace,yayan nan muje kutayani daukan kayana mukai dakin Hajiya, yo kaji matar nan ga dakuna da yawa agdn nan bazaki bari nasa baba Barka ta gyara miki inda kikeso kishigaba fadar ammi tana kallon, rabi ,
aa nikam yau ina kusa da Hajiya ta dakinta zan sauka because nayi kewarta, tafa tana kallo Hajj mama tana dariya,
shikenan to autar Hajiya se kudau kayan ku isa mata dashi, ammi tafadi yayinda take kallon su reeda, nan suka dauki akwatin kasan cewa akwatin biyun suka raba kowa yadauki dada suka fita, yayinda rabi da Hajiya suka rufa musu baya, banda ammi da ta nufi kitchen dan duba halin da baba Barka take ciki,
tana zuwa tasamu baba Barka takammala komai, nan ta tayata suka jera komai inda ya dace, daga bisani ammi tanufi bedroom dinta sallah, tana shiga tayi alwala tayi sallah tanufo kasa,
direct bedroom dinsu Nisha tanufa domin dubata taga awani hali takeciki, tana zuwa tasameta kwance tana bacci da almun baccin nata yayi nisa sosae, dafa koshinta tayi wanda yayi sanyi qlau da alamar zazzabin da takeji ya sauka, ganin tana zufa yasa ta dauki remote din AC ta kuna mata takuma rage fawanshi kadan, ahankali sanyi mai dadi dasa kwanciyar hankali ya lullube dakin nan taja mata kofar tafito,
akokarinta nafita su fadeela suka kunno kai zasu nufi bedroom dinsu, kukuma fa ammi ta tambaya, sallah zamuyi sukaba amsa atakaice, to kadde kutashi yarinyar nan , to shikenan karki damu baza mu tashe miki babynkiba suka cikin zolaya suna dariya suka she dakin nasu,
ammi ban garan Hajiya tanufa tasanar dasu abinci ya kammala sufito suyi lunch, rabi tashiga wanka bari inta kammala se mutafi gaba daya Hajj mama tafadi , okay ammi tace tareda da neman guri tazauna sukashiga hiransu,
bada wani bata lokaciba goggo rabi tafito cikin wani shiri maikyau shin riga da siket na atamfa tamata kyau kamar su yakara fito da dan uwanta wato daddy , rabi duguwar ce fara mai diri maikyau ga manyan idanu kasan cewa ba inda taba mamanta wato Hajiya,
duk da ta manyanta ga wanda bai santaba in aka fadi she karunta bai ce tayi wannan shekaruba, murmushi yasakar musu yayinda take karisuwa tazauna,
dama ke muke jiran fitowar ki, the food is ready, ammi tafadi yayinda take kokarin mikewa daga zaman datayi, suma mikewa sukayi tareda rufawa ammi baya suka wuce babban parlourn, domin cin abincin,
suna zuwa suka tarar da su fareeda suna zaune a dining table din suna jiransu, lallai fa har kun rigamu zuwa da alama yunwace takoroku, goggo rabi tafadi tana dariya, suma dariyan su fadeela suka kayi batareda sunce komai ba,
dukansu zama sukayi suka suma cin abincin sunci suna dan hiransu har suka kammala, nan rabi take tambayar Daddy a tunanin ta yau weekend ba aiki, ammi ta sheda mata yafita dan yasanar da ita yana da tattaunawa da wasu abokan hurdansu, but kafin dare zai iya da wowa,
yinin ranar bakaramin dadi yamusuba because goggo rabi tasamu kawo musu ziyara , kasan cewa rabi tana da barkwanci bata da matsala kokadan shiyasa suke kaunar zama da ita,
aban garan Nisha kuwa tayi bacci sosae yanda yakamata itace batasamu farkawaba se kusan goshin magarib, bude ido tayi amma takasa mutsawa ta tashi gaba daya jikinta amace yake, rinza ido tayi kamar wacce takoma bacci amma azahiri idonta biyu,
hanunta nakan maranta dayake dan murda mata da because dama dan baccin da tayine yasa tadan rage jin zogin, ta dauke dugun lokaci ahaka tana kwance idonta narufe, harsu fadeela suka shigo sukayi sallah suka sake fita duk akunneta tana jinsu ,
ganin kwanciyar kamar shike kara mata radidin datakeji yasa tamike har wani jiri jiri takeji, gaba daya tagama laushi, ahankali tasuma cire kayan jikinta, tareda samun towel ta daura tanufi toilet, wanka tayi sosae, daga bisani tafito tanemi kaya tasa,
ahankali ta taddafa tanufo parlourn ganin shiru ba alamar kowa aciki yasa tanufi inda tan suka saba zuwa, akokarinta nabarin parlourn, taci garo da AJEEMAL dake kokarin shigowa parlourn , kallon kallo sukashigayi, yana kallonta tana kallonsa da rinannun idanuwanta da suka canza launi,
dan jabaya yayi kadan yana sake dubanta kadan kamar wacce yau yataba ganinta, ita kuwa jiki se bari yake ganin irin kallon da papan aheel ke mata wacce itama batasan wani irin kallo bane wannan,
," follow me abunda yace kenan yafara kokarin juyawa, ganin batayi mutsiba yasa yajuya tareda cilla mata wani irin harara," ko bakiji abunda nace bane yafada cikin wata irin murya, " naji Nisha tace bakinta nabari, juyawa yayi itama tarufa masa baya,
tafiya take ahankali yayinda takejin zuciyar ta kamar zata faso heat dinta, tsabar tsoro,
part disa yanufa yatura kofar yashiga, nan ya tsaya tsakiyar parlourn yana jiran shigowar ta,
Nisha kuwa tsawa tayi a kofar parlourn takasa shigowa, tsoronta mai zai fada mata, "baza kishigo bane, nisha ta tsinkayi murya AJEEMAL yana tambayar ta, shigowa tayi ahankali tareda sake bude kofar dakyau because in abun yatashi naguduwa ne basetasha wahalar bude kofar ba, sede tafita da gudu, close the door and seat down here, yanuna mata saman capet, yana tsaye yana kallonta tamatsu ahankali ta tsuguna inda yanuna mata jikinta se bari yake kanta na sukuye kamar wacce ta aikata ba daidai ba,
🥀🥀 IG AJEEMAL 🥀🥀
Story and writing by Oum AmReesh ♥️
free book 🥰 ga masoyana ina alfahari daku ina kuma godiya da fatan alkharin ku agareni,
Page 14&15
ganin tasamugu tazauna hakan yabashi daman karisuwa bedroom dinsa, still kan Nisha nakasa, har yaje yadawo yasamu kujera nisa da ita yazauna tareda daura kafarsa daya kan daya, yana karewa Nisha kallo wacce kanta ke kasa cikin kakkausar murya yace," ke? cikin hanzari Nisha tadago takalleshi jiki nabari, hanu yamata almar ta kariso,
ahankali Nisha tashiga jan gwiwarta tana kokarin karisawa, seda ta iso dabda kujaran da yake zaune sannan tagyara zamanta saman capet hadeda sunkuyar da kai domin sauraron abuda zaice,
cikin natsuwa yake binta da kallo daga bisani yasa hanu ya dauke black back din dake gefensa yadaura bisa cinyarta yana fadin,"
take this and opened,
ahankali Nisha take bin jakar da kallo, hanu na bari tasa hanu taja zip din jakar tabude makudan kudadene aciki da alamar kudin bata kasar mu, nigeria bane,
I hope kin gane jakar kudinki? AJEEMAL yafadi yana dubanta, gabantane yafidi tadago tana kallonsa tana son jin karin bayani dan kwata kwata ba abunda yazo mata arai,
girgiza masa kai tashiga yi alamar aa tana kuma sake kallon jakar dake gabanta,
bana so na tambayi abu amin karya nakanyi hukunci, hukunci kuma mai tsawari , yana fadin haka yakuma yajin gina kansa da jikin kujera, "
doctor fu' ad shiya bani jakar nan kuma ya shedamin yarinyar da take gdnmu ita takai kudi domin ayiwa mahaifiyar ta aiki, kafin aimata aikin, allah yamata rasuwa,
tambayar da zan miki anan shine, ina kika sami wadannan kudaden, doctor fu'ad ya fada min cewa lokacin aka bukaci kudin ayinin ranar kika kawo, kuma yasheda mun kubamasu karfi bane kuma bakuda hanyar samun kudin da akeda bukata,,
Badole bane na bukaci nasan inda kika samu wannan kudaden ba, but yanzu kin kusanci familyna har kinsamu nasaran shiga zuciyar su, bugu da kari kinsa soyayyarki acikin zuciyar dana dana family,
dan haka bazan zuba ido wani abu yakawo mana shakko acikin family ba,
zan sake tambaya ki karo nabiyu, karkuma kimin karya hakan shi zai baki daman kwanciyar hankali gdn nan,"
so tell me wakika daukarwa kudi,? nina miki alkawari zansa a mayarwa maishi batareda kowa yajiba, yafa yana kallonta,
Nisha kam tunda yasoma mgn hawaye suka shiga wanke mata fiska, tarasa mai yake mata dadi, tabbas wannan kundin da kamal yabatane ,
to amma Allah yagani bazata iya sanar da AJEEMAL cewa kamal ne yabataba, bakiji mai nace bane AJEEMAL yafada atsawace,
cikin hanzari da rudu Nisha tace,"
wlh tallahi ba wanda na daukarwa kudi kuma ni tunda nake banta daukarwa wani kudinsaba bani akayi tafada tana shashshekar kuka,
Gyara zama AJEEMAL yayi tareda fadin," okay who are given ,? kuma wani aiki kika masa yabaki, cikin hanzari Nisha tadago tana dubansa because takasa fahimtar inda zancensa ya dosa, wani kuka tarushe dashi jin zarginda yakeso yalika mata,
wani guntun tsaki yaja yana fadin," nifa ba kuka nakiraki kiminba tambayar ki nake kuma amsa nake bukata, ganin bata da alamar amsa tambaya shi, yasashi tsagaitawa yana sauraron kukanda take rerawa,
ganin zasu batawa juna lokaci yasashi cema ta tashi tabashi guri daga ita har jakar kudin nata, jin haka yasa Nisha tamike dasauri daga ita har jakar fuuuu tayi waje da gudu tana kuka,
AJEEMAL bin bayanta yayi da wani harara hadeda guntun tsaki gaba daya yasakejin tsanar yarinyar acikin zuciyar sa, kalleta is too young amma tana kokarin bata rayuwar ta akan wani dalili,
jin aheel yafado cinyarsa yasashi dawowa daga tunanin da yatafi, dagoshi aheel AJEEMAL yayi yana kallonsa yana fadin," katshi, eh papa, aheel yafada yana duban mahaifin nasa,"
papa mai kayiwa aunty naga tafita tana kuka, AJEEMAL bin yaro yayi da kallo wato da alamar yaga abunda yafaru kenan, bakomai AJEEMAL yafadi tareda mikewa yamaida aheel kujara ya zaunar dashi, jirani anan bari naje nayi sallah na dawo,
aban garan Nisha kuwa tunda tabar daki tafi waje, tasamu daga gefe talafe tana share hawayenta , seda tabbatar bakowa haraba gdn hakan yabata daman shiga parlourn ahankali, duba da cewa bakowa parlourn yasa tazura dagu tayi dakinsu, waje tasamu daga bakin gado tashiga rera kuka mai cin rai, tana tuna kalaman AJMAL dayayi akanta, jakar hanunta takalla tana fadin," dole namaidawa da kamal kundinsa , yanzu damuwarta daya, ina zata ajiye Wannan jakar kafin haduwan su da kamal, dan tabbas a deran yau takesun tamai da masa, kuma batada bukatar kowa yasan da kudin har ta maida masa, because bataso kowa yasan tasan kamal tunkan zuwanta gdn
jin muryoyinsu fadeela da alamun sunshigo parlourn yasa tayi saurin sunkoyawa kasan gado ta tura jakar kudin tareda mikewa tanufi saman bed takwanta ta lumshe ido tamkar mai bacci,
su fadeela suka shigo bedroom din daya nabin daya suka karisu tareda haura saman suna fadin,"haba wakiup mn, tundazu se bacci kike ko abinci bakiciba,
bude ido nisha tayi ahankali da idonta ya kubura tsabar kukan da tasha, ganin haka yasa reeda tace,"what happened Nisha, naga idonki ya kubura kamar wacce kikayi kuka,
ko cikin nakine bai daina ciyoba haryanzu fadeela tafadi tana kallonta cike da tausayawa, mikewa Nisha tayi tazauna tareda kallonsu tana fadin," ciyon cikin nan ya matsamin dayawa, haryanzu bai dena ciyoba,
okay to yanzu kitashi kizo muje muci abincin daga bisani sekisha kikara shan magani ki kwanta reeda tafadi tana kallonta,
banjin yunwa bazan iyacin komaiba yanzu, bayadda basuba dan ta bisu suci abincin amma sam taki, ganin haka yasa suka fita daga dakin, suka nufi parlour,
a dining ta tarar dasu ammi dasu Hajiya da goggo rabi suna zaune suna jiransu, karisuwa sukayi suna kokarin zama ammi ta tambaya ina sukabar Nisha nan suka shiga zaiyanu mata yanda sukayi,
amma ae bai kamata mara lapia yazauna da yunwa musamman da kukace tun breakfast bata sakecin komaiba, fadin goggo rabi because already dama su Hajiya sunbata labarin Nisha ahiransu na dazu sun sanar da ita komai,
bari mu kammala zanje nasameta dakaina ammi tafada, daga bisani suka shiga fara cin abincin su, suna dan hiransu , seda suka kammala , ammi takai hanu tazubawa Nisha zazzafan pepper soup na kayan ciki da jalop din kuskus yaji salad tadaura akan try, tanu dakinsu Nisha,
kwance ta sameta, yayinda kanta ke kallon sama tanata sake sake cikin ranta, jin ana kiciniyar shigowa dakin yasa tamaida kallonta ga kofar, ganin ammice tashigo hanunta dauke da try din abinci, hakan yasa Nisha tamike daga kwanciyar datake tazauna tana kokarin kirkiro murmushi,
zama ammi tayi kusa da Nisha tana fadin," yajikin , tareda kokarin ajiye try din abincin saman capet,
hand dinta takai gefen fiskar nisha tana fadin," ahar yanzu cikin naki naciyo ne, gyada mata kai Nisha tayi hawaye na kokarin gangaro mata,
sorry gashi kuma bakisa komai acikin kiba tun safe shiyasa , yakamata kici wani abu maybe ma harda yunwar take kara miki ciyon cikin, tafada yayinda ta dire mata plate din abinci gabanta,
maza kici kidaure kitaba kokadanne, ammi tafada yayinda takai mata 1 spoon bakinta, karban spoon din tayi tasuma ci ahankali, yauwa inkingama ga plate din pepper soup ma yana jira acinyemin shi tass,
hakade nisha ta dan ci abincin, tanaci ammi na tsokanarta, seda ta tabbatar taci sosae takyaleta, ta dauki try din abincin tana fadin," bari naje nadawo, bayan ammi Nisha tabi da kallo nan da nan tafashe da kuka, because yanda taga ammi na kula da ita sekace daga cikinta tafito,
tadauketa kamar yarda ta haifa, kular da take bata kosu fadeela batabawa, jin shigowar ammi yasa tayi saurin hadiye kukan da takeyi tashiga mis mis da ido,
ammi magani tabude tabawa Nisha hade da ruwa, nan nisha ta karba tasha, daga bisani ammi tace mata takwanta tayi bacci,nan tai mata seda safe tayi ficewarta,
parlourn ammi takoma tazauna aka cigaba da hiran da ita, " oo yau kama ganin Daddy yamin wuya bacci nakeji but kuma inaso naga dawowar daddy, yau tunda nazu daga MODIBBO har kamal bawanda nasa aido, shima daddyn shiru haryanzu goggo rabi tafadi cikin jimami,
da kinyi hakuri ma ibaki gansu yauba zaki gansu gobe, Hajj mama tafadi,
dariya ammi tayi tana fadin," wlh kam dan seta gaji da ganinsu, nan suka cigaba da hiransu har wajan karfe 9:30 daga bisani goggo rabi ta mike tana musu seda safe domin kuwa tagaji tana bukatan hutu,
suma mikewar sukayi domin kuwa dare yayi kowa da alamar baccin aidonsa, nan suka shiga yiwa juna seda safe kowa yawatse yanufi turakarsa banda ammi da tazauna zaman jiran shigowar Daddy,
se guraren karfe 10 Daddy da kamal suka samu daman dawowa gd, daddy parlour suka shigo tareda kamal, ganin shigowar su, ammi tashiga musu sannu da dawowa, jakar daddy dake hanun kamal ammi ta karba tana tambayar su, akwai yunwa ko babu domin tasa barka ta kawo musu abinci, nan suka shaida mata ba mai bukatar wani abu yanxu,
nan kamal yamu seda safe yafice daga parlourn yanufi bedroom dinsa, ammi da Daddy suma suka haura upstairs sukanufi nasu dakin, anan ammi take shedawa Daddy zuwan kanwar sa, goggo rabi,
su fareeda tuni sunyi nisa da bacci banda Nisha da tayi lumui kamar mai bacci, sedata tabbatar baccin su yayi nisa hakan yaba taman lallabawa ahankali ta sauka daga bed din,ta sunkuya tareda zaro jakar daga kasan gadon cikin sanda tanufi hanyar waje,
🥀🥀 IG AJEEMAL 🥀🥀
Story and writing by Oum AmReesh ♥️
Free book 🥰
Page 16&17
kofar parlourn abude yake hakan yabata daman budewa ahankali ta fita, gida yayi shiru alamar dare yayi sosai, cikin tsoro tanufi sashin kamal, gaba daya tsoro yakaba kamata amma itade sotake jakar kudinnan yabar hanunta,
Knocking tashiga ahankali, badawani bata lokaciba taji anbude kofar, cikinsa saye da jallabiya babu alamar fara bacci atare dashi,
tsayawa yayi yana binta da kallon mamaki me yakawo Nisha ban garnasa awannan time din, ganin yanda jikinta ke rawa hanunta rike da jaka, hakan yabashi daman fadin,"
what happened yafada yana kallonta cike da mamaki, ganin bata bashi amsaba se waiwai take hakan yasa yasake fadin," come in tareda bata hanya tashigo, cikin sauri tashige kamar mara gsky,
daga door din ta tsaya hade da sunkuyarda , bakinta se rawa yake dake ta iya bude baki tana fadin,"
please kamal I'm sorry for the foolish for you nasan ban kyauta ba .
kataimaken lokacinda bamai taimakona daga bisani kuma na mance dakai for now kuma danazo gdnku bun hadu but haduwa dakai yazama aiki agareni,
allah yagani ina matukar kunyar ido dakai, because baza karasa sani jerin masu butulciba,
cikin shashshekar kuka tareda sake kasa dakanta hadeda mika masa back din tana fadin,"
ga jakar kudinka daka bani domin ayiwa mahaifanta aiki allah bai nufaba ya karbi rayuwarta
ba samu damar amfani dashiba nagode,
shiru yayi hade da kallonta cikin tausayawa,shima yasan ba haka banza take gudunsaba, tawani ban gare kuma yayi farinciki kasan cewarsu tare gata gashi, hakan yamasa dadi kuma yaddai dasanin wannan ranar zatazo,
hanu yasa tareda amsar jakar hadeda jan wani goron numfashi, baki yabude da nufin magana ga mamakinsa tajin ya amsa jakar tabude kofar ta kwasa da gudu tafice,
wani cool smile yasake tareda sake rufe door din dakyau batareda yasa key ba because dama bacika sa key a door dinsaba,
komawa yayi yazauna kan sofa dake parlourn tareda daura back din saman table yana sake murmushi,
mikewa yayi kan sofan kamar wani mai Shirin yin bacci , murmushi yadingayi kamar wani zararre because allah yaga zuciyar shi, yana matukar feeling din soyayyar Nisha da kaunarta acikin heart
duk dacewa yasan batama san yanayiba, gefe kuwa inyatuna da bikinsa da nabeela yakusa seyaji duk ransa yabaci dukda yasan aikin gama yariga yagama manya sunshiga cikin lamarin,
wani bangaran kuma tunani yake namiji mijin mace hudune to amma yasan azababben kishi irin na nabilah, but komade mainene yasan yana kaunar Nisha kuma zai sanar da ita ,
Ahaka yaita juyi yana tunani, har bacci barawo yayi awun gaba dashi nan saman sofa,
Aban garan Nisha tunda ta watsa aguje tafita, tana zuwa parlourn cikin sanda tashige bedroom dinsu because kowa yadadai da bacci, ahankali tasamu tanemigu ta kwanta,
Washe gari da suba kamal nakwance kan sofa yana minshari, AJEEMAL ne yashigo domin tashin kamal sutafi masallaci kamar yanda suka saba,
yana sanye cikin jallabiya biya kamar wani balarabe yayi kyau dashi, ganin kamal kwance kan sofa ba bedroom saman bed dinsaba , han yasa yamatsu yashiga tashinsa,
ahankali kamal yafude ido domin ganin waye yakatse masa wannan kyakykyawar markin dayake tareda gimbiyarsa Nisha, dan zunburo baki yayi kamar wani baby, ganin yayansane yazo tashinsa sallahn asuba, hakan yasashi tashi ya mike hade da yin mika, yanufi bedroom domin yin alwala , ganin yashiga bedroom hakan yabawa AJEEMAL daman kokarin juyawa yafita, karba idonsa yasauka kan jakar dake daure saman table,
sosai yakebin jakar da kallo domin harsashinsa na tabbatar masa da wannan jakar da yabawa Nishane jiya, to me jakar takeyi anan kuma AJMAL ya tambayi kansa, hakan nanufin kamal ne yabata koyaya ko kuma ajiya takawo masa yashiga tambayar kansa , abun yayi matukar bawa AJMAL mamaki,
to ko sunsan junane dama,? dan babu abunda zai kawo back din nan wajan kanisa sede dama shi yabata, to komade mainene akwai time din da zai bukaci sanin hakan yafada cikin zuciyarsa,
juyawa yyi yafita abunsa yakoma inda Daddy ke tsaye yana jiransu domin tafiya masallaci, " ina kamal din Daddy ke tambayan AJMAL bekaiga bashi amsaba, kamal yafito hakan yabasu daman wucewa duka,
su Daddy na dawowa duk suka nufi sashin Hajiya domin duba goggo rabi sugaisa because yau Daddy da kamal da wuri zasu wuce office , shikuwa AJEEMAL tuni yawuce part dinsa domin yasanar dasu kansa na ciyo da safe zaizo sugaisa,
aban garansu fadeela kuwa bayan ammi ta tashesu, wanka sukayi tareda alwala suka fito sukayi sallah, suka shiga shirin makaranta kamar yanda suka saba, banda Nisha daketa sharan baccinta because tana up,
yau seda suka tsaya sukayi breakfast mai dan sauki Barka tamusu sukaci , daga bisani suka tattara izuwa part din Hajiya domin rage time because yau akwai sauran time nan suka tarar dasu Daddy da kamal tareda ammi an kacame da hira da raha da wasa nanfa suma suka shiga aka cigaba da damawa dasu,
se wajan 8 sukayiwa su ammi sallma suka wuce, haka su Daddy da kamal basu dadeba suka tashi kowa yanufi bedroom dinsa dan shiryawa, nan ammi tanufa musu baya tanufi kitchen domin shiryawa Daddy nashi breakfast din, bayan ta kammala komai nan ta haura upstairs tanufi bedroom dinsu, ba adadeba suka fito tareda Daddy suka nufo downstairs , dining suka nufa Daddy ya zauna nan ammi tashiga zuba masa abunda yakeso tamika masa tareda hada masa coffee, nan yasuma ci, kamal yashigo shima cikin shirinsa maikyau gwanin shaawa, yazauna yashiga karyawa shimade ammince ta zuba masa abinci ta tura masa gabansa yadauki spoon yasunaci,
suna kammala wa, suka mike kamal yakarbi jakar hanun Daddy suka nufi hayar fita ammi na musu asauka lapia, nan ammi tashiga domin sanar da barka cewa adaura wani girkin, nan tabata umurnin abunda za adaura daga bisani tafito wajansu goggo rabi suka cigaba da hiransu, se guraren karfe 9:30 suka tattara izuwa babban parlourn domin karyawa,
kamar yanda ammi tashedawa barka haka tayi takammala komai tajere inda yadace, suna suwa suka zauna a dining din, nan kuwa yashiga diban abunda yakesu yaci,
seda suka kammala, ammi tamike tanufi bedroom dinsu Nisha domin dubata , koda tashiga sesamu tayi ta tashi daga bacci saka makon dazu datazo tasamu tana bacci,
Nisha kokarin mikewa tayi ganin ammi datayi tana shigowa yasa takuma tazauna daga bakin gadon tana kallon shigowar ammi,
Murmushi ammi tashiga yiwa nisha yayinda takariso tazauna kusa da ita, nisha Nisha tayi saurin dagawa ammi gaisuwa tana fadin,"
ammi brk da safiya antashi lapia, lapia kalau Nisha yajikin nake I hope everything is fine, gyada kai nisha tayi hadeda sunkuyar da kai kasa tana wasa da yan yatsun ta,
ammi ce tasake magana dacewa," to yanzu kitashi ki kimtsa seki fito parlour kiyi breakfast ammi tafadi yayinda tamike tsaye tana sake fadin," ki hanzarta nima bari nashirya nazo nawuce office karna makara, tana fadin haka tajuya tafita,
nan Nisha tayi hanzarin fadawa toilet tayi wanka tafito jikinta daure da towel tazauna kan stool din dake wajan dress mirror tazauna tashiga shafa mai tamulke ko ina ajikinta, yar Hoda tanema tadan shafawa fiskarta tareda lipstick , baby face din nan takara kyau, mikewa tayi tanufi hanyar ma ajiyanda kayansu yake, tanemi wani riga da wando pakistan red color wandon white color mayafinsa ma haka, tasaka tareda daura mayafin ahakanta tafito mekyau da ita kamar wata ba india,
parlour tanufo bakowa a parlourn, jin mutsin ammi nakokarin sakko daga downstairs cikin shirinta nazuwa office hakan yabawa Nisha daman tsayawa tana jiran sakkowan ta,
ammi ganin Nisha datayi tasaki wani kayaceccen murmushi takariso tana fadin, wow my daughter kinyi kyau sosai, sankuyar dakai Nisha tayi tana dan murmushi batareda tace komaiba, muryan ammi taji tana fadin," yanzu se kikarisa dining breakfast najiranki, nibari nawuce se nadawo, Allah yakiyaye hanya nisha tafadi, ameen thanks my dear ammi tafadi tareda sakai tafice,
nisha karisawa tayi tazauna bisa table din dinning tashiga farayin breakfast, seda ta kammala tamike domin nufa part Hajiya because wunin jiya kaf batazo anyi fira da itaba,
tana isuwa kofar parlourn takejin muryoyinsu ana kyakyatawa hada wata bakowar muryan da bata san da itaba, da sallama abakinta tareda tura door din tashiga, zaune suke goggo rabi nagefen Hajiya,
.
ganin Nisha dasukayi yanda dakatar da daga hiran dasuke suka tsura mata ido suna jiran karisowarta, ahankali takariso hade da dukawa kasa tashiga gaidasu,
amsawa sukayi cike da fara'a da sakin fiska, musamman goggo rabi ganin yarinyar datayi taji ta kwanta mata a rai tashiga zuciyar ta itama, ga mamakin Nisha seji tayi goggo takamu hanunta tareda zaunar da ita akujera tana fadin," ko bancanki daidai nasan wannan beautiful girl din kuke bani labarin ta, tafada tana kallon Hajiya, itacede kincanki daidai Hajiya tafi tana murmushi, kai irin wannan kyakykyawar flower gaskiya nayiwa muhaiseen dina kamu goggo rabi tafadi tana dariya hade da sake kallon Nisha, to seki fada masa yashirya dakyau ban tsan manin zai sami nisha abagas dan haka kema se kitayashi shiryawa, Hajiya tafadi tana yar dariyan itama,
Nisha ma dariyan take kasa kasa hade da sake kasa dakanta tana wasa da yan yatsunta, duban Nisha goggo rabi tayi na fadin," baki sanniba koh, gyada kai nisha tayi alamar eh, ni goggonsu fadeela ne , kanwar Daddy, but as from now kuma nazamo cikin jerin sirikar gdn nan domin nayiwa dana kamu kafin ace wani yarigamu goggo rabi tafadi cikin zolaya, dariya sukayi yi dukansu, lokaci AJMAL ya kunno kai cikin parlourn hadeda sallma,
Karisuwa yayi yazauna ganinshi da goggo rabi tayi tashiga suma masa tsiya tana fadin,"
yanzu MODIBBO yau kwana daya a gdn nan amma ko lekoni bakayiba konayi laifine ansakani cikin magarkama baza azu inda nakeba, halama bakasan da zuwanaba, tafadi cike da zolaya,
dan murmusawa yayi wanda hakan yakara kawata fiskarta shi kyansa yakara baiyana, yana fadin," nasani but bana jin dadine kaina kedan ciyo tunjiyan shiyasa ban lekoba, ayya sorry yajikin rabi tafadi, alhmdllh yafada atakaice, nan yashiga gaishesu, seda suka gaisa sosae daga bisani yamike yana kokarin fita,
murya Nisha yatsinkaya tana gaishesa wacce dama jiratake sugama gaisawa dasu goggo rabi seta daga masa nata gaisuwan, amsa mata kasa kasa yayi daga bisani yasa kai yafice,
Nisha tabe baki tayi dama tunshigowarsa bawai tayi niyar daga nasa gaisuwa bane sa a kawai yaci because abunda yafaru jiya da magan ganu dasharri da kokarin maidata shasha da yasuyi, yanzu tsoransa datakeji ya ragu sema dan hashi daya fara bata because taga kamar bakin hali gareshi ba kamar kamal ba shiyada dan sakin fiska da magana mai Dadi,
🥀🥀 IG AJEEMAL 🥀🥀
Story and writing by Oum AmReesh ♥️
Free book 🥰 to all fans lovers I love you so much
Page 18&19
Oh ni rabi haryanzu MODIBBO yana nan da wannan miskilanci nasa goggo rabi tafadi tana kallon Hajiya tareda kama haba,
ke kinsan mutumin naki tun yarintarsa haka yake yanzukam ma se abunda ya karo Hajiya tafadi tana yar dariya,
aini nadauka yanxu miskilancin yaragu because yanzu ga mata ga da ashe abun sake girmama yayi, kodayake itama matar tasa miskilarce but itakam ma ya hadu mata da bakin hali da rashin kunyar tsiya Kai Allah de yakyauta goggo rabi tafadi tana tabe baki, ameen Hajiya tafadi,
Nisha kam shiru tayi batace komai ba tana sauraron su ,
sunyi hira sosae awannan ranar Nisha tasake da goggo rabi kai kace dama can suntaba sanin juna, kasan cewa goggo rabi macece mai wasa da kuma barkwanci dason mutane dakuma sakewa dasu, musamman Nisha data kwanta mata arai,
yau Wednesday anshiga satin bikin kml su fadeela suka shirn fita wanke kai, Nisha tanajin su, sunayiwa kamal tsiya suna fadin yau tareda ango zasu fita,
sun shirya tsaf daga bisani suka fito waje tareda nufar sashin kamal,
Nisha batabi bayansuba tsaya tayi daga bakin kofar parlourn tana jirasu suje su dawo daga nemo maganar dasuka tafi,
part din su aheel Nisha tabi da kallo tanajin kewar aheel aranta , tayi kewar aheel sosai, sauda dama setayi tunanin tashiga bangaran su ko asace domin taganshi setaji tana tsoro bazata iyaba,
duk da tayi alkawarin bazata sake ko kallon inda sashensu yakeba because papansa yaso yamai data shasha yana mata kallon mai halin bera,
tunda take ba wani mahalukin da yataba kwatanta yimata irin wannan kallon , har tambayar ta wani aiki tayi aka bata kudin, to meyake nufi watoma ni yar iskace komai yakeso Fadi ,?
ganin ranta yasuma baci yasa takauda wannan tunanin aranta, nan tafara kokarin nufa sashen Hajiya domin su dan taba hira irin na wancan ranar,
dan bakaramin jin dadin hira da goggo rabi takeba, karab idonta ya hango mata raheela dake tafe tana tin karota, ganin haka yasa Nisha hanzarin kokarin shiga sashin Hajiya,
.
hey you, where are going , jin haka yasa Nisha tayi kokarin jinkirta tafiyar datake,
ina kuma zakije naga kina kokarin guduwa, raheela tafadi tareda da hararo Nisha
magana nakeson nayi dake kuma ba komai tsawo bace, kallon up and down heela tashiga yiwa Nisha tareda sannan ta tabe baki tana fadin,"
nadade ina bukatar ganinki but time bai bani daman hakanba amma yau nakashe duk wani uzuri dake gabana domin na gargadeki nakuma miki kashedi naja kunnenki,
this is the first and last da zan gargadeki akan aheel daga yau inaso kifita aharkansa ko inuwa daya banason kusake hadawa, domin nagane take takenki dakuma inda kika dosa,
tunda kinsamu shiga zuciyar aheel shiga zuciyar mijina baizai baki wahala ba because kinga yanason danshi sosai, to kisani IG ba irin mazan da ake saye zuciyarsu da sauki bane,
let me tell you something inma turoki akayi domin shiga Wannan ahalin gdn nan to kitsaya iyaka bangaransu but karkishiga hurumina,
domin kuwa wani gigi yadebeki kika kuskure to ina mai tabbatar miki.... ganin su fadeela sunfito daga part din kamal yasa ta tsagaita da abunda takeson Fadi dan haka seta saki wani shuumim murmushi hadeda dan jan kumatun nisha tana fadin,"
be careful your self se anjima tana fadin haka tajuya takoma part dinsu
Nisha kam shiru tayi gaba daya abun yagama bata mamaki tabbas se hali yazo daya ake abota daga shi har matar tasa kusan daya suke, gaba daya jitake magan ganu heelah suna mata yawa cikin kanta,
jitake kamar ta tattara ta gudu daga gdn takeji wanna wani irin rayuwace daga wancan se wannan,
toma inbanda abunta maima zatayi da mijinta wannan shugaban yan bakin halin itade gani take ko kyauta akabata shi bakarba zatayiba dan wannan miskilanci nasa se itan,
Nikuwa nace,( ajura zuwa rafi domin kuwa IG nada banne baki fahimci mutumin bane kuma bakowa yake iya fahimar saba,)
what is going on,? mai wannan rasa kuyan take fadamiki, reeda tafadi tareda dafa shouldern Nisha wanda yayi saurin dawo daga ita daga dunyar tunani data wulla,
kirkiro murmushi nisha tayi tana fadin,"bakomai, gwara kifa dan san ba alkhari yakawotaba fadeela tafadi tana kallon Nisha,
dariyanda baije zuciba nasha tasake tana fadin," aa nikam ba abunda tafadamin,
Alright mukarisa part din Hajiya mujirashi ya kamal din reeda tafadi tareda shigewa suma suka rufa mata baya ,
da sallama suka shiga dakin suka tarar dasu suna tsaka dan hiransu, karisa shigowa sukayi tareda neman guri suka zauna, Hajiya ce ta kallesu tana fadin," dama bakutafiba har yanzu , eh Hajiya kamal muke jira shizai kaimu,
goggo rabi ce takarbi maganar dacewa," kai amma ya'yan nan da neman magana kuke, yo ga driver agd amma se kun gajiyar da angon namu tun yanzu,
To ai daga yaune gabama ba ganinsa zamuyiba balle muce yakaimuba koya fadeela tafadi tana kallon reeda, eh mana shidama ba zama yake akasarba
daga andaura aure zai dauke matar shi suwuce canada Allah sarki lovely bro zamuyi miss dinshi tafada tareda yin raurau da ido kamar mai shirin yin kuka ,
jin maganar da reeda tayi ba karamin sanyi jikin Nisha yayiba jin kamal bayan daura aure zasutafi, jitayi kamar itama ta taya reeda kukan suyi tare
yo da allah kujimin yarinyar nan, insun tafi tabbata zasuyi acan, goggo rabi tafadi tareda kama haba tana kallon Hajiya,
Dariya dukansu suka bushe dashi, shigowar kamalne ya dakatar dasu daga nishadin dasuke ciki, karisuwa wa yayi yasamugu shima yazauna, nan yashiga gaisawa dasu Hajiya daga bisani goggo rabi tabige da tsokanar shi tana fadin,"
ikon allah kai yanaga angon jibin namu sewani fresh yake kara yine, meye sirrine ,kaiba amaryanba ,
inbanda abun ki shimafa angone dole kika canji Hajiya tafadi tana yar dariya, okay ashefa hakane sede naga kamar angon baya wani Happy sosae goggo rabi tasake fadi cikin tsokana,
shiru kamal yayi se dan murmusawa dayake Allah ne kade yansan abunda yake juyawa cikin ransa,
mikewa yayi yana fadin," mukam bari muje, kutashi muje kamal yafada yana kallon su fadeela, dukansu mikewa sukayi tareda yiwa su hajja mma sallma,
harsun kai bakin kofar parlourn suka tsinkayi muryan goggo rabi da fadin," afayiwa sirkata wankin kai yafi nakowa kyau harna amaryanma, tafadi tana dariya,
Kamal ne yajiyo ahanzarce yana kallon goggo rabi yana fadin," waye kuma sirkarki,? gatanan kana ganinta tanuna nisha da tasunkuyar da kai tana murmushi dan tasan halin goggo rabi da zolaya,
dan murmushin yake yayi kasan cewa yadan ji wani abu aransa duk da san fada kawai take,
dariya fadeela tayi tana kallon reeda data dan gimtse fiska fareeda iyayen kishi , sekuwa tasake fashewa da dariya because goggo rabi tasani sarai reedace sirkarta kawai tsokanace,
Fadeela ne tayiwa goggo rabi ido alamar takalli reeda daga Hajiya har goggo rabi kallon reeda suke suna dariya, reeda ganewar datayi da ita suke wannan dariyan yasa tafice da sauri tabar parlourn , Nisha ma tabi bayanta, ganin haka yasa kamal da fadeela suka rufa musu baya suka fice,
Goggo rabi takalli Hajiya tana fadin," ni naga gaba daya kamal ya canzamin, but senaga kamar baya happy da auranda zaiyi, sekace wanda za amasa dole,
Eh to kusan dolen za ace tunda bason auran yakeba, amma ai yanasun nabeela sede yan yanzune yake kokarin sauya ra ayi, kokuma auranne baya bukata yanzu,
tokumade mainene bakin alkalami yabushe , yanzu kamar kamal inbeyi aure yanzuba se yaushe,? Hajj mama ta tambaya tana kallon goggo Rabi, gsky de kama to allah de yazaba mana abunda yafi alkhari ya kuma basu zaman lpy, amin ya Allah Hajiya tafadi,
compound din gdn suka nufa inda akayi parking motorcin, kamal ne yasa key yabude motar yashiga, nan suma suka bude suka shiga, reeda na gdn gaba su fadeela da nisha suka nufi gdn baya,
mai gadi yana ganin shigarsu mota yaje yaye musu geat suka fice, tafe suke akan hanya suna ta zuba surutu, banda kamal dake tuki yana satan kallon nisha ta glass,
Tun Nisha bata kula da abunda yakeyi harta kamashi dumu dumu yana satan kallonta, murmushi kawai take tana dan girgiza kai, batareda su reeda sunsan wainar da ake toyawaba,
karo nakarshe da yadago suka hada ido Nisha ta tsinci kanta da sake masa wani kayaceccen murmushi wanda yasa kyakykyawar dimpul dinta baiyana, wanda yasa kamal rasa nitsuwarahi,
yafara kokarin sake hanyar daya kama, kiris yarage subugu da wata motar allah yatsare kamal yayi saurin kaucewa motar,
daga nisha harsu fadeela seda abun yabasu tsoro ganin abunda kekokarin faruwa dasu, oh my God bro what happened baka ganin kakusa buguwa wancan mai motar nagama kamar hankalinka baya kana driving din,
baki ganin shiya yasake hanyarsa ya kama hanyar da batasaba kamal yafadi yana dan hade gira, gefe kuma yamaida kallonsa ga glass yana kallon Nisha datake wuli wuli da ido,
murmushi yasake lokaci daya kuma yadan hade rai yana maijin wani iri aransa, inama ace da nisha zasu kasance matsayin ma aurata ba wataba, shikade yadinga sakawa da kunce cikin zuciyarsa allah ya isu dasu wajan saloon d'in
yanayin parking wayansa tashiga kara, nabeela ya baiyana screen phone din, fiska bayabo ba fallasa ya dauka ya kara akunne hade da sallama
Magana suka danyi daga bisani tasake tunasar dashi tana jiransa, because tunjiya da sukayi waya sunyi dashi zasu hadu yau, nan yasheda mata yana zuwa daga bisani sukayi sallma yakatse wayar,
reeda yakalla da tunda yafara wayar sukayi tsit suna tsauraron abunda ake cewa awayar," bari natafi inkun kammala komai you can call me
amarya tayi kira kenan to bari mu hanzarta muje se kadawo din reeda tafadi tareda kokarin bude kofar tafita , suma su Nisha fitan sukayi yayinda kamal yaja motar shi yatafi,
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D8AO9ndEkrVIe0gZ1Q9GcP
🥀🥀 IG AJEEMAL 🥀 🥀
Story and writing by Oum AmReesh ♥️ (khaleeseart Raeys)
Free book 🥰
Page 20
Nan suka karisa shiga cikin shagon salon din, ba mutane aciki daga mata mai saloon din se ma aikatan ta guda biyu , se wata babban mata matashiya da ake yiwa wankin kai,
sallma suakayi tareda kokarin neman guri suka zauna, cike da fara'a mata mai saloon din ta tarbesu da alama ta dade da wayansu, gurin ba bakonsu bane,
gaisuwa suka shiga yida mutane gurin daga bisani su reeda suka shiga fadin suzo ayimusu gyaran gashi mai kyau da kunshi mai daukar ido, because bikin yaynsu da za'ayi,
nan matar tasheda musu basuda matsala, batareda bata lokaciba ita dakanta ta tashi tana fadin cinsu wata tazo tasuma mata,
Nisha suka tura afara mata, ahankali Nisha tamike tazo aka suma da ita, sede gaba daya han kalinta yaki kwanciya da gurin,
because tun shigowar su wajan wacce suka samu anayiwa wankin kai take ta binta da kallo duk daguwar da nisha zatayi idon matar nakanta,
duk da batasan wani irin kallo take mataba, dan itade Nisha tasan ba sanin matar tayiba balle ace ko kallon sani take mata, to allah de masani,
seda aka kammala wa matar sannan tamike tasanya mayafinta tareda ciru kudi ajakar tamikawa matar tana fadin," to Aunty sofy gashi nagode nibari nawuce still hankalinta nakan Nisha,
okay Hajiya zulai nine da godiya se anjima kigaida gd Aunty sofyn tafadi, to gd yaji daganan hajiyar tajuya tafice,
bada wani bata lokaciba aka samu daman farayiwa su fadeela, emergency abunka da kwararro basu wani jima sosai shagon salon din ba, nan da nan aka kammala komai,
gyaran kai da kunshin da aka musu yayi kyau sosai especially Nisha yanda kunshin hanunta dana kafarta sukayi mata kyau kai kace itace maryan,
bugu da kari yanda gyaran gashin nan yayi kyau yasake black dashi se wani walwali yake yana daukan eyes,
ita kanta kallon kanta take tacikin mirror tana sakin murmushi yanda gashin kanta yasake kyau dashi ya zubu har bayanta kamar wata kyakykyawar ba india,
hasali ita kanta matar shagon tayaba da kyan yarinyar dakuma sumar da Allah yamata,
haka su fareeda suka komai yayi yaji allhamdullah because suma ba bayaba wajan kyau da halittar gashi, amma de sirrin kyau irin na Nisha abun ba acewa komai say masha Allah,
Fareeda ne ta dannawa kamal kira, ganin ya dauka nan yashiga sanar fashi sun kammala, nan yace mata gashi nan zuwa, jin haka yasa suka zauna zaman jiransa,
ba a wani dade ba sega motar kamal ya iso, inda yaderesu dazu nan yayi parking yana jiran fitowar su,
jin alamar isuwarsa , yasa suka mike reeda tabude handback dinta tazaro kudi ta sallami matar, daga bisani suka mata sallama suka wuce,
Inda yayi parking suka nufa tareda shigewa motar , daganan kamal yayiwa motar key suka dau hanyar gd,
sannu hankali har allah yanufa suka iso, kamal ya danna hon mai gadi yabude masa geat yashigo yanufi compound din gdn yayi parking daga bisani suka fito, fadeela kikawomin food part dina quickly kamal yafadi tareda kokarin maida kofar motar yarufe,
to fadeela tafadi, daga bisani baki dayansu suka nufi sashin su ko takan su Hajiya basuyiba direct parlour suka nufa suka nemigu suka zauna kowa yashiga maida ajiyar zuciya,
reeda ne tamike tanufi kitchen, tana zuwa tasamu baba Barka tana tsaka da aikace aikacen da tasaba, ganin reeda yasa ta tsagaita da abunda yake tashiga fadin," yayan daddy kundawo, eh wlh yanzun nan shigowar mu reeda tafadi yayinda take tambayar abinci, ayya to bari nazu na hada muka abincin ku koh , barka tafadi, okay reeda tace tafara kokarin barin gurin,
cikin hanzari barka tace," yauwa dazu bayan fitanku telan nan yazo yakawo dinki nakarba nakai muku bedroom,
reeda bata jira barka takarisa maganar taba tajuya dasauri takoma parlour tasanar dasu fadeela dinkinsu ya iso,
daga fadeela har Nisha bayan reeda suka nufa suka shiga bedroom din, saman bed suka hangi ledan kayan, nan suka karisa shiga tareda haurawa saman bed din suka shiga dai dai da kayan ledar,
wani tsadeden Court less ne purple color mai kyan gaske da daukan ido da alama dinkin da zasu sane nawajan dinner da za ayi gobe,
gown ce duguwa kala 3 iri daya anyi masa tsadeden dinki yayi kyau sosai, haka sauran dinkuna da zasusa abikin suma sunyi kyau sosai ,
nan suka shiga shiga gwadawa suna kallon junansu, farin ciki far zuciyoyinsu, musamman Nisha da tamatsu gobe tayi taganta cikin wannan gown din,
wannan ranar sun wani cikin farinciki sun kosa gobe tayi jisuke kamar sujawuta, dan ko makaratarsu sundau hutu se angama bikin kml, because bikine dasuke ji dashi,
washe gari kankame gd ALH ABUBAKAR MODIBBO BATURE yacika da yan uwa da abokan arziki kama daga kawayan ammi matan abokan daddy, friend dinsu fadeela yan school dinsu su fauzee da sauransu , gakuma salma kawar Nisha,
yau aikin gdn yafi karfin barka ita kadae, hakan yasa tasa akara yawan ma aikatan, tundaga iman restaurant aka debo mai aikata domin girke girken gdn, c
ciye ciye da tande tande gdn a magana abun se wanda yagani,
yamma lis, ango kamal da abokansa acan gdn masaukin bakin Daddy, can suka ya dazango suma anyi musu ordern abinci iri iri da abunsha,
kamal nazaune yana kwance saman gado idonsa nakallon sama, kamar mai nazarin wani abu, jin saukan duka saman ciyarsa yasa yamike zaune yana kallon abokin nashi yana fadin," meye haka kamal yafadi yana hararo abokin nasa, oh sorry my man naga kamar baka sense dinkane but tundazu naketa magana naji shiro baka amsaniba, abokin yafadi, so what happened
dan wani guntun tsaki kamal yana fadin," nothing kawai kamal yafadi yana kokarin mikewa, yazakace bakomai bayan face din ka yanuna akwai alamar problem,
yaufa ranar nishadine indan kasan akwai wani matsa gwara ka amshi wannan karage zafi kar dan karkaje wajan dinner nan ba walwala afiskanka but today kai angone, abokin yafadi tareda mikewa yana miko masa shishan hanunsa, "
karbi kadanja nan da nan duk wata damuwar ka zai yaye kaji kwakwalwar tayi fine,
wani bazan harara ya kamal yawatso masa yana Fadi," kaide har abada bazakayi hankaliba kb abuda kamal yafadi kenan yasa kai yafice yabar dakin,
mtsww banza daga naganka cikin damuwa insun tai makonka shine kake kokarin fada min baka, bakomai kaje can damuwar ta kasheka, kb yafadi tareda bajewa saman bed yana cigaba da zukar abarsa ,
can parlourn kamal yanufa infa wasu abukan nasa suke shakatawa, zama yayi kusa da wani friend dinsa yanata faman sake wani abun tsaki,
kai kuma fa tsakin mai kake abokin ya tambaya, " wani guntun tsaki yasake saki yana fadin," kb mana suyake lalle sena koma ruwa, ranar aurena ma bai banniba"
, hmm nasani ai mai hali baya fasa hali ko ainane kakyaleshi da shirmensa yanzu katashi kaje kaahiga wanka kashirya, kasan time se gudu yake bajiranmu zaiyiba, ga aiyuka agabanmu, kasan amarya tafadi kar amusu african time,
mikewa yayi, tareda komawa bedroom din, koda komawa ya tarar da kebi na baje yana cigaba da aikin da yabarsa yanayi,
girgiza kai yayi tareda shigewa toilet yana mai jin haushin kb duk da cewa dan uwansane but haushinsa yakeji because shine ummul aba isin damuwar da yake ciki yanzu,
aban garan su, Nisha kuwa , tundaga parlour kakejin muryoyinsu da shewansu suna kyakyatawa da kawansu ,
yau Nisha kamar ba itaba ta zage se tadi ake, because gata ga salma kawarta anan ne salma ke basu labarin bikinta saura 1 month tana gaiyatarsu ,
Murna gun nisha ba a magana ganin bikin babban kawarta yakusa, dan yanda takeji dabikin salmanta ko nata iyaka kenan, yanda nisha tasake take surfa surutu, bakaramin mamaki yabawa su fadeela ba,
basuyi tsammanin haka Nisha takeda baki da surutu ba,
kawansu reeda ba girman kai sunzage se fira suke dasu nisha da salma kamar sunsansu musamman Nisha da labarin ta ya gabama isa garesu wajansu reeda, sun kuma sheda masu irin kaunar dasuke mata kamar ciki daya suka fito, kullum surutun su a school Nishan su,
se guraren magrib su Nisha suka nufi toilet yin wanka tareda alwala daya bayan daya, daga bisani masu yin sallah sukatashi sukayi haramar alwala sukayi sallah wayanda suke fashi suna zaune suna danna wayoyinsu,
bayan ko yakammal ibadarsa yakuma yazauna, ganin haka yasa reeda tamike tafice, akokarinta nafita taci karo da wacce suka kira domin tazu tamusu makeup, tareda mai tai maka mata agefenta tana rike da makeup kit a hanunta, nan tace musu sukarisa bari taje ta dawo,
jin haka yasa suka sakai suka nufi cikin bedroom din, ita kuwa reeda kitchen tanufa tayiwa barka magana kai musu abun tabawa bedroom dinsu, nan baba Barka tasheda mata yanzu kowa, daga bisani reeda tajuya takoma ciki,
koda shigowar ta tasamu har anfarayiwa fadeela, nan itama tazauna dayar tashiga mata, Nisha kama tana daga zaune saman bed suna hira da salma,
seda aka kammala wa fadeela, daga bisani Nisha tasakko aka shiga yimata, basu wani bata lokaciba abunka da kwararro nan danan aka kammala musu duka,
fadeela ne tadauki kayanta tashige toilet domin tasa, because, dakin da mutane bazai yiyu su canza kayansuba,
ganin haka yasa reeda taja hanun Nisha suka nufi wani dakin domin canza kayansu suma, kuda isarsu dakin reeda ta dauki nata kayan tayi toilet din cikin bedroom ne domin bawa Nisha daman shiryawa itama,
nan itama tashiga sari gan koda mamakinta dake kayan yashige , hakan nanufin takara gibane ko me, duk dacewa shima telan bawai ya gwada taba bane ganinta kawai yayi,
kasan cewarsa kwararre shiyasa bai nemi gwadataba, gown din yadan matseta kadan, gaba daya shef dinta ya bayyana masha Allah,
fareeda ne tafito idonta yasauka kan Nisha datayi tsaye tana kallon gown din jikinta, wow masha allah Nisha tsinkayi muryan reeda, dagowa Nisha tayi tana kallon reeda data tsaya tana kallonta,
reeda matsowa tayi tana fadin," kai my lovely kiga yanda gown dinnan ta mashi jikinki kuwa gsky tamiki kyau sosai,
murmushi nisha tayi tana Fadin," nagode kema tamiki kyau ai, murmusawa reeda tayi tareda fadin," okay muje aima dauri musamu mudanyi picture kafin motarcin dinner su suma zuwa,
ahankali Nisha take daga kafa, because yanda takejin kayan ya matseta dan haka setakeji kamar tsirara take, dan gaba daya a tsarge take ita damuwartama karya barke mata cikin mutane aji kunya,
tundaga shigowar su nisha yan dakin suketa wow wow nikuwa nace,( baku suma wowba sema an kammala kwaliyar,)
nan akashiga rangada musu dauri, kowacce da kallan daurinta, sunfito sunyi kyau dasu kai kace yan ukune masha allah, gaba daya sae suka zama abun kallo, gani yanda suka fito sukayi kyau dasu kamar wasu taurari,
kuwa phone dinsa yadauka yashiga daukar su a photo, suna cikin daukar hutun ammi tashigo tana sanye cikin kayaceccen shirnta mai kyau da ban shaawa sewani walwali take uwar angoba ,
masha allah abinda ammi tafadi kenan sanda idonta yasauka kan kyawawan taurarin yayanta 3 , ganinta da su fadeela sukayi yasa sukayi kanta suna daga salfi,
seda tajira sungama daukan photon nasu daga bisani ammi taja hanun Nisha suna kokarin barin dakin, ganin haka yasa su reeda fadin ," ammi ina kuma zakuje muna pictures , babu yanzun nan zata dawo,
Ammi na fadin haka taja nisha suka fita, upstairs ammi tanufa da Nisha, direct parlourn Daddy suka nufa yanda manyan bakinta suke,
nan tashiga gabatar musu baby girl dinda take riko wacce ta basu labarin marainiyace, nan Nisha tashiga gaishesu suka amsa cikin fara'a da sakin fiska, tareda mata fatan alkhari,
daga nan ammi tanufi bedroom dinta da Nisha, suna shiga tazaunar da Nisha saman sofa, tana fadin,"bari nazo, juya ammi tayi tanufi bedside tabude tareda jawo wani kwalin kwaya, tanufo Nisha dashi,
hanun Nisha taja tareda daura matar kwalin wayar iphone xr zaro ido Nisha tayi tana kallon kwalin wayar da ammi ta ajiye mata, daga bisani tamaida kallonta ga ammi, murmushi ammi tayi tana fadin,"
Kyautata agareki, na dade insu nabaki but nayi tunanin bari sekin fara zuwa school zaifi miki amfani, to, yau naga ranace daya dace nabaki kema kidanyi walwala dashi, kuma naga kamar phone dinki ta dan tsufa bazakiyi wani walwala da ita sosaeba,
tsit tayi ganin Nisha ta sunkuya tana kokarin kuka, " oh meyena kukan kuma kanasun bata kwalliyarki, ammi tafadi tana tana tallafo ta tareda dan babuga bayanta alamar lallashi,
ammi nagode allah ubangiji yasaka miki da mafificin alkhari, narasa wani irin godiya zan miki, Nisha tafadi tana sharce hawaye,
Nibanason wata godiya, kukan nakeso kibari, share hawayenta fiskarta tayi tana bin kwalin wayar da kallo, tana mai jin dadi,
daga nan ammi taja janunta suka fito, daga nan suka rabu Nisha ammi ta koma parlourn Daddy Nisha tanufi bedroom dinsu,
tana zuwa tashiga nunawa wasu salma da su fadeela kyautan waya da ammi tamata suka tayata murna, duk dasu fadeela sunsan da zancen wayan su fada mata bane kwai sede taji surprised,
wuraren 8:30 motarcin angwaye suka shiga zarya cikin gdnsu kamal, manyan motoci na yayan manya, daga farkon layi har kanshan layi,
dan haka masu haramar tafiya suka suma turoron shiga mota, already dangin amarya sunacan babban Hall din da aka kama dan gudanar da invent
daga saman bene ta window su reeda suka lura da zuwan motocin dan haka , suka fara shirye shiryen fita, nan kowa dake dakin yamike wasu suka fara fita, yarge daga Nisha se salma dasu fadeela, da fauzee, suma kokarin fitan suke
nan fareeda ta dauki handbags tazaro kudi tamikawa me makeup, taimusu godiya suka tafi, suma fitowa sukayi , tareda neman motar suna kokarin, shiga,
Su biyar ne kuma mutu hudene sukeda damar shiga motar because baza biyune agaba, mai driving se nagefensa, fauzee ne tafara shiga daga bisani reeda tashige se fadeela tabi bayanta,
Nisha da salma tsayawa sukayi suna kallon juna, ganin haka Nisha ta kutsa salma ciki tana fadin," kishiga nibari na shiga nabayanku, tana fadin haka tamayar musu dakofar tarufe,
su reeda sam basu ji dadiba suso sukasance atare, jin sunshiga mai driving din motar yayiwa motar key , nan motocinda akwai mutane aciki suka suma tafi, ganin haka Nisha nufi wata rantsatsiya mota da nufin shiga,
budewa tayi mutum ukune ciki, hartasa kafa daniyar shiga taji anjawota da karfi, har seda tafara kokarin nemana faduwa ,
daker Nisha ta daidaita tsayuwarta tana binta da kallo, bakowa bane da wannan aikin face raheela, tasha uban kwalliya yuwa aljana tana ta wani huci da kumburi
Khaleeseart Raeys ✍️
08105565439Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D8AO9ndEkrVIe0gZ1Q9GcP
🥀🥀 IG AJEEMAL 🥀🥀
Story and writing by Oum AmReesh ♥️
Free book 🥰
Page 21_22
gyara tsayuwa Nisha tayi tana cigaba da kallon raheela daga ita har zagada zagadan ham shakan matan guda biyu dake bayanta, "
ina kike kokarin shiga heelah tafadi tana hararo Nisha, banganeba Nisha tafadi, dama bazaki ganeba, ina kikabar aheel kike kokarin tafiya gayyar sudi, ban ganshiba nisha tafadi atakaice zuciyar ta na mata wani irin suya,
to kisani ba inda zaki kije kinemu yaron nan because nasan ba inda zai shiga agdn nan se gurinki dan haka kikama hanya kiwuce kinemu munshi,
Nisha tariga tagane muguntan datakeson mata sutake kartaje wurin dinner nan, shiyasa take kokarin kawo wadan nan zantukan,
but ita kuma tasa ranta azuwa wajan, dan haka cikin bacin rai Nisha tace, ," ni ban ganshiba kuma ba gurina yazoba, kije kine mesa can inda yake, Nisha tafadi tareda kokarin matsawa tashige cikin motar,
cikin zafin nama da takaicin kalaman nisha agareta yasa raheela tafisgo Nisha tareda hankata baya dakarfi,
nan da nan Nisha tarintsa ido tareda sakin wani ihu tana neman faduwa, jin tafada jikin mutum yasa tayi saurin gwalo ido tasauke kan goggo rabi da take tallafe da ita,
goggo rabi tsaida Nisha tayi ta tsaya dakatarta cak, daga bisani tayi kan raheela cikin bacin rai, tas kakeji tadauketa da mari seda cingan dinda heelah keci yafado kasa,
," kaji min mutumiyar banza, yarinyar wofi, ni anya hankalinki daya kuwa, wannan wace irin bakar mugunta ne, kina kokarin ilata yarinya, goggo rabi tafadi cikin fada da bacin rai,
goggo rabi juyawa tayi takalli Nisha daketa ta faman rau rau da ido tana shirin kuka,
matsawa goggo rabi tayi kusa da Nisha tareda janyuta jiki tana fadin," sorry karkiyi kuka kinjiko, tafadi tareda kokarin kutsata cikin motar daza sushiga, daga bisani goggo rabi ma tashige,
nan da nan motacin biki suka suma yin reverse suna fita, daga compound din gdn because kowa yan biki angama shiga,
Lallai fa haka fiskar ki tayi cheesepiet haka gdn nan da kowa zai iya bugu, friend din heelah tafadi tana tabe baki, yayinda take sake kallon heelah tayi tsaye tana rike da kumatun ta, tana furzar da wani irin huci,
tsabar takaici raheela takasa magana because irin wula kancin da goggo rabi tai mata sa hanu da tayi ta mareta agaban jiga jigan kawayenta,
Wani dugun kwafa tayi tareda ratsasu fuuuu tayi part dinta zuciyar ta na wani irin suya, ganin haka yasa suma kawan nata suka rufa mata baya suka bita,
dinner da heelah bata samu zuwansa ba kenan,
guri yayi guri taro yayi taro yan uwa da abokan arziki maza damata manya da yara ancika tam cikin babban Hall din dinda aka ta nada domin su,
Isuwarsu goggo rabi da Nisha kenan, nan sukashiga cikin hall din da sauran tawagar dasuke taredasu,
Nisha tunda sukashiga se wul wul ga ido take tana kallon gurin irin kudinda aka narkawa wajan da kuma tsari da kyau da yayi,
Ahankali takebin wajan da kallo, idantane yasauka akan amarya nabilah da angonta kamal cikin kyakykyawar yanayi tareda shiri mai daukan ido da hankali,
jitayi gaba daya wani abu yataba mata zuciya duk da itama batasan meyeba,
Jin anrungumuta yasa mind dinta yadawo jikinta, aheel ne rungume da ita yana washe mata baki, cikin murna da daukin ganinshi yasa Nisha tadago shi tarun guneshi hade da masa wani cool kiss akuncinsa,
duk da tayi mamakin ganinshi anan saka makon mummyn da take nemansa, tambayar shi tashiga yi shida watso nan, nan yasheda masa da grandma dinsa wato ammi, batakaiga sake maganba,
Fareeda tazo taja janunta suka nufi inda suke zaune seat reeda tanunawa nisha nan tazauna tareda daura aheel acinyarta, gefe dasu kawayan nabilah yan rawar kai suna opposite da abokan kamal
goggo rabi dama tuni tashiga tawagar ammi tasamu guri tazauna,
nanfa guri ya hargitse yakacame da nishadi
daga abokan ango kama da amarya su fadeela anyi rawa kamar ba gobe, uwar amarya da ammin kamal se barin dollars sukewa yayansu,
banda Nisha da salma dake zune suna kallo dama su ba gwanayen rawa bane,
anci ansha anyi rawa yanda yakamata anyi photo sosai, ango da amaryansa sun yanka cake sunbaiwa junansu,
gefe guda kuwa wata matashiyar matace ke zaune daga daya daga cikin kujeran da su ammi ke zaune tana ta kokarin dealing wani nurmber amma shiru ba adaga ba,
ba kowa bace face mahaifiyar raheela Hajiya jumana, tana ta dealing numbern heelah yanata ringing but bata daukaba, kuma tayi tsamanin ganita gurin dinner, but shiru haryanzu babu alamar zuwanta,
wani dan guntun tsaki taja tareda daukan handbag dinta tafice, but ba wanda yalura da fitarta, because ba wanda hakalin sa ke gareta yana wajan bidirin da ake,
tana fita motarta tashige tareda yimata key tadau hanyar gdnsu reeda, sannu ahankali take tafiya harta karisu gdn a gaggauce tayiwa hon, mai gadi yazo yabude mata geat tashigo tareda yin parking compound din gdn tafito tayi part din raheela cikin hanzari,
shiru parlourn yake se heelah data hango tana kwanta saman kafe kamar wata macecciya, cikin rudu da hanzari takarisa gun raheela tana kiran sunanta,
muryan ummanta datajine yasa raheela ta mike daga kwanciyar da tayi still hanunta narike da kuncinta, nan da nan raheela ta fashe da kuka tareda fadawa saman cinyar ummanta, "
ke lafiyanki kuwa mai yasameki, hjy jumana ta tambaya, tana sake kallon ya daya tilonta, ganin ta rike da kumatun ta ,
ganin haka yasa ta matsar da hand din heelah daga kuncita, ganin yatsu biyar kwance kumatun ya daya tilonta yasa ta waro ido tana fadin," kutumar uba , waya mike wannan aika aikar haka, fadamin wani shegenne,
cikin sheshshekar kuka heelah tashiga bata labarin abunda yafaru tsakanita da nisha dakuma marin da goggo rabi tai mata agaban friend dinta, karya da gaskya duk ta hada tafadi,
wani zazzafan huci Hajiya jumana ta furzar tana fadin," lallai kuwa dama nasan arina yanda naga suke wani haba haba da yarinyar, to sun tabo tsuliyar dodo yanzu akan wancen sha sha shan yarinyar har rabi ta iya daukan hanu tamareki?
wato bare yafi dan gd kenan, lallai zasu san sunshigo gunata musamman yarinyar nan , tunda ammi tazu tana wani introducing dinta agurinmu, nidama tunda naga yarinyar bai ta kwanta min arai bane, kuma nasan bahaka banza tashigo gdn nan ba, harta samu karbuwa haka,
gashi ta dalilinta aka mari gudan jinina, to kuni da na haifeki yatsama ban taba gwada mikiba balle taba lafiyar jikinki, hmmm ba komai tashi kizauna, umma tafadi,
seda suka zauna akujera, Hajiya jumana takalli heelah cikin tausayawa da takaici na marin ta da goggo rabi tayi, janyuta tayi jikinta tana fadin," kiyi hakuri kikyalesu kuma kibarni dasu,
daga zuwar yarinya ana kokarin amayarmin da ya kamar ganga, nan gaba kuma bansan me zai faruba matsawar wannan yarinyar tana gdn,
Ina mijin naki yake umma ta tambaya tana duban heelah, tashi tayi daga kwanciyar da tayi jikin umma tana fadin,"baya nan yayi tafiya yau kwansa biyu,
Yaushe kenan zai dawo umma tasake tabaya, bansani because bai sanar da niba nikuma ban nemisaniba tunda bai sanar daniba, heelah tafadi tana dan tura baki,
hmm wato de haryanzu yana nan da zafin kanshi da miskilanci, because bakida mahimmanci kinsan tafiyarshi da dawowansa ne komai? umma tafadi,
nima bansaniba heelah tafadi atakaice, hmm yayi kyau wato kekuma ga shasha sha kizauna kina basa jiran daki da yaronsa koh,
shiga agogo sarkin aiki ko bikin dan wansama baya gabasa, hmm zamu hadune, Hajiya jumana tafadi tareda mikewa tana fadin,"
yanzude kitashi ki kimtsa nizan tafi zamuyi waya, daga nan tayi mata sallama tafita, tana fita tashiga motar ta taimata key, maigadi yabude mata tasa kai tafice,
ban garan yan dinner kuwa guraren karfe 10:30 aka suma watsewa masu tafiya suka suma tafiya gdajensu, amarya da kawaye da yan uwa tuni anwuce dasu gd jensu,
haka bangaren kamal yan uwa da abokan arziki kowa hankali ya tattara ya kuma gd,
salma da fauzee da suran kawayan su fadeela tuni sunyi gaba because dama su basu wani dade wajanba suka tafi
su fadeela motar kamal suka shiga , se motar dake tafe bayansu abokinsa md yana jansu ammi ,
sanu ahankali suke tafiya har allah yanufa suka iso, mai gadi yabude musu geat sukashigo tareda nufan compound din gdn sukayi parking,
nan kowa yafo yanufi sashensu, because kowa yadibo gaji da bacci aidonshi,
Kamal tsayawa yayi gun md seda sukayi sallama tareda yiwa md godiya har seda yaga fitanshi daga bisani shima yanufi nashi ban garan,
Su Nisha suna shiga seda sukayi sallar isha dinda basuyiba daga bisani kowa yayi shiri cikin night dress daga bisani suka kwanta,
washe gari Friday da safe akashiga yin walima tareda saukan Allah Qur'ani mai girma, gd yasake cika da yan uwa da abokan arziki,
bayan sakkowa daga sallahn jumma'a cikin masallaci aka daura auran KAMAL ABUBAKAR MUDIBBO BATURE, tareda amaryarsa NABILAH MUHMMAD MODIBBO BATURE yan uwa da abokan arziki kowa ya samu halarta masallaci da aka daura auran ,
Da misalin karfe 4:30 motan angwaye suka shiga zarya gdnsu nabilah, domin daukota akaita gdnta na sunna,
goggo rabi da kanta tashiga ta dauko, tanata kukan rabuwa da mom dinta, mom nayi itama nabilah nayi haka suka rabu abun ba Dadi, gwanin ban tausayi, nan aka kutsata cikin mota aka dauki hayar gdnsu kamal,
anan ban garan kamal aka sauketa tareda wasu kawayanta, masu dan debe mata kewa, duk da gdn yakasan ce ba bakonta bane but yau setaji gdn yamata daban,
seta kasance tamkar bakowa, guraren magarib kawayeda suke tareda ita suka shiga yimata sallama suna watsewa daya bayan daya, gashi parlourn ba kowa ita dayanta,
aban garan cikin gd kuwa nan ma gd yayi shiru duk yan barka kowa ya watse ya kama gd,
guraren karfe 8 su reeda zaune saman bed sunjeru kamar kifi gwan gwani suna latsa wayarsu, Nisha nadaga kwance tana kallon picture dinsu da fadeela ta tura mata cikin new phone dinta,
goggo rabi ce tayi sallama tashigo tasamesu cikin yanayida sukeciki, jin mutsin shigowar goggo Rabi yasa suka dakata da danne danne dasuke awayoyinsu, nisha kuwa ta tashi daga kwanciyar da take tazauna,
Goggo rabi, seda takallesu daya bayan daya daga bisani tasuma fadin, " sako nazu nafada muku yayanku kamal yace kunbar masa amarya ita kade, dan haka kubar duk abunda kuke kuje kutayata fira,
Khaleeseart Raeys ✍️
08105565439🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by Oum AmReesh ♥️ ( khaleeseart Raeys ✍️)
Free book 🥰
Page 23, nabilah amarya tana can katafaren parlourn mijinta jikinta sanye cikin kayaceccen lulubi irin na amare, sezuba kamshi take ,
Jin anbudu kofa hakan ya tabbatar mata da angonta kamal ne ya iso, dan haka cikin natsuwa tadago tana kallon kofar domin ganin shigowar sa,
ga mamakinta setaga ashe su fadeela ne suka shigo daya nabin daya, bata kaiga karisa ganin shigowar su ba , nabilah tadukar da kai kasa tana sakin wani goron numfashi,
Amarya kina nan ke kadanki reeda tafadi tana tambayar nabilah yayinda take kokarin zama kusa da ita,
Gyada kai nabilah tayi tana murmushi batareda ta dago takallesu ba,har
friends din naki suntafi? nadauka zasu tsaya se ango yazo ae, fadeela tafadi tana yar dariya,
wannan karon nabilah dagowa tayi danufin magana , karaf idonta yasauka kan Nisha dake zaune takurawa guri guda tana kallonsu,
,
Oh my God nabilah tafadi yayinda tamike tsaye tana kallon Nisha, itama Nisha mikewa tayi wacce duk taji jikinta yasuma bari, se yanzu idonta yayi tuzali dana nabilah,
saka makon ko wajan dinner bawai ta ganetabane because irin ado da bride makeup datasha ba lallai tagane ainihin face din taba,
haka itama nabilah bata kula da Nisha wajan dinner ba because attention dinta baikai wajan Nisha ba, "
meyakawo wannan stupid girl dinnan cikin gdn nan, ? nabilah tafadi tana kallon Nisha datayi tsaye hawaye na shirin wanke mata face,
" Fareeda da fadeela sake baki sukayi suna kallon ikon Allah, but sun gagara cewa komai sun koma kasa gane meke shirin faruwa, ahankali nabilah take matsawa kusa da Nisha tana kallon ta, duk da nisha tadan canza but hakan bazaisa nabilah tamance da face din yarinyar da tagansu tareda kamal gdn masaukin uncle dintaba,
yarinyar da kamal harya iya daukan hanu ya wanke ta damari saboda tafita mahimmanci wani irin azabebben kishin yaturnike nabilah , because Allah yagani yanda take bala in son kamal da kuma kishinsa, tun ranar da idonta yagane mata Nisha da kamal sun kebanta hankalinta yakasa kwanciya takuma kasa mancewa da ranar,
Wani kukan kura nabilah tayi tareda yin hakan Nisha, Nisha naganin haka yasa tajuya da gudu tana kokarin fita daga parlourn, aiko kafin tayi wani yunkuri nabilah ta janyo hand dinta takai hanu danufin marin face din Nisha, carab taji anrike hand dinta,
Kallon kamal tayi dake rike da hanunta yashiga tsakanisu da Nisha datayi kasa dakai tana sharce hawaye, gefensa nadauke da md tareda muhaiseen dayazo tun farar safin da aka daura auran kamal,
ganin yadan kamal ya rike hanunta gam yana binta da kallon cikin wata siga yasa nabilah tashiga kiciniyar kwace hand dinta danufi auwatar da abunda tayi niya because idonta yarufe,
kamal kuwa yanda yaga nabilah na kokarin kaukawa dashi yasa cikin bacin rai yatureta gefe wanda hakan yasa tashiga tangal tagal tana neman faduwa, cikin hanzari kamal yarikota tareda daidaita mata tsayowa yana fadin," I'm sorry ba danufi nayiba, baikai ga karisa maganar ba nabilah tadukar dashi, tana fadin," ba hakurinka nakeda bukatan jiba , seda ta zame jikinta daga rikon dayayi mata daga bisani taja gefe guda tatsaya tana kallon Nisha tana fadin,"
meye dalilin zuwan yarinyar nan gdn nan, duk haduwar dakukeyi awaje ahakan bai wadatar ba seta biyoka har inda kake tarabeka meye hadinka da ita da har take bibiyar rayuwarka haka, nabilah tafadi cikin kunar zuci, parlourn ne yadau shiro kamar bakowa cikinsa, su fadeela mamaki yagama cika kwakwalwarsu haka muhaiseen yakalli Nisha yakali nabilah gefe kuwa ya maida kallonsa ga kamal da nabeela ta tsaresa da ido, shimade yakasa gane inda zantukansu ya dosa, shide yasan sanadin zaman yarinyar agdn kuma ya dade dajin labarin ta gurin reeda dakuma goggo rabi wato mahaifiyar sa, md kuwa kai sunkuye because already dama yasan komai ,
kamal jan hanun nabilah yayi suka nufi sofa, zaunar da ita yayi shima kuma zaman yayi, kuma yiwa abokan tafiyarshi md da muhaiseen tayin zama, yakuma kumarci su fadeela dasu zauna suma, banda Nisha datake tsaye kai sunkuye tana ta jan hanci," kizo kizauna kamal yafadi yana kallon Nisha datayi tsaye abun tausayi, gagara daga kafarta tayi shiyasa takasa matsawa tazauna, se reeda ne tamike daga zamar da tayi tanufi Nisha tareda rukota suka taho tazaunar da Nisha daga bisani itama tazauna, nabilah se bin Nisha take da wani mugun kallo, haka kamal shima Nishan yake kallo face dinta yayi jawur gwanin ban tausayi , daga bisani yamaida kallonsa ga nabilah da ta tsareshi da eyes, ahankali yasuma magana da cewa,
niba abunda yake tsakani na da ita but bun dade da sanin juna hasalima akwai abubuwan da suka faru abaya wanda bawanda yasanda faruwanso,
TUNABAYA******____________________________*****
Wata kyakykyawar motar hadaddiya tsa daddiya write color takunna kai a million tana tasheka gudu bisa hanyar kan wata layi cikin wata anguwa, kai kace wanda yake tukin ba hankalisa yakeba,
Yammane lis gari yarufa yanayin gari na damuna, yayafine take diga dis dis, saka makon tsagaitawa da ruwa yayi, Matasan yan matane guda biyu dake tafe suna tafiya suna fira , jikinsu sanye da inform hijab yarufe musu jiki kirib se dan sawayansu da ake hangowa cikin black socks, da alamar antashesu daga mkrnt suna kan hanyarsu takomawa gd,
duk da dan yayyafi dake hakan bai hanasu tafiya slowly yanda sukeba, da alama suna cikin nishadi a cikin firan dasuke,
jin wani mahaukacin hon yasasu firgici yasa sukayi saurin watsewa junasu kowa yafara kokarin yin takansa, cikin tsurita da rudu, daya tayi hanyar motar da take kokarin bi, jikake gauu, motar data tahu ta bugeta, duk da bawani bugeta yayi sosaeba because yalura da ita but yayi kokarin taka Burkin allah yariga da ya iko da tsautsayi yadan bugeta,
dasauri wacce suke tafiya tare tayi kan kawarta dake kwance tana duka salati tana kiran sunan ummynta , da Nisha tana fadin tazu ta taimaka mata takaita gurin ummynta, wayyo namutuna, itama Nisha duka sallallami tashigayi , tana kiran sunan, salma
nanfa motar tafara yin reverse danufin cigaba da tafiya tabar gurin, oh my God meka aikata haka, kuma kake kokarin tafiya kamar baka san kayiba? dayan yafadi yana kallon mai driving din, " mekuwa nayi baka ganin ita tashigo gabana bawani bugeta nayibafa kawai tsoritace tayi tafadi, mai driving din yabashi amsa, yana kokarin cigaba da tafiya, cikin hazari dayan matashin ya taka Burkin motar tareda zare key yabude motar yafito, daga bisani yazagayo ya bude gdn gaba yafito da abokin tafiyar tasa, yatusa keyarsa zuwa ga gurinda yan yan matan ke tsugune Nisha na tallafe da salma, guri yayi tsit se muryan salma dakakeji tana ta duka salati ita dakko daga farko Nisha ta karshe mata karshe,
seda suka kariso yadan duka kusa dasu yana musu sorry, but daga Nisha har salma ba wanda ya dago yakalleshi balle susan abunda yake Fadi,
ganin basu amsashiba yasa yamike yana kallon, dayan yana fadin," kb yanzun kaga abunda kayi fa taji ciyo kanta yafashe ga head dinta se bloodshed yake yanzu se muyi hanzarin zuwa mukaita hospital abata taimako , "lallai fa gsky banida time kasan sauri muke yaushe zamu tsaya biye wadan nan, kadubafa magana ake but sunyi shiru sunajin mutane, wani tsaki kb yaja tareda ciru kudi cikin pocket dinsa ko irgawa bai yiba ya watsawa su Nisha yana fadin," kuje hospital aimata magani, rashin hankali da nutsuwa darashi kula yajawo muku,... tas kamar walkiya yaji andaukesa da mari , cikin hanzari ya dafe gefen fiskar sa yana kallon Nisha datayi tsaye agabansa cikin fusata da bacin rai,"
wato shi talaka abun wulakancine dacin mutunci koh? kabuge yar mutane baka iya cemata sannuba kana kokarin zaginta, rashin hankali da rashin kula yawuce wanda kayi yanzu, karike tsiyarka allah zai saka mana, nisha tafadi tareda watsa masa kudin a face dinsa, tanufi inda salma take akwance, tafara kokarin tallafo ta,
Dukansu matasan tsayawa sukayi suna kallon karfin hali irin na yarinyar da harta iya daukan hanu ta daurashi face din namiji irin kb, tab dayan harde hanu yayi bisa karjinsa yakalli Nisha yakalli kb daya sake baki yana rike da kuncinsa, azafafe kb yayi kan Nisha dayan yarikoshi yana bashi hakuri tareda tausansa,"
Please kamal kyaleni nakoyawa yarinyar nan hankali naga kamar hankali bai wadaci kwakwal wartaba , bata san waye niba dan haka kabarni nafada mata,
daga cikin motar dasu kamal suka paka wata matashiyar budurwa dirarriya cikin wata irin shiga, sanye take cikin t shirt skintight ko ina ya dame , fitowa tayi tatsaya daga jikin motar tana kallon su kb da kamal keta faman rirrikeshi, tabe baki tayi tareda zaro phone dinta tayi dealing numbern kb,
bawani ratane tsakanisu suba baifi kayi taku 5 zuwa shida ba ka isa garesu, but baza ta iya karisawaba hakan yasa takirashi, kb najin wayarshi tashiga kara yasa, cikin fusata yaciro yaduba yaga mai kiransa, ganin baby nice dinsace takira yasa yamaida kallonsa ga wajan da motarsu yake yahangota jin gine tana kallonsu, wani kwafa yasake yana kallon Nisha da dake tallafe da salma har sun mike suna shirin barin gurin, lips dinsa yakuma ciza daga bisani ya kwace hand disa daga na kamal yawuce shi, yanufi motarsu, shima kamal din bayansa,
suna zuwa gurin motar kamal yanufi seat yazauna haka kb itama yarinyar bude motar tayi tashiga suka ta da motar suka wuce,
ahankali Nisha take takawa da salma because kafarta yasamu rauni shima , Nisha jitake kamar ta daga salma domin tarage mata ra dadin datakeji, amma batada wannan karfin da ta taimaka, basu wani dade atafiyarba suka iso gdnsu salma, duk dama sun kusa isowa gdn wannan tsautsayin ya afka dasu,
tundaga kofar gd kanin salma ya hangi yar uwarshi salma nisha narike da ita, hakan yasa yawatsa aguje cikin gd domin afadin abunda yagani, Nisha nashiga da salma cikin tsakar gdn ta ta tarar dasu ummyn salma da babanta dayi alwala yana kokarin fita masallaci because magarib ya gabato, da kuma faruk kaninta suna tsaye suna jiran shigowasu,
ummyn Salma tana ganin Nisha tareda yarta anrokota magashiyan yasa tayiyo gunsu dasauri tana tambayar abunda ke faruwa, ba da wani bata lokaciba nisha tashiga tsaiyanu musu abunda yafaru, " oh allah kai amma wayan nan yaran basu kyautawa kansuba,wani irin rashin imani ne haka ummyn salma tafadi yayinda take kokarin tallafo salma da jiki yayi tsami, hmm Allah kyauta yakuma kara tsarewa, kushiga da ita bari naje nataho da mai adaidaita se mukaita hospital, baban salman yafadi, tareda sakai yafice faruk ma yarufa masa baya, har dakin ummyn salma Nisha ta taimaka suka kaita suka tsaunar da ita suna mata sannu, daga bisani Nisha tai musu salma zata koma gd tareda fatan samun sauki, takuma sheda musu gobe in allah ya yarda zata dawo, haka sukayi sallama Nisha tafice tanufi haryar gdnsu,
kasan cewa gdnsu salma da Nisha bawani rata sosai nan da nan ta iso, cikin dan ma dai daicin parlourn su gwanin shaawa Nisha ta tar da umma na tsaye takasa tsaune takasa tsaye, umma nagani Nisha tashigo da sallama taja wani dugun ajiyar zuciya, tareda tin karo Nisha tana tambayar ba asin rashin da wowar nisha da wuri because bata saba hakanba shiyasa hankalin umman nata ya tashi, nan fa nisha tashiga labarta mata rashin kyautawa da su kb sukayi musu dakuma raunin da salma tasamu, harta kaisu ga bata lokaci haka, tabbas itama umma bataji dadiba takuma nuna damuwarta da halinda da salma take ciki, takuma yi allah yakyauta yakuma kara tsare nagaba,
awannan ranar Nisha ta kwanta da bakinciki da takaicin wadan nan samarin especially wannan mai zubin mashayan wanda taji dayan yakira da kb daka ganshi kasan kwa kwalwarshi akwai gyara acikinta, talk din shima wata iri babu dadin ji bugu da kari ba furci mai Dadi, amma de ko banza rada din datakeji yaragu inta tuna da marin data masa koba komai tasan tabar masa wani gibi azuciyarsa da zai dingajin haushi da takaici,
washe gari Sunday kamar yanda Nisha tayiwa salma alkawarin zata dawo haka kuwa akayi, guraren karfe 10, tana gama breakfast tayiwa umma sallama danufin zuwa dubo kawarta salma, nan umma tasheda mata tagaishesu itama inshallah allahu tana tafe domin zuwa ta dubata, in allah yasa tasamu saukin jikinta itama because ita dinma bai tacika lapia bane,
to Nisha tace mata ga nan tafice tanufi hanyar gdnsu salma,
tundaga nisa Nisha ta hango wata jibgegiyar mota red color afake kofar gdnsu salma cikin matsuwa ta karisa shiga ciki hade da sallama tana dan wul wul ga ido , daga tsakar gdn nisha tayi turos tana kallonsu, anshin fida taburma , salma nazaune jikinta sanye da hijab tajin gina bayanta da filo leg and head anyi dressing dinsu, gefe kuwa matasan samari guda biyu , saurayin salma wato muhammad bello wato mb se gefensa saurayin jiya kamal , suna zaune dukansu sun tsura mata ido suna kallonta , itama kallonsu take tana kokarin karisawa ahankali
Khaleeseart Raeys ✍️
08105565439🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by Oum AmReesh ♥️ (khaleeseart Raeys ✍️)
Free book 🥰 ga masoyana ina alfahari daku ina kuma godiya da fatan alkhari much kauna nagode sosae 🤝
Page 24
Seda takarisa kusa da salma, daga bisani tashiga gaishe dasu mb kasa kasa, seda suka amsa mata cike da washe baki, sannan takalli kawarta salma wacce itama itan take kallo tana murmushi,
Nisha tambayar salma tayi yajiki, nan salma tace jiki alhmdllh, daga haka Nisha tasuma kokarin mikewa, "ina kuma zakije salma tafadi tana kallon Nisha, zanje mugaisa da ummy ne, to ae bata nan tashiga makota salma tafadi tana murmushi dan tagane bawai gaisuwar ummynne yadametaba ganin mb tareda kamal yasa tafake da wani batun gaisuwa, dan tsuke baki Nisha tayi still tana tsaye bata zaunaba,"
kode zuwana tareda abokinane zai takuraki mb yafadi yana kallon Nisha yana yar dariya, sorry yanxu zamutafi mubaki space ma karmu takuraki, munzo tareda abokinane saboda mubaku hakuri bisa a
kuskure da yafaru jiya ,"
kuskure ko sakaci da rashin kula,? Nisha tafadi yayinda take kokarin neman guri tazauna, munsani shiyasa mukazo mubada hakuri akuma gafar cemu, kinga abokina bashi bane da laifi bro dinsa ne but karkiga yanda ya damu se munzo tare yabaku hakuri gameda abunda dan uwansa yayi, "
aigwara dakukazo kudin don da wancan zauceccen kukazo bazamuma saurare kuba, kamal duk yana jin abokinsa tareda yarinyar but baitaba ganin yarinyar mai tsiwar tsiya irin yarinyar nan ba, dagowa yayi yana kallon yarinyar yayinda suke magana da mb, Allah yama ta kyau ta hada komai allah yabata sede masi faffiyace,
amma de shi yasan tun haduwarsu jiya yarinyar tasuma burgesa kasancewarta mara tsuro komai kai tsaye take ba boye boye bare shakka, "muna mai neman afuwa nida dan uwana akan abunda yafaru munsan munyi kuskure da sakaci da rashin kula kamar yadda kikace, munyi laifi amana afuwa kamal ya tsinci kansa da bada hakuri tareda hade hand dinsa guri guda asha gwabe yana kallon Nisha,
daga mb harsu Nisha kallonsa sukayi yanda yawani marai raice fiska, kasancewan kamal mai barkwanci ne wani sa'in salma da mb fashewa sukayi da dariya mb yashiga zungurin kan kamal yana fadin,"
kai meye hakan? shiru kamal yayi yana kallon Nisha yana kuma sake hada hand dinsa yana fadin," please yana wani sunnar da kai kasa, basu salma bama hatta ita Nisha seda takusa barkewa da dariya but seta matse ta dan turo baki tana fadin," nifa ba ni akayiwa laifi ba kawata ce intayafe to nima nayafe inkuma bata lamunceba to nima fa... bata karisa maganar ba taji salma nafadin," nikam nayafe allah ya kiyaye nagaba, sake baki Nisha tayi tana fadin," da wuri haka kamar wacce kike jira , "
ato mai zata jira kinsanmu bama rike abu, daga anyi muke yafewa mb yafadi yana kallon salma koya kikace, gyada kai salma tayi tana kallon Nisha tana murmushi,
dariya dukansu sukayi daganan fa hira ta barke tsaka ninsu sunyi hira sosae har guraren azahar daga bisani su kamal suka mike tareda ajiye kayan dubiya dasukazo dashi sukai wasu Nisha sallama suka wuce,
bayan tafiyar su Nisha kamar jira take tashiga tambayar salma," ke ina kuma mb yasamu wannan mutumin aina yasanshi,?
friends ne tun american tare sukayi karatu still kuma yanzuma tare suke abokaine sosai mb yafada min muna cikin hirannema kika shigo salma tafadi,
dan jinjina kai Nisha tayi dan bawai ta gamsu bane, sotake takuma wani tambayar but seta fasa ta ajiye se wani ranar idan time yabata dama,
mikewa Nisha tayi tana fadin," bari naje gd nabar umma ita kadae gakuma aiyuka da nabari, zaki tafi baki taba kayan makulashen da aka kawo ba, gashi ummyn bata dawoba, waifa sbd bello tagudu makota salma tafadi tana tabe baki,"
dariya Nisha tayi tana fadin," ba damuwa kigai sheta intazo, oh na mance umma tace agaisheki da jiki zatazo ta dubaki intaji sauki dan bata jin dadi jikinta sosae, "
Allah sarki umma har yanzu jikinne allahde ya bata lapia salma tafadi, ameen bari naje se wani lokacin Nisha tafadi tareda yiwa salma sallama tafice,
Nisha na komawa gd ta tsinci umma bisa sallaya ta kishingida da alamun bacci ya suma daukarta, dan haka batabi takantaba bare ta takura mata, bedroom dinsu tashige tanufi toilet tayi alwala tafito tayi sallah tanufo tsakar gdn tashiga daura musu sanwan rana dan tasan umma bata dauraba because lapia bai wadaci jikinta ba, gashi abubuwan cefanen nasu da kudin dake hanunsu na dab da karewa,
gashi kuma haryanzu abba bai lekosuba balle yasan halinda suke ciki,ga rashin lapiyan umma ya tafi ya dawo, gaba daya abun dunya ya gama isarsu,
Aban garan kamal kuwa tunda suka bar gurinsu Nisha yake son sake sa yarinyar aidonsa, dan shi jiyake gaba daya yarinyar tasuma taba masa heart dinsa, duk Wani juyi da mutsinda zaiyi ita yake tunawa,
da alama son yarinyar ne yafara addabar zuciyar sa, yasa mb ya nema masa numbern yarinyar gurin kwata salma but amma yakasa kiranta, because baisan mai zaice mataba
kamar kullum da yasaba zuwa gdn masaukin daddy shida abokansa wani sa'in kuma shi kadai yake kasan cewa because shi bai cika zama gd ba, yawanci gdn masaukin daddy yake tattaro yazo ya kadaice kansa, ya gama hutawarsa indare yayi ya nemi hanyar gd,
yamade kamar kullum yana kwance saman sofa yarintsa ido kamar mai bacci, jin kiciniyar shigowa yasa yamaida kallonsa ga kofa dan ganin mai shigowa, kb ne tafe yashigo cikin dressed dinsa da yasaba kamar na yan isaka, gashi kan nan acukurkude bakin gashi kareshi amma saboda dunyanci yarinata takoma ruwan kasa, hanusa dauke da shesha,
kamal na kallonsa har yakarisu ya zauna," yade boss bacci kakeyine,? kb ya tambayi kamal, "
No kawai ina kwancene kamal yabashi amsa, ,"
Saboda rashin abunyi,? kb yakuma tambaya",
eh to kusan haka kamal yafadi tareda kokarin tashi yazauna, "
to ga abunyi na kwawo maka kasan mu ba arasa nono ariga kb yafadi hade da ajiye tukunyar shishan saman capet yamikawa kamal daya igiyar shima yaja dayan yasuma zuka yana furzar da hayaki,
kamar zukar shishan yake but yakasa gane meyakeji daya, kamar wani yau yasuma Shanta,"
Ammade akwai abunda yake damunka koh yau naganka kamar wani mace bana mijiba, se wani abu kake sanyi sanyi meyake faruwane,? Kb ya watsuwa kamal tambaya,
Kamal dakatar da abunda yake yayi tareda kallon kb yana fadin,"
inba na mantaba kamar na baka labarin naje gdnsu yarinyar da muka buge da mota tareda kawarta, kasan na sanar dake munje tareda mb,"
Eh kafada kunzame kunje ba da saninaba gudun karna bata muku shiri kb yafadi yana tabe baki,"
Aa ba haka bane ganin nayi kana fusace da marin da tamaka gashi kai ba hakuri garekaba, ita kuma tanada fada da masifa ba barinka zatayi ba, kaga garin gyaran gira se arasa ido, shiyasa mukaje tareda mb,"
hmm to meye kaketa kawo wadan nan zantukan kb yafadi azafafe because ransa yasuma baci ya tunu da marin da yasha gurin Nisha,"
bakomai ji nake kamar na kamu da sonta cikin heart dina, "
What so,? Kb yafadi tareda zaro ido,"
Eh ina expecting haka, ko kamai kana muradintane naga kawani zaro ido kamar katsorata, kamal ya fadi yana kallon kb, "
mtsww allah yakiyaye, kaiko mai zakayi da wannan crazy girl din kb
ya tambaya, kamal hararo kb yayi yana fadin,"
waye kake kira da crazy kodan kasha marin crazy girl ne,shiyasa ,? Kb jiyayi yafara kubula rainshi yasuma baci dama yasan za arina tunda yasha mari gaban kamal yasan ya dinga goranta masa kenan,"
mikewa kb yayi yana fadin," thanks agabana kake fadin kakamu da son wata bayan baikon yar uwata dake kanka yayi kyau, kb yafadi yana huci,"
Nifa bawai nace ina sonta bane alama nakeji nace, nasan yarinyarn ma ba lallai ta amince daniba shiyasama ko nuna alama banyiba, kamal yafadi yana mikewa shima,"
dan kada kai kb yayi yana fadin," hmm naji yanzude ba jin wannan wakokin nazuyiba, please key din gdn nan nake bukata inkatashi tafiya gd, wani harara kamal ya watsawa kb tareda fadin,"
mezakayi da key din,?
baby nice zata ziyarceni zamu dan tattauna kb yafadi atakaice,"
ba anan ba, dan nan gdn bana kawo mata bane ana tattunawa dasu ko kataba ganin nakawo mace gd nan,?kamal ya tambayi kb, "
toni ina zan sani tunda ba kullum muke tareba yau da gobe zaka iya kawowa kaima wazaisan anyi kb yafadi,"
hmm allah ya kiyaye ni da bata yar wani masuyima allah ya shiryasu, wannan hanyar da kadaurani kai addu'a nake allah yabani daman sauka daga kanta, kamal yafadi tareda shigewa cikin bedroom yabar kb tsaye tana binshi da kallo har yashige bedroom,
Lallai fa ni kamal yake shirin wula kantawa haka, har wani hanunka mai sanda yakemin ina bata yar wasu, bakomai hanyar da kake neman tsari dashi, shidin zaka tsinci kanka wata rana, kuma akan wacce kake magana yanzu,
da ninaso na gyara mata zama da kaina domin tagane irin mazan da zatasa hanu tamaresu ba irina bane, but amma yanzu na hakura kaida kanka zakamin ramuwa, wani dariyan mugunta kb yasake tareda kada kai yafice yana kuma bushewa da dariya,
yau one week kenan, salma tafara jin saukin sosai Nisha kusan kullum setazo ta duba jikin kawarta because salma kawace tagari shiyasa Nisha ke ji da ita,
yamma lis umma zaune bisa taburma hanunta rike da carbi tanaja, zuciyar ta kuwa fal tunanin mijinta da sun ganinshi ko ba dan yabasu wani abuba dan kawai tasashi idonta, kullum addu'arta allah ya karkatu hankalisa da tunanin sa kansu, kafin mai duka yayi aikinsa, dan bata tunanin yanda takeji ciyon nan bazatayi wani tsawon rai ba,
Yo banda abun umma mai rai ai baya yanke tsammanin kuma cuta ba mutuwa bace,
haka itama Nisha tana can bedroom tana sakawa da kuncewa, tunanin rashin ganin abba dakuma rashin sanin wani hali yake ciki, kullum intaje gun mami nemansa se tace baya nan, inta tambayi ina yaje ko ina yakezuwa ba asamun shi , se tace," itama ba tasaniba, to ina yashiga ko saceshi,
akayi ?
wannan tambayar kullum Nisha kewa kanta but kuma ba amsa, allah shiyasa sirrin ciki da na boye, tana cikin wadan nan tunanin karan shigowar message wayanta yasa tamike tazauna tadauki wayar tashiga dubawa,"
kusan kullum se anturo mata text awayarta da wani bakuwar number wacce itama batasan ta wayeba, kuma Tex ne zafafan kalaman soyayya , wanda ya turo yake bai yayyana mata tsantsan so da kuma kauna dayake mata, yakuma kasa fitowa ya baiyana mata gudun kartaki amsar soyayyarsa,
Nisha tun bata kulawa da text din tana sharewa because atunanin ta bazai wuce mutane masu hada numbern yan mata suna shirmeba, but yanzu tagane har sashenta ba daidai bane,
Saboda wanda ke turo text din yanuna yasanta , hakan yasa tasuma bawa sakon mahimmanci, wajan karantawa, sede yau sakon yasha ban ban da sauran,"
Nagaji da boye kaina agareki, yau zan baiyana kaina kisan ko ni waye da kuma so da kaunar da nake miki, zuciyata zata buga saboda tsantsan so da take yimaki,
zanzo yau bayan sallahn magarib domin gd susan dani, kishirya tar ban babban bako kuma mai kaunar ki maisun farin cikinki akoda yaushe, kihuta lapia
Nisha mikewa tayi ta tsam tsakiyar gado tana sake bin sakon da allah, da sauri tashiga tasuma kiran numbern but amma yaki shiga, nan tacigaba dakira ko zai shiga amma sam abu daya takeji,..
Khaleeseart Raeys ✍️🌴🌴 AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by Oum AmReesh ♥️
Daga ALKALAMIN khaleeseart Raeys ✍️
Free book,
Ya Allah yanda nafara rubutun littafin nan lapia kasa na gamashi lapia,
Page 25, tana tsaka dakira still tasakejin wani sabon sako yashigo wayar, "
I'm sorry banida butar takura miki ko saki cikin wani damuwa, akwai option ra ayin ganina zan iya hakura najiraki har se lokacinda kika bukaci ganina ahuta lapia,
Dan zamikewa Nisha tayi bisa gadon tazauna tashiga maida ajiyar zuciya, tareda sharce zufar dake tsats tsafowa goshinta, ita tarasa waye wannan dake bibiyar rayuwata da wani batun soyayya,
Allah yagani ita kwata kwata ba wani babin soyayya cikin rayuwarta, ko akasin haka, ita karatu tasa gaba tareda rayuwa da mahaifanta yafi mata komai dadi, shiyasama ko gender aure babu alamarinta balle wata soyayya ayanzu,
Kwana biyu da faruwan hakan, nisha na kitchen ta daura musu abincin dare because yamma tayi, tana tsaka da aikace aikacen taji wayarta tashiga ruri,
cikin hanzari ta dauki wayar domin taga mai kira, wannan numbern da ake turo mata sako dashi again yau shiya kirata, tsayawa tayi tana kallon call din har kiran ya yanke,
ajiye wayar tayi tacigaba da aikin dake gabanta, still aka kuma kiranta, jin yanda aka damu da kiran yasa ta dauki wayar tareda karawa akunne ba tareda tayi maganaba,
wani sallallami taji anfara jeruwa daga bisani aka suma magana," asslamu alaikum cikin wata rudadden murya da batasan ta wayeba batasan kuma tawayeba da alama mai maganar ahanzarce yake,
Amsa sallamar Nisha tayi batare da tace wani abuba, " baiwar allah kece nisha aka tambaya, cikin natsuwa gami da gyara tsayuwa Nisha tace,"
eh nice,
kina sane dacewa wani bawan allah yana dab da rasa rayuwarshi ta dalilinki? yanzu haka yana kwance baisan inda yakeba yanata ambatu sunanki, da alama kafin zuwarki rai zai iya halinsa, "
subhanallah please malam kai din wayene,? kuma ni wanda kake magana akai bansanshiba, Nisha tafadi adan tsurace,
ni friend dinsa ne but tsayawa wani bayani bata lokacine zaifi kyau kizo kiga halinda bawan allahn nan ke cikin domin banda Nisha ba abunda yake furtawa kuma ko yanzu aka samu akasi yamutu da sunanki abakinshi munriga munsan kece sila,
dan haka yanzu zan turo miki da address kizo ki tai maki rayuwar bawan allah, ko kuma inyamutu munemi gdn ku mukawo miki gawarsa, ana gama fadin haka akashe wayar,
tashin ankali, Nisha aza hanu tayi aka kamar mai shirin kurma ihu kiris yarage kuka ya subuce mata tayi saurin tushe baki gudun kar umma tajiyu ta,
har kullum tunani take waye yake kokarin shiga rayuwarta bada yar dartaba,? kuma bakuma ita ta gaiyyato shiba, ,? da ahar yake kokarin rasa rayuwarshi ta dalilinta,
cikin hanzari Nisha tafito daga kitchen din zufa ya gama wanke mata fiska, fitowar umma daga daki ta hadu da nisha tsakiyar parlour tana tsaye tayi zuru, "
Ke Nisha yadai umma ta tambaya, cikin hanzari da kirkiro murmushi nisha tace,"
bakomai tareda barin parlourn tanufi bedroom, umma de bayan Nisha tayi da kallon gami da karisawa kitchen din dan ganin maike tafiya, umma na zuwa ta tararda komai Nisha ta kammala se dan wasu aiyuka da bata samu daman karisawaba,
hakan yasa umma tashiga jarisa aikace aikacen, nisha kuwa tana shiga daki ta tazauna tana tunanin iri iri, shigowar sako wayarta yasa cikin sanyin jiki tadau wayar tashiga dubawa, address aka turo mata hakan yasa tashega wasi wasi, because allah ya gani bazata iya daukar kafa taje gurin Wani saurayiba, wannan ma ai se duniya ta tsine mata,
Kuma umma bazata yafe mataba, saurayi yazo guntama bazata lamunci hakaba balle kuma ita tadau kafa taje,
ta wani fannin kuma tsoro take kar akawo mata gawar sauri kamar yanda mutumin dazu ya sheda mata , dan haka gwara ita taje ayi mai yiyuwa tayiwa tufkar hanci,
tashi tayi tashiga kimtsa jikinta, tareda sauya kaya ta nemi hijab tasaka tareda nufo parlour cikin sauri yayi daidai da fitowar umma daga kitchen,"
Ina kuma kike saurin fita kije,? umma ta tambaya tana kallon Nisha dake ta fidda ido, "
Gdnsu salma zani because na kwana 2 banje naduba jikintaba,"
to adawo lapia ki gaishesu abunda umma kawai tace nisha tasa kai tafice,
tunda tafito take ta tafiya tareda tunanin wannan saurayi da ya tacewa rayuwarta haryake tunanin salwantar da rayuwarsa akanta, inko harda gskne shiko wani irin sone haka,?
Nisha tafiya tayi sosai seda tabar arean anguwar tahau titi, sannan ta tsaya ta tsaida mai daidaita tanuna masa address inda zai kaita daga bisani tashiga suka dau hanyar tafiya,
bada wani bata lokaciba haya ta kawosu, daidai jikin gdn mai adaidaita ya dire Nisha, daga nan ta sallameshi tasakai dan ma daidaicin gdn, tura kofar tayi tashiga kirjinta se dukan uku uku yake,
Koda isuwarta cikin compound din gdn bakowa gurin shiru yake, to nan din gdnsune ko ina,? but bata ga mutane cikinsaba, ga kofar parlourn abude yake nisha ke tambayar kanta,
jitayi tsoro yagama mamayeta kamar tajuya takoma because taji gaba daya bata yarda da gdnba, jin shiru datayi ba alamar kowa, maybe ma yan yankan kaine ko kidnapping, soke kokarin wasa da hankalinta da sunan soyayyarta na kokarin ilata Wani,
har tajuya zata fice daga gdn wayarta tayi kara, kamar bazata dagaba sekuma ta dauka tareda karawa akunne,"
Na hangoki ta window but naga kamar kokari kike kikoma please ki kariso bawan allahn nan ya ganki ko zai kuma cikin hankalinsa kafin musamu mukaishi hospital,
daga cikin phone din takejin ana ambato sunanta, daga gefe da wace irin raunan niyar murya, ana neman agajinta hakan ya tabbatar mata akwai matsala kuma akwai kamshin gsky alamarin
dan haka takarisa takutsa kai cikin parlourn bakinta dauke da sallama, ga mamakinta parlourn ma shiru yake ba kowa nan ta tsaya tana dan wul wul ga ido tana karisawa tsakiyar parlourn, jin an murda handle din kofa ana kokarin fitowa daga bedroom din yasa ta kurawa kofar ido dan ganin mai fitowa,
turos tayi tana binshi da kallo tana dan gwalo ido, kamal ne yafito daga dakin yana sanye cikin t shirt da gajeran wando, yayi kyau dashi, tsayawa yayi yana kallonta shima da mamakin mai ya kawo yarinyar gdn ,
Rintsa ido yakumayi atunanin shi ko gizo tafara masa, kara bude idon yayi dakyau because yanda yaji sunyi masa Wani nauyi , tabbas itacede ba wataba tayi tsaye kamar sakaguwa, ta gagara motsi daga inda take,
dawata kasa lalliyar murya kamar wanda yasha wani abu kamal yakira sunan ta yana fadin," Nisha kece ,? mekuma ya kawoki nan,? yajero mata tambaya yana mai kokarin karisuwa ciki parlourn,
ita kuwa nisha jin tambayar da kamal ke mata yasa ya tabbatar mata wani ke kokarin rena mata hankali ko kuma shida kansa yake kokarin zargata, dan haka kafin ya kariso tsakiyar parlourn Nisha tayi baya da sauri tana kokarin barin parlourn,
kirif taga anja kofar anrufe daga waje, Nisha kamar ta tsula fitsari awajan aikin tsoro da kidima, nan tasuma bugun kofar da karfi tana fadin," waye agurin please kabudemin natafi gdnmu, dan Allah , tafada cikin sigan kuka, kamar daga sama taji murya daga waje ana fadin,"
Rashin kunyarki ya kwaceki yaude kinshigo hanu yau zanyi maganin rashin kunyarki, ashema bakida wayo harna iya zargaki yau gaki amakomata, bake har Zaki iya daukan hanu kimari wanda bakisan waye shiba, zakiyi bayani
makwat kakeji Nisha ta hade wani yawu, tareda sakin handle din kofar da tarike tamaida kallonta ga kamal dake tsaye yana rike da head dinsa yana rinrintsa ido tareda girgiza kai,
Nanfa ya tsulale kasa, jiyayi kansa yayi nauyi kafafuwan sa sun gagara daukansa, jiyayi kamar ba aduniyar yake bama, Nisha na ganin haka tayi kansa da sauri tareda tsuguna wa , kusa da kansa tana tambayar sa wanda baimasan tanayiba, "
Kai lapiya kuwa mai kakeyi haka,? please katashi ga budemin kofa natafi gdnmu wajan ummana, tafadi cikin sheshshekar kuka, ganin babu alamar zai tashi yasa tasuma kokarin mikewa tsaye, carab taji yarike hand dinta,
Kallonsa tayi dashima kallonta yake da idonsa dasuka canza launi zuwa jaaa, ganin haka yasa tasuma kwace hanunta, jin yarike hanunta gam still yana kwance saman capet bayida niyan tashi,
baki takai da niyar cizonsa but kafin tayi yunkuri ya jawota saman jikinsa, ya rungume ta tsam, waro ido Nisha tayi because jitayi wani irin yarrr tsoro da firgici yasa tashiga kiciniyar kwace kanta da karfi tana bugun kirjinsa,
shima cikin zafin nama ya yunkura tareda yin kasa da Nisha shikuwa yakuma sama,"
Innalillahi wa'inailaihi raju'un hasbunallahu wani'imal wakil, abunda Nisha tafadi kenan tareda sakin wani ihu tana neman agaji,
Kb daga waje yajiyo ihunta nan da nan yasake wani ihun dadi hankali tareda rawar murna yana sakin wasu wakoki ," yaude yayi magani mara kunya buri yacika,
dan tsa gaitawa yayi da rawan jin shiru yasa yamatsa kusa da kofar yayi kusan minti 10 daga bisani ya dan murda handle din kofar yashiga lekawa ahankali, " inna lillahi wa'inailaihi raju'un kb yafadi tareda kara bude kofar da sauri, kamal ya hango kwance saman carpet kamar macecce keyarsa se fidda jini yake,
gefe kuwa kwalban da sukasha drinks dazu acikine afashe awatse agurin ," subhanallah kb yafadi atsorace tareda karisawa cikin parlourn kusa da kamal dake kwance ya tsuguna yana kallon sa, fusace kb yamike yana fadin,"
Where are you yau zakici ubanki kashemin dan uwa kikayi,? yafadi yana kama kugu, yana dan wul wul ga ido yaga daga ina zata fito, yana tsaka da surutain sa, Nisha ta fito daga bayan labulen da tabuye dama taci alwashin bazata tafiba seta illatashi shima,
yana cikin surutun nasa yaji saukan kwalba akeyarsa shima, bai fadiba seda yajiyu sukayi ido 2 da Nisha yana rike da kansa dake kokarin zubda jini, yasuma kokarin magana nisha ta hankada kirjinsa da karfi yafadi sumamme,
da sauri Nisha tayasar da rabin kwalbar dake hanunta takalli kamal dake kwance gefe takalli kb nan da nan tafashe da kuka tayi waje da kudu
Mai gadi dake zaune awaje saka makon dazu shiharta yatafi zagawa shiyasa baiga shigartaba se fita,
Mai gadin ganin yarinya tafito da gudu hakan yasa yamike atsorace yanufi cikin gdn, yana karisawa parlourn ya kamal da kb kwance cikin jini kamar mataccu, ,"inna lillahi wa'inailaihi raju'un mai gadi yafadi ya rude tareda ciru yar karamar phone daga aljuhu yashiga kiran wata number ringing daya biyu aka dauka, mai gadi nayin sallma yashiga zaiyanu abunda idonsa yagani da abunda yafaru, cikin tsoro da faduwar gaba baba mai gadi baikaiga karisa maganar ba yaji ankatse wayar,
.
ganin haka yasa yamai da wayar aljuhu yaja ya tsaya daga gefe yana kallon su kb dasuke kwance, bada wani bata lokaciba baba mai gadi yaji wani irin gawurceccen hon cikin hanzari ya karisa geat din tareda budewa,
Kyakykyawar mota black mai daukar hankali ta danno kai cikin gdn , tsakiyar compound din gdn akayi parking mai gadi yazo da sauri yabude masa murfin kofar motar yafito,
Masha Allah kyakykyawar namiji dirarre dan matashi maijin kanshi, dan gaye son kowa kin wanda yarasa , yana sanye cikin black suit face dinsa sanye da bakin glass gwanin burgewa da shaawa kamar kasaceshi kagudu,
IG AJEEMAL kenan tareda abokinsa inspector Ahmad gefe kuwa doctor fu'ad AJMAL na gaba suna binshi abaya shima baba mai gadi na biye dasu,
Seda suka shiga tsakiyar parlourn suka tsaya, IG kallo daya yayiwa parlourn daga bisani yakalli kamal yakoma yakalli kb, daga nan yakoma nisa dasu ya nemi kujera yazauna yana kuma kallon gurin su kamal inda suke kwance,"
Baba come here IG yafadi yana kallon baba tareda masa hanu alamar yazu, jikin baba mai gadi har kerma yake ya karisa kusa dashi tareda dukawa saboda yaji mai zai Fadi,
Khaleeseart Raeys ✍️
08105565439
🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by Oum AmReesh ♥️
Daga ALKALAMIN khaleeseart Raeys ✍️
Free book 🥰
Page 26_27
IG seda yakarewa baba mai gadi da kallo daga bisani yashiga fadin,
What happened? meyafaru da wadannan,,? jikina kyarma mai gadi yasuma cewa,"
Yallaboi kamar yadda kace ina lura dashiga da fitan yaran nan agdn nan, yau ansamu akasi domin kuwa wata yarinya ce tasaci jiki tashigo ta aikata wannan ta asar
Kaikana ina har akashigo akayi wannan danyar aikin,? anyama macece ta aikata wannan aikan haka?, inspector Ahmad yafadi tareda tare baba mai gadi da maganar yana kuma kallon sa,
Shima AJMAL din kallon mai gadin yake yanason jin karin bayani, "
Tabbas macece yarinya karama tana sanye cikin hijabi lokacin da tashiga na dan zaga bayine dataga bakowa wajan shine tasidado tashigo, se fitanta nagani.. bai kaiga karisa maganar ba, sukaga IG yamike daga zamar dayayi yakalli doctor fu'ad yana fadin,"
Check them,
doctor fu'ad kamar jira yake dama, nan da nan yashiga checking dinsu, ya kuma tabbatar wa da IG suna da rai, "
dan matsowa yayi kusa da doctor fu'ad tareda karewa su kamal kallon da kwalbar dake watse saman capet wanda akayi amfani dashi wajan lahantasu, hankali yafurta,"
A daukeso daga nan asasu cikin mota, cikin hanzari inspector Ahmad tareda doctor fu'ad suka suma tattara su kb baba mai gadi ya taimaka musu suka kutsasu cikin motar kamar yadda IG ya bukata,
Shima AJMAL din bin bayansu yasuma kokarin yi sekuma ya tsaya yana kallon saman capet inda aka daukesu kamal, hankali ya sunkoya, yasa hanu yadauki wani hadden zuben azurfa, mai kyalkyali da ban shaawa, kallon zuben yashigayi sosae daga bisani yadan sake wata murmushi wacce nima bansan tameye bace, sannan yamike tsaye tareda sanya zuben cikin aljuhu yanufi hanyar fita,
Jikin motar ya taddasu doctor fu'ad suna jiransa tareda maigadi daga gefe, seda ya kariso indasuke yakalli baba mai gadi yana fadin,"
agyara parlourn nan yayi excels arufe shi abunda yafadi kawai yasakai cikin motar yayi mata key, mai gadi dajin haka yanufi geat yabude musu suka fice
*****Nisha***************
Aban garan Nisha kuwa tunda tabar gurinsu kamal tawatsa da gudu tafice daga gdn, bata zame ko inaba sae gd gab goshin magarib, tundaga nesa ta sallami mai adaidaita tundaga kofar gdn ta tsaya tashiga goge hawayen dake face dinta, gaba daya fiskar yayi jawur dashi, seda tagama kimtsa face din ta, daga bisani takutsa kai cikin gdn, koda shiganta ciki bakowa umma bata ciki da alama tana bedroom dibta, cikin sanda tasuma tafi domin shiga dakinta, "
Seyanzu,? Nisha taji muryan umma wacce fitowar ta kenan daga daki , hanzarce Nisha tajiyu tana kallon umma cikin sanyin murya tace," eh seyanzu munata fira da salma ban ankaraba ashe magarib tayi, Nisha tafadi tana tsili tsili da ido, "
To seki samu kiyi sallah kizo ga abinci najiranki, to kawai Nisha tace tanu daki dasauri, umma de bin bayan Nisha tayi da kallo ganin yanda gaba daya fiskar ta tasauya bayacce tasaniba, kamar akwai wani abunda ke damunta, shiru umma tayi kamar mai nazarin wani abu daga bisani tajuya tanufi kitchen,
Nisha tana shiga daki toilet tanufa tazauna tayi kuka mai isarta tashare hawaye tayi alwala tafito, nan tashin fida sallayan tayi sallah tana idarwa tabarke da wani sabon kuka gaba daya abun ya faru yakuma dawo mata,
itakam tashiga uku ina zatakai hakin daukan rai har mutum2 wannan wace kallar kaddarace ta fada mata, lokaci daya akasi ya giftawa rayuwarta, sukuma meye dalilin su nashiga rayuwarta harsuke kokarin rushe mata gobenta, ?tana tsaka da sheshshekar kukan taji muryan umma,"
Subhanallah meyafaru meyasame ki kike kuka, ,? umma ta tambaya lokacinda ta karisu tasun kuya kusa da Nisha tana tambayar ba asin kukanta, cike da wayancewa Nisha tafada jikin umma tareda sakin wani kukan tana fadin,"
Umma ina matukar kewar abbana inason sashi cikin idona, inason sani wani hali yakeciki, Nisha tafadi nan da nan taji kukan ya hadu mata biyu, kukan kisan kai da kukan rashin abba, ba Nisha ba hatta ita kanta umma jitayi gabobinta sunyi sanyi zuciyar ta tayi wani irin rauni hawaye nasonyi zarya saman face dinta, kamar ta tayata suyi kukan tare but bazata jure ganin diyarta cikin wannan halinba, dan haka tamatse nata kwalan ta dago nisha tana fadin,"
Ya isa haka karki damu abbanki yana cikin kushin lapia kina misha fatan alkhari da addu'a a duk inda yake allah ya karkatu hankalisa gd, yanzu kitashi muje kici abinci umma tafadi tana mikar da Nisha tsaye suka fice daga dakin,
kwana2 da faruwan hakan amma sam Nisha takasa mancewa da abunda yafaru, koda yaushe jira take bincike yayi bincike taji sallaman yan sanda sunzo tafiya da ita, tana zaune tayi jugum adaki tana tunane tunane tajiyu sallama daga bakin door ana kokarin shigowa,
salma ce tafe taja ta tsaya daga bakin kofa tana kallon Nisha dake kallonta da rinannun idanuwanta, cikin hanzari salma takarisa gadon nisha ganin yanda face din ta yakoma da alamar damuwa,
salma nazama ta dafo shoulder Nisha tana kokarin magana setaga Nisha tafada cinyarta tasake wani kuka mara sauti kasa kasa,"
salma nashiga ukuna na aikata abunda ya dameni, nayi abunda bazan yafewa kainaba
dagota salma tayi tana kallon tasuma tambayar ta,"
Lafiyanki mekike? fada haka keko wani laifine kika aikata kiketa wadannan zantukan, ? dago ido Nisha tayi tana fadin,"
Kisa nayi mutum harbiyu nan Nisha tazaiyanawa salma tun farkon wakanan lamarin har karshe , yanzu tunani na sun mutu ko suna raye allah masani Nisha tafadi cikin kuka mai tsuma rai,"
suna raiye basu mutuba kamar yanda kike expecting "
how kinsan abunda yafaru ne,? Nisha tafadi hanzarce tana zazzare ido,"
Eh but naga wautanki cikin lamarin kuma banyi tsammanin akwai wani sabon lamari da zaishigo rayuwarki kibuyeminba, ko danki bukaci idea daga gareni amatsayina na kawarki kuma aminiya wacce zamu kashe mubinne tare ba wanda yaji balle yasani why,?
salma tafadi tana kallon Nisha datayi mata zuru da ido cike da mamakin magan ganuta takasa cewa wani abu, kinyi shiru inata surutu bakice komai ba salma tasake fadi still idonta bakan Nisha ,"
Please bani labarin taya kikasan wannan abun yafaru, Nisha tafadi asukwane, ,"
dan gyara zama salma tayi tana fadin," inba ki manceba mb friend din kamalne , kuma wannan abun da yafaru kanshi nazo muyi magana, shine makasudin zuwana gdnan,
Nisha share hawayen face din ta tayi hade da gyara zama tana sauraron salma da abunda zatace,"
Mb baya gari baisan mai akecikiba, yakirani yakuma sanar dani abunda yafaru, yasheda min tun bayan faruwan lamarin kamal yakirashi cikin tashin hankali da damuwa yakura masa jawabin abunda ya wakana ,
Ba damuwarsa illan dakika masaba, damuwar shi baisan mai ya aikata agarekiba fatan shi Allah yasa ba abunda yashiga tsakaninku ,
duk wannan abubuwan da suka faru babu laifin kamal, wannan duk shirin kb ne, yayi duk yanda zaiyi dan yacutar dake ta dalilin magan ganu mara dadi da kuma marinshi da kikayi
🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by oum amreesh
( Khaleeseart Raeeys)
Free book 🤗
Godiya mai tarin yawa gamasoya abun alfahari ina alfa hari daku koda yaushe 🤝
Page28
Kamal yayi iyaka kokarinsa wajan ganin ya tare duk wata hanya da hakan zai kasance
ganin haka yasa kb yayi amfani da kamal wajan cutar dake ta hanyar zuba masa abu cikin abunsha batare da saninsaba duk abunda kikaga yafaru time din kamal baisan da kasan cewarsaba,
dan nunfasawa salma tayi kafin tacigaba da fadin," allah sarki yanzu suna can suna amsar magani kamal duk ya gama daburcewa cikin wannan lamari da ya afku, kwata kwata baida masaniyar abunda dan uwansa ke shiryawa,
gaskiya kb takadarine hmm Allah ya kyauta yacigaba da karemu daga sharrin masu sharri,"
amin Nisha tafurta asanyaye, salma duban Nisha takumayi wacce tayi kalar tausayi se kuma tamai da idonta ga phone dinta dake gefen cinyarta tadauka tareda kai hand tadauki dan ma daidaicin phone din nisha,
wani number salma tashiga jerawa Nisha cikin phone dinta sannan tamikawa Nisha wayar tana fadin,"
gashi wannan numbern dakike gani nasanya miki cikin phone numbern kamal ne shiya bukaci da abaki because yace inda akwai wani issue daga gareki you can call him dan haka ki barshi cikin wayarki tana gama fadin haka tamike tana fadin,"
To nikam bari nawuce sena jiki tafadi tareda shigewa gaba itama Nisha mikewa tayi tarufa mata baya suka fice, kishingide umma take saman kujera wacce tun shigowar salma gurin ta sameta, ganin fitowarsu yasa umma ta mike tana fadin," har anfito
"Eh umma salma tafadi tana washe baki yayinda Nisha ke biye da ita,
" To kigaida gd kice ina gaida ummyn taki,
"Zataji inshallah daga haka sukayi sallama nisha itama daga bakin parlourn sukayi sallama tajiyu ta dawo kusa da umma tareda yin matashi da cinyarta tana sauke ajiyar zuciya ahankali jitake zuciyarta fes,.
dan shafo suman kan Nisha umma tayi tana fadin,"
Ina zuben da abbanki yasemikine kwana 2 ban ganshi ayazunkiba kin gaji dashine ko yardashi kikayi awani guri dan nasanki da shiririta wani lokacin,
rass nisha taji kirjinta yabuga nan ta sulale tamike daga kwanciyar tashiga kallon yatsun hand dinta sam ko batayi da zuben baya hanuntaba se yanzu da umma ta ankaradda ita "
to ina zuben yashiga kuma ina nayaddashi? Nisha tashiga tambayar kanta cikin zuci, ganin umma ta tsareta da ido yasa Nisha kirkiro murmushi tashiga sosa keya tana fadin,"
Nima bansan wani lungun yashigaba tunda natashi abacci ban kalleahiba maybe ya yashiga wani gurin kinsan dama bai kama yatsun hand dina sosaiba, amma dai zan dubashi bata jira taji mai umma zatace ba tawuce fuuu tayi daki tabar umma awajan,
tundaga wannan lokacin nisha ke neman zuben ta dan zubene mai matukar mahimmanci agareta zuben da abba ya bata lokacin da yasa kafa yabar gdn bai sake waiwayan suba,
batan zuben ba karamin taba zuciyarta yayiba duk lokacin da take tare da zuben jitake tamkar da abba take tare, gashi yau tawayi gari babu shi atare da ita bata kumasan inda taya dashiba,
aban garan kamal kuwa kullum tsumayin kiran Nisha yake dan atuna ninshi kiranta agareshi tamkar tayafeshini komai ya wuce,
ita kuwa Nisha tun time din da salma tasanya number kamal cikin phone dinta batayi tunanin kiraba bata kuma ji alamar zata kiraba har se lokacin da umma ta kwanta rashin lapia sannan tasamu daman kiranshi nanma ba yanda ta iya batada kuma wani zabi because tasan yana da arzikin da zai iya taimaka musu , awannan yanayi Nisha ta dangana ga kamal wanda lokacin sukayi ido biyu da nabilah wacce ta daura mata karan tsana duk da batasan dalilin zuwan Nisha wajan kamal,
Atakaicede wannan shine labarin abubuwan da suka faru abaya***********
Parlourn ne yadau shiru tamkar bakowa, kama daga su fadeela muhaiseen da sukejin abun da yafaru abaya da kuma abunda kb ya aikata, kowa da abunda yake sakawa cikin zuci,
Nabilah kanta kasa tagagara daga kai gaba daya kunyan Nisha da tausayinta sungama mamaye kwanyarta, ta kaicin abunda dan uwanta kb yayi yagama bata mamaki duk da tasan ba bakon al amari bane agareshi komai akace yayi babu makawa zai aikata, suna tsaka da wannan alhinin sukajiyo sallama ana kokarin shigowa,
dagowa sukayi sukayi dukansu suka tsurawa kofar door din ido dan ganin mai shigowa, goggo rabi ne tafe tana sanyi cikin lullube fiskarta cike da fara' a ta kariso tsakiyar parlourn tanabin kowannensu da kallo daga bisani ta tsaida idonta kan nabilah dake ta matsar kwalla, "
oh haryanzu kukan bai kare bane goggo rabi tafadi tareda matsawa kusa da ita ta dagota tamikar da ita tsaye tana fadin,"
Kukan nan ya isa haka, kukuwa duk taronku nan arasa mai lallashita, barinma kai kamal kana kusa da ita kanaji tanata asarar hawayenta, to kutasu muje Daddy ya dawo yana nemanku a parlourn sa, tana gama fadin haka ta tusa nabilah agaba kamal da mb tareda muhaiseen suka rufa musu baya jiki amace kamar wayanda aka zarewa laka,
reeda fadeela Nisha anrasa mai kwakwaran mutsi acikinsu, Nisha hawayen idonta tanema tarasa sotake tayi kuka ko abunda takeji cikin zuciyarta zai ragu but hawayen yaki zuwa balle kukan yabiyo baya, "
kutashi mutafi muje mukwanta , reeda tayi magana cikin karfin hali yayinda tamike taja hanun fadeela da Nisha suka fice ,
parlourn bakowa duk sun hauwa sama parlourn Daddy hakan yabasu daman shige bed room dinsu domin shirin bacci, seda kowannensu ya kimatsa yayi night dressed daga bisani sukanemi guri suka kwanta, amma sam bacci yaki zuwa se kwafa suke suna tsake in fadeela tayi se reeda takarba itama se juyi suke sun kasa bacci gaba daya haushin kb yagama cikasu jisuke inama ace zasu ganshi yanzu se sun hadu sunmasa dukan da se yagagara tashi, duk da sunsan sangarcewa irin tashi mom dinsa tagama san gartashi but basusan abun yakai hakaba yana kokarin lalata yayan wadan su da kuma son daura yayansu kan turban da bai daceba,
Nisha shiru tayi ta lumshe ido kamar mai bacci duk tanajin yanda su reeda suke juyi sun kasa bacci saboda damuwar dan uwansu,
itama bacci yaki daukarta gaba daya tausayin kamal da kaunarsa suna taba zuciyarta , kwata kwata batasan da kaunar da kamal yake mataba se yau da labari yasa tasani , to amma yanzu haryanzu yanajin sonta cikin zuciyarsa kamar yadda yafadi abaya ko kuwa yashafeta cikin heart dinsa yanzu Nisha tashiga tambayar kanta
🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by oum amreesh ❤️
(Khaleeseart Raeeys)
Free book 🤗 to all my lovely fans
Page29_30
Duk da tasan abaya tasawa zuciyarta babu wani tunanin akan so ko soyayya cikin rayuwarta amma ko yanzu kamal ya gabatar da kaunarsa agareta zata amince dashi batare da wani jayayyaba,
saide yanzu tasan hakan ba mai kasan cewa bane because yanzu yana da mata kuma tasan sonda nabilah keyiwa kamal akwana atashi zai manta da wani sonta da yatabayi gashi yanzu zuwa gobema wata kila basa kasar se yanda tayi dashi,
da wadannan tunane tunanen bacci barawo yayi awun gaba da ita suma su fadeela tuni bacci yacinye idanunsu,
Abangaransu kamal da nabilah sun tattara parlourn Daddy nasiha tayi nisa ammi hajja mama goggo rabi gefe muhaiseen da mb kowa yana tofa albarkacin bakinsa, daga karshe daddy yakalli kamal yana fadin,"
gobe tafiyar taku ko an daga?
dan dagowa kamal yayi yana kallon daddy nasu fiska bayabo ba fallasa yace,"
No tomorrow inshallah, because akwai wani wasa da zamuyi cikin satin,
haba mutumin basusan kai sabon ango bane yau aka daura maka aure ba daga kafane muhaiseen yafadi yana kallon kamal cike da zolaya, ,"
ba daga kafa malam su ina ruwansu yaje yabuga wasa kawai shine magana mb yafadi yana dariya,
dariyarsu muhaiseen suka shiga masa suna tsukanarshi shikuwa kamal kallonsu yake yana hararansu yana cizon lips, "
to allah de yaba da saa yakuma baku zaman lapia yasa albarka cikin auran ku, muyiwa annabi salati,
daga nan aka shiga rufe zama da addu'a daga bisani kowa yamike yanufi turakarsa, goggo rabi da kanta tamaida nabilah dakinta inda tadauketa dazu,
Kamal kuwa suna waje yaraka abokinsa mb tareda muhaiseen dan shima ba agdnsu yasaukaba hotel yakama dan ba wani dadewa zaiyiba bikin kamalne yakawoshi yanada aiyuka da yawa agabanshi, seda yarakosu kowannensu yashiga mota mai gadi ya bude musu geat suka fice sannan kamal yajuya yanufi part dinsa,
yana shiga a parlour ya tarar da nabilah bisa kujera ta takure seda ya iso tsakiyar parlourn yakallita yana fadin,"
kitashi kije kiyi alwala kizo muyi sallah, dan dago kai tayi ta kalleshi time din har ya juya baya yanufi toilet din dake parlourn danufin alwala ganin haka yasa nabilah mikewa jiki bakwari tanufi cikin bedroom, direct tayi toilet tayiyo alwala ta dauko musu sallaya tayiyo parlour ,
atsaye tasameshi yana gyara hannun rigarshi da ya tattare wajan alwala,tana karisowa tashin fida masa sallayan daga bisani tayi baya ta shin fida nata, nan yashige gaba suka tada sallah,
bayan sun idar sun dan dade awajan suna addu'a daga bisani suka mike nabilah ta ninke sallayan tamayar bedroom ta dawo ta zauna, "
ba zama zayiba kitashi kidauko wancan ledar kamal yafadi yana kallon nabilah yana mata nuni da ido inda ledar take , ahankali tamike tanufi dining table inda ta hago ledar ta dauka daga bisani tadawo ta ajiye saman table din parlourn ta nemigu tazauna, "
kibude kici mna kamal yafadi yanadaga kishingide daga saman sofa yana latsa wayar hanunsa, "
Kai kumafa,? Nabilah ta tambaya tana kallonsa
" Akoshe nake abunda kawai yace kenan yaci gaba da abunda ke gabansa, shiru nabilah tayi tana kallonsa daga bisani ta dauke kai daga kansa tasauke kan ledar tashiga budeta, ledodine guda biyu aka sasu cikin leda daya shiyasa tun daukowa datayi taji ledar da nauyi,
chicken roasted fish se pack din irish guda biyu daya ledar kuma yoghurt kayan shaye shaye na drinks d
tareda kayan marmari bada wani bata lokaciba tasuma ci dan kuwa yunwane atare da ita,
tana tsaka daci tsulum taga ya mike yana kokarin nufa bedroom ,"
indan kin kammala kishigo ciki
to nabilah tafadi baki na fari, daga haka yajuya yashige ciki,
tana kammala wa kamar yanda ya umarceta ta tashi tanufi toilet ta wanko hand dinta tare da bakinta sannan tanufi bedroom din
akwance tasameshi time din harya sauya kayan jikinsa zuwa farar jallabiya face dinsa na kallon sama ya lullube jikinsa da blanket idonsa alumshe kamar mai bacci, tsayawa tayi kikam kamar wacce aka dasa agun tana kallonsa, "
kinemi gu kiwanta mana kintsaya, kamal yafadi yana kallon ta, ahankali tamatso jikin gadon tasuma kokarin hawa,"
Waited! kamal yafadi yana kallon kayan jikin nabilah wani tsadeden les mai nauyi ga kuma lullube bisa kanta, "
zaki iya bacci da wannan dress din jikin kin,? cikin fiskar tausayi nabilah ta kalleshi tareda gyada masa kai alamar" eh
okay kamal yafadi tareda gyara kwanciya itama tarabe daga gefe ta kwanta ta rintsa ido daga ita harshi ba wanda ya iya rintsawa se juyi da kyar suka samu bacci ya daukesu
Guraren asuba aka suma kiran assalatu wanda ya doki kunnuwan nabilah wanda yasa tamike tazauna gaba daya baccin rabi da rabi tayishi because kayan jikinta duk sun isheta, gefe kuwa tamaida kallonta ga kamal dake kwance yana bacci hankalin kwance dan shi ko kiran sallahn dama can yayansa ajmal shike zuwa yatashisa sallah asuba ko daddy in ka rasa 1 tofa ranar amakare za ayita,
tashi tayi tanufi toilet tayi alwala nan tasamu ta sauya kayan jikinta zuwa mara nauyi yar gown mai lushi tasamu tasa daga bisani tayi gadon dumin tashin kamal,
tana zuwa kusa dashi tashiga tashinsa ,nan yabude ido tasanar dashi dayatashi yayi sallah nan ya mike ya saukko daga gadon yanufi toilet tana ganin shigarsa ta shin fida sallahya tasuma gabatar da sallahnta,
yana fitowa yasa kai yafice yana fitowa sukaci karo da daddy shima yafito da niyar fita masallaci, nan kamal ya rufa masa baya suka wuce,
nabilah na idar da sallah ta haye gado ta kwanta nan da nan bacci mai nauyi ya dauketa,
shima kamal yana dawowa daga masallaci yanufo bedroom din yasamu nabilah tayi rashe rashe tana bacci da alamar baccin yayi nisa, dan jinjina kaiyayi yana kuma kare mata kallo seda ya kalleta sosae daga bisani ya lumshe ido yabude sannan yasakai yafice daga dakin ya koma parlour kan sofa ya kwanta ya lumshe ido yanata kwancewa da sakawa cikin ransa,
karfe 10 nasafe ahali daya antattara gurin cin abinci anaci ana raha ana kuma tadi, kamar yanda suka saba dazaran sun kammala breakfast za adawo parlour acigaba da fira , yauma hantake , Nisha na kusa da hajiyanta farida da reeda suna kusa da daddy sun sanyashi tsakiya se goggo rabi da ammi suna daga gefe cikin farin ciki da annashuwa, sallaman su kamal da nabilah yasa suka dan dakata suna kallon shigowar su,
Kamal na gaba nabilah nabiye dashi tareda try din breakfast da ammi tasa baba barka ta kai musu, ammine ta kwadawa barka kira baba barka na fitowa ammi ta umarceta da ta amshi try din hanun nabilah, nan barka ta amsa tanufi kitchen dashi, hakan yabawa su kamal daman karisawa cikin parlour kamal daga gefe saman carpet yasamu guri yazauna haka itama nabilah kai sunkuye nan suka shiga gaisawa dasu daddy seda suka gama gaisawa kamal ya dan dago ya saci kallon Nisha datayi lamuda ita uwar son jiki tasanya kanta saman shoulder din hajiya kamar wata mara lapia gaba daya ya sakan kance da kallon Nisha wacce zuciyarta ke bata kamal na kallonta but sam takasa daga ido takalleshi because hawaye zai iya ziyarta idanunta,
nabilah duk tana lura da kallon da kamal ke yiwa Nisha ban sauran yan parlourn da hankalinsu ke kan hira,
Nabilah ba kallon kamal , kamal kuwa idonsa na kan Nisha duk da nabilah ta lura Nisha batasan da kallon da kamal ke mataba, gaba daya setaji zuciyarta na mata suya because nabilah tanada zafin kishi sosai musamman akan kamal
🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by oum amreesh
(Khaleeseart Raeeys)
Free book 🤗
Page29_30
Jitayi tamkar tasa kuka ganin abunda idanuwanta ke kallah, shigowar su mb da muhaiseen yasa duk ilahirin hankulansu ya dawo garesu,
Nan su mb suka shiga gaisawa dasu daddy, daga bisani muhaiseen yakalli kamal yana fadin,"
My man muje ko,
jiki ba kwari kamal yamike ganin haka yasa nabilah mikewa itama, daga bisani Daddy da dukanin mutanen parlourn suka tashi domin yiwasu kamal rakiya,
seda suka iso filin gdn indasu muhaiseen sukayi parking, goggo rabi ta bude kofar motar gdn baya ta kutsa nabilah wacce hawaye suka suma wanke fiskar ta, ammi hajja mama reeda fadeela se allah ya kiyaye sukeyi tareda musu fatan alkairi, banda Nisha dake gefen hajja mama tayi rau da ido kamar mai shirin kuka,
Shima gdn baya inda nabilah tashiga kamal yashige ,"
Allah ya tsare yakiyaye kakula dakanka kakula da kanwarka sosai please daddy yafadi yana dafa shoulder din kamal,"
Inshallah Daddy kamal yafadi yana yar murmushi daga haka Daddy ya rufo musu kofar motar nan su mb suka shige gaba muhaiseen shine me driving ,
Nan mai gadi yabude musu geat daga nan muhaiseen yayiwa motar key suka fice, seda sukaga ficewarsu aharaban gdn gaba daya hakan yabawa su daddy daman dugumzuma su koma parlour inda suka fito,
kowannensu jiki amace abun ba dadi , haka kowa yanemigu yazauna sukayi shiru nadan wani lokaci, daga bisani Daddy yasuma kokarin mikewa, harya fara nufa upstairs se shigowar su heelah tareda mom dinta hajiya jumana, hanunta dauke da na aheel kamar wayanda aka jefo daga sama,
ganin haka yasa daddy jiyuwa ya koma yazauna inda ya tashi suna ganin isowar su, aheel cikin hanzari da dauki ya zame hanunsa daga na kakar tashi da gudu yanufi inda yaga Nisha zaune ya fada saman cinyar Nisha tareda washe baki, yana fadin,"
Aunty!
rungumeshi nisha tayi cikin farin da daukin ganin shi , "
ba shakka hajiya jumana tafadi tana tabe baki yayinda take kallon aheel da Nisha yanda suka wani rungumi juna, gefe takalli heelah wacce itama idanta ke kansu ,
seda suka karisa tsakiyar parlourn heelah da mom dinta suka nemigu suka zauna, suna bin yan parlourn da kallo wanda suma idansu akansu yake, cike da mamakin ganin su,
hajiya jumana atsatsaye ta daga musu gaisuwa suka amsa ba yabo ba ballasa, itakuwa heelah baki tatura gaba bata daniyar gaishesu jin mom dinta ta zungudeta yasa tabude baki ta daga musu gaisuwa ciki ciki suka amsa,
hakama su reeda da Nisha suka gaisheda mom ta amsa nasu reeda amma nisha ko kallo bata ishi hajiya heelah ba,
"Lapia kuwa,? Daddy yafadi yana kallon su
" Eh lapia yar kenan magana nake tafe dashi ko nace kara na kawo, hajiya jumana tafadi atakaice, ""
kara! daddy ya furta ahankali, se kuma ya kalli su fadeela ya basu umarnin su tashi sushiga ciki, nan suka mike dukansu suka nufi bedroom tareda aheel duka,
"Kara kuma karan wa kenan hajja mama ta tambaya,
rabi! dalili nakeso tabani na kama diyata taita duka kamar jaka, saboda kawai fada ya hadasu da waccen yarinyar Nisha take ko waye, rabi bata tsaya taji kan zanceba tayi kan heelah da duka ,
kunganta tanan tun jiya zazzabi mai zafi yarufeta tayiyo gd ba wanda ya damu da damuwarta balle yasa me yasameta,"
Subhanallah anan gdn kum wannan abun ya faru, ammi ta tambay
cike da yamutsa fiska hajiya jumana tace ,"
Aina kike tunanin hakan zata faru inba anan dinba, ranar da ake shirye shirye tafiya dinner hakan tafaru dalili daya hana heelah zuwa partyn kenan sbd rashin kyautawa da kunya tata cikin friend dinta, anuna mata kasawarta, angwada mata bare ta fita mutunci,
parlourn ne yadau shiru kaman ba mutane cikinsu mamaki hajiya jumana da maganganunta ya gama basu mamaki,
Daddy ne yamaida kallonsa ga rabi wacce tayi tsuri tana kallon heelah da mom dinta da irin karai rayinda suka zo dashi,"
Rabi kinji abunda hajiya tazo dashi daddy yafadi,"
Naji sede amma sun fadi sun zuciyarsu ne indan zasu fadi yanda zancen yake heelah ce batada gsky nikuma amatsayina na babba nayi hukunci yanda ya dace, "
Oh hakama zakice mun fadi sun zuciyarmu to shikenan nida kaina zanyiwa tufkar hanci dama nazo nafadane dan kusani but tunda kun sani shikenan, hajiya jumana tana gama fadin haka tasuma kokarin jan hanun heelah, ,"
Dakata mana yakuna abu sekace wasu kananan yara kutsaya abin abun abun asunnu mana, daddy yafadi yana kokarin dakatar da hajiya jumana daga kokarin tashin da take, "
kin kawo karanki munji mun gamsu muna baki hakuri bisa kuskuren da ya faru, hakan bazata sake kasance waba,
kuma batun rahilah ta koma dakinta tazauna duk abunda yake damunta za amata magani anan, batun bata da lafiya ta koma gd duk bai tasuba, "
Mijintafa baya nan kuma ko sanar da ita baiyiba balle tasan time din da zai dawo , ya barta ita kadai ba waya ba komai se bautar dansa datake ko time din zuwa aiki yanzu batadashi , baisan wani hali suke ciki ba wayarsa akashe,
dan haka kubarni zan kula da abuna agdna har ta warke ta kuma haiyacinta idan da yiyuwar da wowa seta dawo ai ga danku shikam nasan yafi kaunar zama anan, dama nan din yafi dacewa dashi, nabarku lapia,
daga haka suka mike suka fice, baki bude daddy yabi bayan matar dan uwan nasa da kallo daga bisani ya jin jina kai tareda sunnar da kai kasa
Nanfa daki yasake daukan shiru, jiki asanyaye daddy yatashi ya haura sama, yabarsu ammi saune suna jimami, ba wanda yacewa da dan uwansa kala,
jim kadan hajiya tamike tanufi hanyar fita goggo rabi ma sidi sidi ta tamike tabi bayan hajiya, ganin haka yasa ammi tashi itama jiki ba kwari tabi bayan mijinta,
Yaufa zama sam bata kare da dadiba kamar yanda aka saba, aheel yanacan bedroom dinsu Nisha yanata zuba musu surutunsa da yasaba baisan su mummynsa sun tafi sun barshiba, su kuma sun biyeshe da shirmensa basu san wainar da aka gama tuyawaba ,
rayuwa tacigaba musu kamar yanda suka saba cikin farin ciki da annashuwa Nisha da kanta tashiga da wai niya da aheel cinsa shansa duk ita ke kula dashi, domin ammi tasanar dasu heelah batada lapia tana gun mom dinta ke kula da ita shiyasa tabar aheel anan, jin hakan ba karamin dadi yayiwa Nisha ba dan tanaso yaron sosai kuma tana son kasan cewa dashi
shiyasa ta dau ragamar kula dashi tare suke kwana su tashi ta shiryashi cikin uniform tarakashi har mota drive yakaishi
aban garan hajiya kuwa takasa mancewa da abunda uwar heelah tazo tayi , na maganganu na rashin da'a dacewa da samarwa karya wajan zama. ,
gaba daya abunda tazo tayi yabata mamaki batasan tsaurin idon jumana ya kai hakaba , ba inda diyarta ta barota, ashe gurin uwarta take koyan wasu halayi da da'biu gaba daya tagama shagwabasu da lalata tarbiyarso da sunan wani so,
Itade hajiya tun daren ranar tagaba yanke hukunci kuma very soon zata zartar dashi kuma dole akarba huncin da tayanke ko anaso ko ba aso tunda kowa kasa yake da ita🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by oum amreesh
(Khaleeseart Raeeys)
Page 31
Bayan yanke hukunci na hajiya take ta dau waya ta dannawa abban heelah kira tasanar dashi tana bukatar ganinsa nan yasheda mata baya gari but inshallah allah in ya dawo zaizo dajin haka hajja mama ta katse wayar tasa ido rana da lokacin zuwansa,
Ranar alhamis da dare bayan sun kammala dinner yau ba dan wani dugun hira sosai kowa yanufi ma kwancinsa ,
goggo rabi da hajiya suna zaune parlour suna jiran dawowan su Daddy da abban heelah domin sun sanar da hajiya suna tafe tare,
ba dadewa motarsu ta kunno kai cikin gdn mai gadi yabude musu geat suka shigo, sunayin parking direct part din hajja mama suka nufa,
haka su daddy suka shigo cikin parlourn daya nabin daya suka nemigu daga gefe suka zauna,
nan suka shiga gaisawa da hajiya daga bisani sukayi shiru dan jin meys makasudin ganinsu da hajiya takesonyi , "
Modi wai meya yake faruwa agdn kane, hajiya ta fadi tana tambayar abban heelah, baki na bari yasuma maganaa,"
Haj.. hajiya mai kuma yafaru,?
Magana nake akan matarka da heelah naga kamar yanzu sundauko wata da bi' a narashin ta ido,"
Hajiya gwara kiyiwa yaya modi bayani yanda zai gane ba se anbita wani dugun turanciba, bari nina kura masa jawabin abunda ya wakana bayanshi, goggo rabi ta karbi maganar,
Heelah da mahaifiyarta bakaga iban albarka da rashin kunya da sukazo suakayi agdn nan ba agaban hajiya,
Nan goggo rabi ta labarta masa abunda yafaru wanda jin hakan ba karamin mamaki yayiba, duk da yasan halin jumana sarai za ta aikata ,
Shiru yayi kansa kasa yakasa cewa komai, se tsinkayar muryar hajiya yayi dacewa,"
Ni baruwana da rashin kunyar da sukazo suakayi duk wanda yayi na gari dan kansa, tunda tace yarta baza tazauna tayi zaman aure kamar yanda kowa yakeyiba ba matsala gari da yawa maye bazaici kansaba,
duk lokacin da taji zata iya dawowa dakinta yana nan yana jiranta , amma kafin nan akwai hukunci dana zartar hajja mama tafadi tana kallonsu,"
hukunci kuma hajiya? wani irin hukunci?"
Gobe in allah ya kaimu bayan sallah jumma'a ina bukatan adaura auran MODIBBO da yarinyar nan Nisha"
Hajiya aure kuma? please kar ayi gaggawar yanke wannan hukunci mana, idan baki manceba ko auran MODIBBO na fari bawai da amincewar sa bane kekika bukataci ahadasu muka hadasu yanzu kuma ake shirin kakaba masa wani,.. daddy yafadi cike da damuwa ,"
Nasani idan yanzu kowa bayida bukatar hakan ni inaso, kamar yanda nabukaci nabaya akayi to wannan ma haka nake bukatar akullashi ,
dan haka bana bukatar shawarin kowa umarni nake baku ba shawaraba, koshi MODIBBO danake shirin kara masa auran bai isa ya kaucewa magana taba ,
naso agabana za adaura auran ina gani amma kasancewa ana bukatan shaidu shiyasa nabarshi zuwa gobe, dan haka indan allah ya bamu tsawon rai zuwa gobe ashafa fatiha,
Daga Daddy har abban heelah shiru sukayi suna jinjina maganar hajiya ammade wannan hukunci data yanke da tsauri yake, to amma uwarsuce ba yanda suka iya basu isa sukaucewa maganar taba,
Goggo rabi kuwa se washe baki take ranta kal zuciyarta fes ba karamin jin dadi hakan tayiba"
To kutashi kutafi dare yayi se allah yakaimu goben, hajiya tafadi, jiki asanyaye suka mike suka fice ,
Daga waje suka tsaya sukayi sallama abban heelah yashiga motarshi mai gadi yabude masa yafice, daddy nagani tafiyar dan uwan nasa shima ya kutsa kai cikin parlourn haurawa yayi sama cikin bedroom dinsu,
a zaune ya tadda ammi gaban mirror tana shafa mai, ganin shigowar sa yasa ammi mikewa tashiga masa sannu da dawowa, "
Yauwa ya amsa tareda neman bakin gado yazauna yana dan dafo goshinsa,"
Bari naje nashirya maka dinner,"
Ah no da kinbarshima, akushe nake, daga fadin haka ya mike saman bed din face dinsa na kallon sama,
cike da nitsuwa ammi ta matso kusa da bed din gefe tanzauna, tana tambayar shi,"
Allah yasade lapia naganka kamar cikin damuwa, bayida niyar fada mata halinda ake ciki, but amma ba amfanin boyewar tunda dole zata sani koshi bai sanar da itaba, "
Hajiya tanaso ta kunno wutar da bazata iya kashetaba, daddy yafadi cikin damuwa"
What do you mean ammi ta tambaya adan tsorace , "
aure takeso ahada tsakanin MODIBBO da waccen yarinyar Nisha,"
What aure? kuma da Nisha? Because of what ammi tafadi akideme ,"
Yes aure, nasan bazai wuce dan magan ganuda mom din raheelah tazo tayi bane maybe abun ya bata mata rai shiyasa take kokarin yanke wannan hukuncin, "
Kana nufin MODIBBO bai san da wannan hadinba to ya za ayi kenan, amma ta tambaya "
Muzubawa sarautar allah ido hajiyar data hadasu da kanta zata musu bayanin dagashi har ita yarinyar mude ta bukaci daura auransu gobe inshallah, Daddy yafadi, "
Allah ya zabar da abunda yafi zama alkairi fadar ammi, "
Ameen
yaude gaba daya suna cikin zulumi akan wannan alamari mai zaije ya dawo?
taya MODIBBO zaizo ya riski wannan lamari aure da yarinyar da baisan waye itaba, su kansu basu da cikekken labari ko masaniya akan rayuwarta , sude susan yarinyar batada kowa hakan yasa hajiya ta janyo yarinyar jikinta takuma bukaci zamanta agdn
yau kuma kwatsan ta bukaci ta hada auran yarinyar tare da jikanta,🌴🌴 IG AJEEMAL, 🌴🌴
Story and writing by oum amreesh ❤️
(Khaleeseart Raeeys)
Whatapp number
08105545639
Face book account
Khaleeseart Abdullahi Bello,
Free book 🤗
Page 32_33
Washe gari hajiya na sashinta cikin parlour saman sallaya bayan gudanar da sallah jumma'a, tana lazumi, gefe goggo
rabi saman kujera bayan idar da nata sallah tashi amfani da wayar hanunta,
Shigowar su daddy bayansa dauke da abban su heelah hannayansu dauke da goro da minti suka taho suka direwa hajja mama gabanta face dinsu ba yabo ba fallasa,"
Hajiya ga goron daurin auran jikanki MODIBBO masha allah yaude andaura aure kamar yanda kika umurta yau MODIBBO yazama mijin mata biyu, daddy yafadi yana dan murmushi,"
Masha allah alhamdulilla allah ya muku albarka, allah yasanya alkairi cikin auran, hajiya tafadi cike da murna da farin ciki
Ameen! Suka amsa dukansu goggo rabi kamar ta taka rawa haka takeji aikin dadi, "
Daddy mikewa sukayi sallama sukayi wa hajiya kan zasu wuce nan tashiga sambada musu albarka daga bisani suka sakai suka fice daga parlourn suka shiga mota mai gadi yabude musu geat suka tafi ,
Nisha ne tafito daga part dinsu wacce zama shiru yasa tafito tanufi parlourn hajja mama,
da sallama abakinta ta turo kofar tashigo parlourn hajja mama da goggo rabi suna bisa kujera gabansu dauke da goro tareda sweet
haka kawaii taji gabanta ya dan fadi wanda batasan kuma mai dalilin hakan ba, fiskansu dauke da murmushi Nisha ta kariso ahankali kamar wacce aka zarewa laka tazo tazauna gefe dasu, "
Surkarmu ya akayi yau yan makarnta sunmiki yaji goggo rabi tafadi cike da zolaya kamar yanda tasaba, "
Jinayi zama shirun ba dadi shiyasa na gudunan, nisha tafadi adan shagwabe,
Hhhhh shiyasa nace daga kinga kiwa yadameki kiyiyo nan gaki ga rabi zatai tamiki surutu tana zuba kamar fanfon da yabaci, hajja mama ta fadi tana yar dariya, suma su nisha da goggo rabi dariyan suke rabi tana fadin,"
Hajiya nice suruna kamar fanfon da yabaci tafadi tana harba sweet da tabude takai bakinta, "
Eh mana narasa ina kika koyi surutu haka koda yake shima mijin naki gwanin surutunne, se allah yabaku da wanda magana ma bawani damunsa yayiba hajja mama tafadi, dariya rabi tayi tana fadin"
hajiya kenan nan daga bisani rabi ta dibi sweet din datake sha ta dan kawa nisha,"
Karbi kisha muji dadin hira mubar hajiya da goro, dariya suka sake titsirewa dashi Nisha ba tunanin komai aranta takarbi sweet tasuma shaa suka cigaba da firansu
washe gari da dare bayan sun kammala dinner sunyi firan dare sunkare, kowa yanufi bedroom dinsa ,
ammi na zaune saman sofa zaman jiran dawowan daddy kamar yanda tasaba, tun wunin jiya da tasamu labarin daura auran MODIBBO da nisha haka kawai taji zuciyarta yakasa kwanciya,
Sometimes tana try din number ajmal setaji baya shiga kuma bai taba kiraba tunda yasa kafa ya tafi yauma haka taji tasake gwada kira ko zata dace,
Yaude tayi sa'a wayar tashiga ringing daya zuwa biyu ya dauka, ammi baki har na bari wajan fadin,"
MODIBBO ina kashiga haka phone dinka baya shiga, murya can kasa taji yana kiran sunanta"
Ammi! What happened, ina gd
Gd kuma ? Ammi ta tambaya ,"
Yes ina parlour ajmal yafadi, kashe wayar ammi tayi tanufo down fitowa tayi daga part dinsu tanufi sashin IG
Tana zuwa ta murda handle din kofar tashiga, bakowa a parlourn se dan kayan tarkacen da IG yayi order na kayan ciye ciye da yagama ci yabarsu awajan, direct bedroom dinsa tanufa da tayi tunanin yana can,
🌴🌴 IG AJEEMAL 🌴🌴
Story and writing by oum amreesh
Free book 🤗
Page 34
Ba takai ga karisawa bedroom din ta hangoshi yana kokarin saukowa daga upstairs yana sanye cikin night dresses,
tsagaitawa tayi tana jiran sakkowar shi , yana isowa ya tsaya agaban ammin tasu yana fadin,"
Yadai what happened? Ammi jan hanunsa tayi suka karisa suka zauna bisa kujera daga bisani tasuma fadin'
MODIBBO lapia kuwa ya naganka wani sukuf dakai what's wrong with you? Ammi tafadi tana dan shafo gefen face dinsa, "
No things mekika gani? ya tambaya"
MODIBBO naga kadan fada kalli eyes dinka duk yanayinka ya canza baka da lapia ne? "
I'm feeling fine kawai kajiyace inaso nayi bacci na huta ajmal yafadi akasalance, "
Are you sure bakomai, ammi takuma tambaya tana kallon dan nata cike da kauna da nuna kulawa,
Gyada mata kai yayi alamar eh hakan yasa ammi nunfasawa sannan tace,"
Okay ka kwanta kahuta naga dare yayi sosae but gobe inshallah akwai magana da nakeso muyi very important ammi ta karishe zancen da mikewa"
Okay kawai IG yace yana dan lum lumshe ido , nan ammi tai masa seda safe ta kama hanya tafice daga parlourn,
Yana ganin fitar ammi shima yamike asukwane yanufi bedroom domin kwanciya ya hutawa ransa,
Washe gari da asuba assalatu akunnen ajmal ya sauka amma kasala ta hanashi mutsi balle yamike gaba daya jikinsa amace yake bacci bata ishi idonsa ba,
.
yanajin yanda ake nocking na door but yakasa tashi daddy jin shiru ajmal baiyi mutsiba yasa daddy bude kofar yashigo
Kwance yasami ajmal kamar wani baby ya takure guri guda yana rungume da pillow tsam akirjinsa, lallausan kashinsa duk ya hargitse saman face dinsa, Daddy kada kai yayi yana murmushi cikin natsuwa ya karisa saman bed din ajmal,
Daddy hanu yasa ahankali yajanye pillow da ajmal yarunguma , ajmal jin anrage masa jin dadi anrabashi da tattausan pillow nsa yasashi bude ido ahankali tar yabude ido akan daddy dake zaune tsakiyar katafaran bed dinsa yana sakar masa murmushi,"
Wake up mana yaufa kayi late daddy yafadi , lum lumshe ido IG yashiga yi tareda tashi zaune ya zame daga bed din yanufi toilet dan gabar da alwala yafito
Daddy naganin fitowarsa yamike yayi gaba ajmal ya rufa masa baya jiki amace, suna dawowa daga masallaci IG yakuma kwanciya dan cigaba da baccinsa,
dasafe bayan kammala breakfast dinsu ammi da hajiya, ammi takoma kitchen takuma hado wani zazzafen break din, tajera a try tasuma kokarin fita daga parlourn,"
Ikon allah kekuma ina zakikai wannan breakfast din hka, hajiya ke tambayan ammi, budan bakin ammi keda wuya daddy ya tari maganar dacewa"
MODIBBO zata kaiwa kinsan ya dawo jiya, "
Ikon allah shikuma ba' a sanin tafiyar sa da dawowarsa fadar goggo rabi tana kallon hajiya datayi zuruu, takasa cewa komai,
Murmushi Daddy kawai yake yana kallon hajiya da idonta da suka fito waje, tuni ammi tayi nisa part din ajmal, tana zuwa ta tura kofar tashiga,
azaune tasameshi saman kujera yana sanye cikin shiri mai kyau t shirt and black jeans yayi kya dashi yayi ordern break ya tusa agaba yana kokarin ci,
cikin saurin ammi ta karisa bisa table din dake gaban sa tature abinci da ajmal yayi order ta ajiye nata girkin tana fadin,"
Please as from today bana bukatar sake ganin wannan abincin kantin, kaifa babban mutumne ba girman ka bane cin abincin kanti, ammi tafadi tana kokarin zama kusa dashi yayinda take kokarin zuba masa abinci,"
Nasan rashin mai dafa maka yasa kake sayowa kuma kai nasan bakason yar aiki to ai gwara nina kashe duk wani uzurina nadafa maka kaci because nasan kayi missing girkina kuma nasan yanzu inkaci zakaji dadinsa sosai ,
zazzafan pepper soup tatura masa gabansa gefe ga arish and bugar tareda zazzafan coffee ,
Ajmal ba musu gskyne yayi missing special food na amminsu tun bayan aurensa da heelah , yayi aure but bai taba sanin dan danun girkin matarsaba because ba abunda ta iya na girki, se fita office da kwanciyar bed,
Ko kimtsa daki batayi se idan sun fita office dukansu aturo baba barka ta share musu dakin ta kimtsa duk da bawani baci yakeba, saboda ba cika zama sukayiba,
Ahankali ajmal ya dauki cup din coffee ya kai bakinsa nan ya dauki spoon ya dibi rumun soup din yakai baki yana lum lumshe ido, ammi inde gurin girkine ba a magana,
Taji dadi sosai ganin yanda yasaki jiki yana diban girkin data kawo masa, "
Kayi waya da matar ka kuwa, ? ammi ta tambaya asukwane,"
Meyasa zamuyi waya ajmal ya watsu tambayar sa yayinda yakai bugar bakinsa hankali kwance yake maganar, sosai ammi take bin ajmal da kallon jin amsar da yabata, "
🌴🌴IG AJEEMAL🌴🌴
Story and writing by oum amreesh❤
(Khaleeseart Raeeys)
Free book😍
Page35_36
Ganinayi bata da lapiya tana gdnsu batajin dadin jikinta, tunda allah yayi dawowarka lapiya yakamata kaje gdnsu heelah kaji lapiyarta koba komai zataji dadin hakan"
Okay ajmal yafadi yayinda ya kammala breakfast ya koma yajin gina bayansa da jikin sofa"
Please kadaure kaje kaji lapiyar matarka ammi tafadi tana dafa shoulder dinshi tareda mikewa ta tattare kayan break dinda ta kawo masa tasuma kokarin fita,
bakin door taci karoda aheel dayashigo dagudu wanda yaji labarin dawowan papansa wajansu reedah, cikin watsawa aguje yayi kan papansa cike da murna yana fadin"
Oyoyo papa nayi missing dinka sosae papa kadawo jiya amma baka nemeniba inata kewarka yafadi cike da shagwaba yana nukewa, "
I'm so sorry jiya nadawo nagaji sosai kuma Nasan time din Kayi bacci shiyasa ajmal yafadi yana dan murmushi yayinda yasake hugging din dan nasa cike da kauna yana dan shafa bayanshi,"
Papa mummy bata sona guduwa tayi tabarni, Aunty nisha ita takemin wanka tashiryani har school take rakani abaki take bani abinci kuma tare muke bacci ba kamar mummy ba
Nibazan sake zama kusa da mummy ba Aunty nisha tafi sona nima inasonta kusa da ita zan dinga zama baruwana da mummy.....mukut aheel ya hadiye maganar ganin yanda papanshi yabishi dawani kallo wanda yasa aheel yashiga mis mis da ido,
sam ajmal baya kaunar aheel yadinga kawo masa zancen yarinyar nan da yake kira da Aunty, zame aheel yayi daga jikinsa ya zaunar dashi gefe,
tsam yamike yanufi hanyar bedroom dinshi jima kadan yafito cikin shiri mai kyau farin shadda gezina tsadadda, yasanya hula shigar tayi matukar kawata kyansa duk dacewa shiyamusu kyau basu suka masaba,
aheel naganin papansa yafito cikin shiri da alamar fita zaiyi hakan yasa aheel mikewa daga zaune yayi gun papansa da gudu yakama hand dinsa yana tambayarsa"
Papa where are you going please zan bika yafadi tareda shigewa jikinsa,"
gurin mummy nka zanje, cikeda washe baki aheel yasuma fadin,"
Please zanbika muje tare , "
No bakace baruwanka da mummy ba kafison Auntynka alright kaje gurinta kazauna sena dawo ajmal yafadi tareda zamewa yasuma tafiya seda yafito haryaje jikin mota yajuyu yasauke idonsa kan aheel dake tafe bayanshi yana matsar kwallah
tabbas yaso sutafi tare domin yaga mummynsa amma ya riga ya bata masa rai da surutun dayaitayi dazu rai adan bace ajmal ya kalli aheel ya na fadin"
stop crying and do what I said , nan da nan aheel yafashe da kuka yawatsa dagudu yayi part dinsu ammi, ajmal yana ganin shigar aheel shima yashige mota yamata key mai gadi yabude masa geat yafice,
sannu🌴🌴IG AJEEMAL🌴🌴
Story and writing by oum amreesh❤
Khaleeseart Raeeys
Free book😘
Page37
sannu ahankali yake tafi har allah yasa yadangana ga gdnsu heelah , nan ya danna hon maigadi yafito yaleko dan ganin wake danna hon ganin ajmal cikin kyakykyawan motarshi yasa mai gadi yashiga rawanjiki tareda washe baki yabude masa get yashigo,
nan ajmal yadangana parking space yayi parking yafito, mai gadi tamkar zai masa sujjada wajan gaisuwa,"
Yallabai sannu dazuwa ,"
Yauwa sannu ya aikin "
Alhamdulillah bari nasanarwa gdn zuwanka mai gadi yafadi , gyada kai ajmal akwai yayi nan mai gadi yasuma sauri haryana tuntube, Yana isa parlourn ya suma sallama yanajin an amsa masa yakutsa kai yashiga,
hajiya balkisu mahaifiyar nabilah nazaune bisa kujera tana kallon tv remote bisa hand dinta mai gadi yazube saman carpet yana fadin,"
Hajiya sannu da hutawa , cike da sakin fiska hajia balkisu ta amasa masa da yauwa sannude ya akayi,"
baban aheel ne yazo yana waje , gyara zama hajia balkisu tayi tana fadin,"
Haba kaikuwa shine zaka barshi awaje maza tashi kamasa iso yashigo , cikin sauri mai gadi yafita yanufi inda ajmal yake jikin motarsa yana danna wayarsa,"
Yallaboi waika karisu ciki! Ajmal dagowa yayi yakalli mai gadi batareda yace komaiba mai gadi nakokarin komawa bakin aikinsa seji yayi ajmal ya jefa masa kudi cikin aljuhunsa , cikin murna da farin cikin mai gadi ya kalli ajmal yana fadin,"
Nagode duk da dama ba yau yasaba masa Kyautar kudiba matukar yazo gdn nan seya masa alkhairi, ajmal bai saurari godiyar da mai gadi yake masaba ya kunna kai cikin parlourn bakinsa dauke da sallama ,
Mikewa hajia balki tayi ta tareshi cikin farinciki , karisuwa yayi yadurkusa yasuma gaisheta seda suka gaisa daga bisani ya gyara zama bisa kujera itakuwa hajia balki tanufi kitchen domin hadu masa abubuwan tabawa , seda hajiya balki tagama hadu abunsha dana tabawa takalli hajjo mai aikinsu wacce take tsaka da aiki, tace,"
Hajjo dan dakata da aikin nan haka ki haura sama kiyiwa umman heelah magana heelah tayi bako mijinta papan aheel yazo cikin sanyin murya mai aikin tace to ,
Tare suka fito daga kitchen din hajjo tahaura sama dan isar da sako itako hajia balki takarisa da inda ajmal yake ta dere masa try din da takawo masa bisa tablet tana fadin,"
Bismillah kafara da wannan kafin heelah tasakko na aiki hajjo ta kirawota, gyada mata kai yayi yana fadin,"
Bakomai tareda cigaba da danna wayarsa,
hajia jumana tana kwance kata faran gadonta tana latsa wayarta jin nocking bakin door dinta yasa mikewa tazauna cikin daga murya tasuma fadin"
Wayene kam yake kokarin damuna haka da nocking, cikin rawar murya hajjo tace"
Nice dama hajiyace tace tanazo nasanar miki baban aheel ne yazo hajjo tafadi daga Bakin door batareda tashigoba, jin haka yasa mom din heelah tazamo daga bed tanufo kofar tareda budewa, seda takarewa hajjo kallo ta tabe baki sannan tace,"
Anji keje anazuwa , cikin hanzari hajjo tajuya da sauri ta sauka Kasa, wani murmushi mom din heelah tasaki kafin ta dangana ga bedroom din heelah , azaune tasamu heelah gaban mirror jikinta sanye da towel tana latsa wayarta tana zuba uban murmushi, da alamar bata ankara da shigowar mom cikin bedroom dintaba,
ahanzarce mom din heelah takarisa kusa da heelah tareda fizge wayar hanunta tana fadin"
yanxuke tsabar sha shanci wanka kikayi but kinkasa sanya sitira ajikinki kinzau kinata chat din banza to kitashi kinyi bako, cikin tura baki heelah tace"
Mom bako kuma? nibawanda nagaiyata koyace zaizo gurina"
To papan aheel ne yazo dan gdnku sekitashi kiyi haraman sa kaya, tsulum heelah tamike dadi kamar me papan aheel yazo cikin hanzari tayi wardrobe tasuma lalubar kaya, "
kiyi shiri mai kyau wanda zaidau hankali karki manta kisanya humranda kawata habiba tabani nakawo miki kishafa duk wani lungu da sako dan humran na dakyau zaki bani labari, mom tafadi hartajuya zata fice nan tajuyu takalli heelah tana fadin,"
Karfa kimanta bakida lapia karki zage dayawa,"
Oh mom nasani kije kawai heelah tafadi cikeda kosawa, tobari naje kihanzarta maza mom tana gama fadin haka tajuya tafiata daga bedroom din tanufi downstairs,
Ahankali mom din heelah take saukowa harta kariso cikin parlourn murmushi dauke afiskarta but ganin hajia balki yasa ta murtuke face tamkar ba itake murmushi dazuba,
karisuwa tayi tazauna ko kallon inda hajia balki take bata kalla ba, ajmal dan zamewa yayi daga kujeran yasuma gaisheta, seda suka gaisa yake tambayar ya jikin heelah
nan tashaida masa jiki da sauki amma saukin ba haushe , because indare yayinema zazzabi ke rufeta baya mata da wasa,
hajia balki duk tanajin karyanda mom din heelah ke shirgawa because ita tasan bawani rashin lapiya tunda rashin lapiyar baya hanta fita yawo inda takeso hmm allah ya kyauta tafadi cikin zuciyarta, yayinda tazora ido da kunnuwa tana sauraron karairayin mom din heelah ba kunya ba tsoron allah tsabar son zuciya ,
shigowar heelah parlourn yasa mom ta tsagaita da surutun da take shikanshi sauraronta yake bawai hankalinsa yana kanta bane dan ko cewa akayi ya maimaita abunda take fadi yayi karya ya iya maimaitawa,
Karisawa heelah tayi tazauna tana rarraba ido atsakani,"
Yauwa kin kariso tundazu kinbar mutum yanata jira komai kike adakin oho mom tafadi tana kallon, itade heelah shiru tayi batace komaiba domin sun hanata rawan gaban hantsi ganin haka yasa mom tamike tana fadin,"
Uhm bari mutashi mubaku waje , malama semubawa ma aurata waje zasu gana mom tafadi tana kallon hajia balki tana wani harare harare, tabe baki umman nabilah tayi daga bisani tamike tanufi kitchen, domin yau itace da office ganin haka yasa mom din heelah itama tamike tahaura sama,
heelah naganin sun watse daga parlourn hakan yabata daman mikewa daga inda take tanufi sofan da ajmal yake zaune kansa kasa yana latsa waya,
sam bai ankaraba sejin heelah yayi bisa cinyarshi nan ya dago suka hada eyes nan tasakar masa murmushi tareda yin hugging dinshi,
kokarin tureta daga jikinsa yasoyi but yakasa because wani fitinanne turare da tasanya wanda yahanashi yin hakan ahankali yaji tana rada masa akunne,"
i miss you so much my lovely kayi matukar ladaftar da zuciyata na tsawan wasu kwanaki tana fadin haka tayiyu kasa da lips dinta tana kokarin kissing dinshi, cikin hanzari taji ajmal yatureta gefe tareda mikewa tsaye yana kallonta, yana fadin"
Sorry sauri nake akwa inda nakeda bukatan zuwa banason bata time, lapiyarki nazo naji bye , yana fadin haka yajuya yafice nan yashiga motarsa mai gadi naganin fitowarsa yashiga mota yabude masa get tareda daga masa hanu ajmal yafice,
heelah shiru tayi da mamakin tureta dayayi dukda ba sabon abu bane wani lokacin haka yake yaita tureta kamar ba namijiba wani time din kuma yanajinta tana kissing dinshi tareda tabashi yanda takeso bazaice mata kalaba wani lokacin ma har biyeta yake, to kode turarenda tasane bai masaba, inba hakaba kodan kewarsa da tayi yakamata ya saurareta,
Nan heelah tashiga shun shuna humran jikinta ko zataji wani aibu amma sam bawata aibu maybe halinne ya motsa kawai
🌴🌴IG AJEEMAL🌴🌴
Story by oum amreesh❤
(Khaleeseart Raeeys)
Page38
Mikewa tayi fiska ba annuri tanufi upstairs Tana surutai,
______Nisha____________
karfe 9:30 nadare bayan kammala dinner kamar kullum kowa ya halarci turakarsa, Nisha na kwance bisa gado Tana kallo cikin wayarta se aheel dake kwance gefenta daya gama rikecinsa har bacci ya daukeshi duk da bacci yaci idonta sosai amma takasa ajiye kallon da take takwanta ,
gefenta reeda ce zaune Tana amsa waya da alamar habibintane akan layi , se fadeelah dake baje saman carpet tana karatun exam dan tuni suka suma jarabawa da alamar tayi nisa cikin karatun, kowanne da aikin da yakeyi
sannu ahankali har bacci barawo yayi nasaran cinye idanuwansu fadeela na kasa tana karatu bacci ya dinke idonta kowacce bacci mai nauyi tashiga yi cikin kwanciyar hankali, guraren 11 aheel yasuma motsawa yana lalubar Nisha dake gefensa yana fadin "
papa, jin surutun da aheel keyi cikin bacci yasa nisha mutsu mutsun bude idonta ahankali, cikin muryan bacci nisha tace "
Aheel what happened fitsari zakayine domin kuwa tasanshi wani time tashi yake yace mata zaiyi fitsari,"
Uhm uhm papana kikaini gurinshi please , Nisha tatsinci muryan aheel yana fadin haka cikin sigan kuka , tarr nisha tabude ido ta tashi zaune tareda kunna wutar gefenta takai hanu ta lalubi wayarta tashiga duba time 11 yawuce , dan waro ido tayi tareda sake kai hanu tadago aheel tajanyushi jikinta tana fadin "
Sorry aheel bazan iya kaika gun papankaba dare yayi sosai ina tsoron fita kar dodo yakamamu gobe zan kaika dasafe kaji! nisha tafadi cikin sigan rarrashi tana dan bubbuga bayanshi, ga mamakinta yaro yasaki kuka mai sauti wanda yanya reeda dake gefensu motsawa ta gyara kwanciya batareda tabude idoba balle tasan rigimar da aheel keyi ,
inba kai yaron nan tayi gurin mahai finshiba da alamar se yarikita kowa nacikin gdn ya ta shesu dan aheel inyatashi rigimarsa baya jin lallashi, tsam nisha tamike tsaye jikinta sanye da gown ta bacci ahanzarce tadauki mayafinta tareda kai hanu tasun kuci aheel tarabashi bisa gafadanta sukayi yuyo parlour
Ahankali take tafiya tamkar wata barauniya kirjinta se bugawa yake tsabar tsoro , tunda suka fitu bakinta keta kwararu addu'a duk addu' ar datazu bakinta yitake tana zare idanuwa ,
Kowa yayi bacci hatta securitys din dake zagaye gdn sunyi bacci gari yayi shiru , seda suka karisa part din tasa hanu tamurda handle din door din taji abude yake hakan yabata daman bude kofar suka shiga ,
Parlour shiru yake nan tasauke aheel tana fadin,"
To gashi nakawoka kakarisa bedroom din papan naka nibari natafi ,
nanfa aheel yanuke yakawo kuka yasaka yana kiran sunan papa shisam sede takaishi bedroom din papansa
duk wannan bidirin da aheel keyi ajmal na kallonsu tasama domin yana parlourn sama saman sofa yana danna system jin motsin shigowarsu da jin sautin aheel yasashi tasowa ya tsaya yana kallonsu,
sanya hanu yayi cikin aljuhun jallabiyarsa yanufi downstairs ahankali yake tafiyan jin motsin ansakkowa aheel da nisha yasa hankalisu ya karkato zuwaga reshi aheel ganin papansa da yayi baijira kariso warsaba yajanye hand dinshi daga na Nisha yayi gurin mahaifinshi da gudu yana washe baki ya fada jikinsa,
zuro Nisha tayi yayinda tabi bayan aheel dakallo yayinda ya karisa ga papansa , kamar ce mata akayi ta tsaya karta tafi haka takebin papan aheel da kallo gwanin shaawa kullum kyansa sake karuwa yake wato ko namiji dan uwansa inya kalleshi dole yasake daga ido ya kalleshi biyu zuwa uku balle kuma macce bataki tasashi agaba taita kallo kamar TV ba
shi kanshi ajmal kallon yarinyar yashigayi da mamaki uwar maita tsaya jira datakasa tafiya se kallonshi take kamar wata mayya duk da yasan ba abun mamaki bane bazai wuce kyawu na face din da Allah yamishi take dubaba , sauda dama inyafita ko ina yashiga andinga kallonsa anasakewa shiyasa yake yawan amfani da face mask dukda wani lokacin yana damunsa saboda matsalar numfashi (asthma)"
Aunty bye seda safe aheel yafadi yana daguwa Nisha hand , seyanzu ahankalin nisha ya dawo jikinta, dakyar ta kirkiro murmushi tare da dagawa aheel hand tajuya jiki asanyaye sidib! sidib!! tafice ,
Ajmal kallon aheel yayi Wanda ya manne masa ajiki ya dagusa tareda azasa bisa shoulder dinsa yakarisa dashi bedroom ya kwantar dashi, yana fadin"
I'm coming , yana fadin haka yajuya yafice daga bedroom din yanufi inda system dinsa yake yakasheta yakuma bedroom gurin aheel yakwanta daga bisani yakalli aheel yana fadin, "
sleep good night lumshe ido aheel yayi yana fadin, "
Good nights papa, nan ajmal ya kashe musu wuta tareda yajanyo blanket yarufesu, bajimawa bacci ya daukeso ,
haka itama Nisha tunda tafito daga part dinsu aheel take ta banka sauri tana waige waige harta karisa sashinsu ta isa bedroom dinsu tanemigu ta kwanta tanamaida ajiyar zuciya , idonta yabude gaba daya jitayi bacci ya kauracewa idonta haka taita juyi daker tasamu baccin ya dauketa ,
Washe gari da misalin 8am ajmal zaune bisa kujera yana sanyawa aheel school shoes ya gama shiryar yashi tsaf domin kai aheel makaranta , murda kofarda akayi ana kokarin shigowa yasa aheel da papanshi suka maida ankalinsu ga kofar
Washe baki aheel yayi tareda zurawa da gudu yayi gunta ya rungumeta yana fadin, "
Good morning murmushi Nisha yayi kana tace ,"
Morning my little baby katashi lapia ?
Lapia qlu aunty aheel yafadi yana murmushi , daga ido Nisha tayi takalli papan aheel time din harya mike yana kokarin barin gurin , muryan Nisha yaji tana daga masa gaisuwa,"
Ina kwana antashi lapia, kamar bazai amsaba sekuma taji yace,"
Lapia! yacigaba da tafiyarsa yabar gurin tabe baki Nisha tayi kafin takalli aheel tareda mika masa school back dinsa data tahu masa dashi , nan aheel ya karba yasanya jakan bisa bayansa sannan ta mika masa lunching box dinsa tana fadin "
gashi special food nayi maka zakaji dadinta sosai, cike da zumudi aheel ya karba yana fadin ,"
Thanks
banda wasa a school yayin karatu , gyada mata kai yayi yana washe baki kamar gonar auduga , suna cikin haka ajmal yafito hand dinsa dauke da key din mota tareda phone dinshi , Nisha naganin haka tasuma kokarin barin parlour, "
Aunty yau bazaki rakani school bane , aheel yafadi yana kallon Nisha da harta bude kofa zatafita , ahanzarce tajuyo tana fadin,"
Sewani lokacin , kafin tafice dasauri tabar parlour, Sam. aheel baiji dadiba yau Auntynsa bazata rakashi school ba , kamar yanda tasaba yan kwanaki , tabbas itama taso rakashi kamar yanda tasaba dan bata gajiya da kallon school dinsu aheel, makarantar burgeta take gwanin shaawa, especially wajan wasanninsu , to amma tareda papanshi zasuje bazaiyiyo tabisuba,
Nan aheel da papansa suka nufi mota suka shiga mai gadi yabude get ajmal yaja mota suka tafi, ,
Nisha na karsawa cikin parlour taci karo da ammi cikin shirinta nazuwa office da alamar cikin sauri take da sauri Nisha ta dagawa ammi gaisuwa,"
barka da safiya ammi antashi lapai, cikin hanzari ammi ta amsa da
lapia qlu, dama bedroom dinku zanje tasuke , aikin lada zansaki idan bakida uzuri nayiwa ajmal breakfast nasa barka tashiryamin ta ajiye a dining table, so kuma ina sauri akwai wani azuri da yataso min office kidauki breakfast dinshi kikai masa part dinsa ,
shiru Nisha tadanyi kafin tagyada kai tana murmushin da baikai zuciba tashiga fadin ,"
Bakomai zan kai mashi sekin dawowa , yauwa kuma kidan tattare masa bedroom din kisan abunka da gwauro ba mace kusa dashi nasan ba abunda zai tabuka, ammi tafadi tana murmushi yayinda take kallon baby face din Nisha, "
To Nisha tafadi ahankali, ammi shafa gefen face din Nisha tayi tana murmushi tana fadin "
Allah yamiki albarka bari naje , murmushi Nisha tasake wanda yasanya dimpul dinta lutsawa because ba karmin dadi tajiba jin albarka da ammi ta Samata , daga haka sukayi sallama da ammi tawuce tafita, ita kuwa nisha tanufi bedroom dinsu,
tana shiga bedroom din tasamu su fareeda sun shirya tsaf zasu wuce school suma because karfe 9 zasushiga paper tuni sunyi breakfast dinsu shape shape dukayiwa nisha sallama suma suka fice, ,
Kwanciya Nisha tayi idanuwanta na kallonsama ta tsunduma kogin tunani amma gani tayi zama cikin tunanin ba amfanin da zai mata zaifi kyau tamike taje tayi abunda ammi tasata kafin yadawo ya taddata cikin sashinsa baisan dashigartaba yazo yanemi lika mata wani sharrin, gwara tayi tagama baisan tashigaba,
mikewa tayi ahankali tanufi parlour tareda wucewa dining table barka tagama shirya komai dan haka ta kinkimi try din abinci tafice tanufi sashin papan aheel, tana shiga parlourn tanufi inda dining area ta dire tr din abincin , sannan tasuma waige waige da tunanin inane bedroom din nasa yake , kallon parlourn tayi bawani dauda yayiba kaikace ba masu rayuwama aciki , sede parlour yana dan bukatan atattareshi abunda yake ba daidaiba amaidashi mazauninsa ,
nan tasuma kokarin haurawa sama inda taga yasakko jiya , seda ta karisa haurawa taci karo da kofar wani bedroom nan tabude tashiga da tunanin shine bedroom dinsa, "
Wow abunda nisha tafurta ahankali yayinda take karewa dakin kallo , bedroom din yayi kyau sosai , komai naciki white and maroon ne , dakin yayi matukar yimata kyau, ga kaya na alfarma komai qlu ba abunda yasamu dakin , dib annashuwar dake face din Nisha yakau saka makon idanunta daya kai wajan mirror ta hangi hoton heelah arantabe agurin ahankali takarisa gaban wajan tadauki hoton tana kallah , dasauri ta ajiye hoton tafito daga bedroom din da alamar dakin matarsace banashiba ,
Gefen damanta da takarisa wani katafaren parlour ne ya hadu ya fasaltu again aciki akwai kofofin bedroom guda biyu dasuke kallon junasu white and pik color dan haka takarisa daya daga ciki inda take tuna nin cikinsu baza arasa bedroom dinsaba,
murda handle tayi tashiga ,"
Ya salam aljanar duniya wannande ko ba afada mataba tasan bedroom dinsa dan bedroom din duk kamshin turarensa kakeji ya gauraye ko ina, komai yaji yayi das dashi alhamdulilah masha Allah kawai za ace dan tsayawa fadin irin kyan dakin bata time ne , komai nadakin back and white color ne because ajmal yanason wadannan color's din su hade guri guda,
ahankali Nisha ke karisawa ciki tana juye juye kamar dan kauye yashigo birni, yanayin tsarin da kwalliyar da akayiwa dakin ba karamin kawata mai kallo zaiyiba , sede dakin yana bukatan gyara because komai nacikinsa ya cukurkude,
Kamadaga bedsheets pillows dindake watse kasa , saman coffee table shima kaca kaca , haka saman mirror dinsa duk ya hargitse , nan Nisha tashiga fara aikinta gadan gadan , duk ta dauke cups dindake saman table din da duk shirgin dake gun tafita dasu kowanne takaishi inda ya dace , koda tanufo kitchen da nufin kai cup's da plate din dayayi amfani dasu , seta tarar da sauran shirgin wanke wanke da ya hada duk da ammi jiya bayan fitarshi tasa baba barka takwaso duk wani shirgin wanke wanke adauraye masa amaida masa "
Hmm lallaifa da aiki nisha tafadi afili kafin tasunce mayafin kanta tadaure jikin kugunta tasuma wanke duk wani abunda akayi amfani dashi tamaidashi mazauninshi,
Atakaice de Nisha yau ta mutsa jiki duminko ta aikato balaifi, tagyara koamai ta kimtsa komai komai yayi tas dashi , nan tafito parlourn sama ta kishingida tana hutawa dan takaji sosai, sassanyar iskar Ac haka yake ratsa jikinta tana wani lumshe ido tana budewa wan dadi se ratsata yake, gaba daya jikinta seya mutu harwani bacci tasumaji,
Nanfa tasake baki tasuma gyangyadawa tanayi tana bude ido , jin hon ana kiciniyar bude get yasa tabude ido da sauri tamike tanufi window, tana daga labule idonta ya hango motar ajmal nashigowa haraban gdn ,
cikin hanzari tanufi downstair sekuma ta tuna da phone dinta dake ajiye saman mirror a bedroom din ajmal marmaza takuma dakin tasun kuci wayarta da sauri har tana tuntube tanufi kasa gudu gudu sauri sauri haka take sakkowa , shikuwa ajmal tuni yakarisu kofar parlour ya murda handle zaishigo, kankace me kafar Nisha daya yashiga cikin daya kafarta ya harde tafadi daga tsakiyar stairs nan tasa ihu arazane , ajmal tsurawa wajanda yaji ihu ido yayi seganin Nisha yayi tana zamuwa daga kwance tana ihu seda takariso harkasa ajmal yashiga binta da kallo yana kuma kallon sama inda tazamu da mamakin mai yakaita saman
🌴🌴IG AJEEMAL🌴🌴
💦Story and writing by oum amreesh💦
DAGA ALKALAMIN✍🏼
🦚Khaleeseart Raeeys🦚
_________________________
FREE BOOK
Ya Allah yanda nafara rubuta wannan littafin kasa naga karshensa lapia, kabani ikon rubuta abunda zai ilimantar ya nishadantar ameen********************page 39
Ahankali Nisha ta Mike tana mis mis da ido tana dan cizon lips din ta kamar maishirin kuka, because jikinta yabugu sosai, yafinta data daure saman waist dinta tasunce tamaidashi saman kanta tasuma kokarin takawa,
slowly take dingisa kafar tana tahowa shide ajmal haryanzu kallonta yake hartakariso gefensa ta tsaya yayinda tasun kuyar dakai kasa baki nabari tasuma fadin, "
Uhm ammice tace nazo nakawo maka breakfast sena gyara maka bedroom dinka idan da wani abunma kafadi zanma, jin shiru bai amsataba yasa ta daga ido ta kalleshi still idonsa nakanta but baice komai, ganin haka yasa ta dan hadiye miyau tazame jiki tasuma kokarin barin parlourn, "
Hee you! cak Nisha ta dakata da tafiyar da take jin muryan ajmal akaushashe yana magana nan tajiyu tana kallonsa suna fiskantar juna, daga inda yake yatako yakariso kusa da inda take tsaye, seda yagama kallonta tsaf sannan yace,"
As from now karna sake ganin kafarki cikin side dina if not zan karya wadannan sirarun kafar takin , I hope kinfahimci point dina , ajmal yafadi yana kallon Nisha da hawaye suka wanke face din kanta asunkuye tana sauraron abunda yake fadi,
Oh allah wannan wace iriyan bakin haline ga mutumin nan duk wahalar da tasha wajan gyara masa muhalli da maganganun da zaisaka mata dashi kenan gaskiya tayi danasani duk da ba ita tasa kantaba ammine tasata kuma dan ita tayi ,
Kikoma kidauki breakfast dinda kika shigo dashi kifitarmin daga side bana bukata, ajmal yakuma fadi karo na biyu, share hawaye Nisha tayi tareda takawa ta isa zuwaga dining table inda ta ajiye abincin da tashigo dashi tasa hanu ta dauki tr din tanufi hanyar fita, ajmal yana kallonta yanda take taka kafar dakyar hartafice tabar side din daga bisani ajmal yaja wani siririn tsaki yacilla phone dinsa tareda key din motarsa saman sofa yanufi upstairs,
Tunda yashiga bedroom din yayaba da gyaranda akayiwa dakin domin ko bakomai bedroom din yayi bakon gyara komai yashiryu yayitas dashi komai yazauna inda yadace gyanin kyau gwani burgewa , dan zamewa ajmal yayi yazauna bakin bed yana maida ajiyar zuciya, yadade ahaka natsawun wasu mintuna daga bisani yashiga sabule kayan jikinsa wanda yarage dagashi sedan short yanufi toilet domin wanke jikinsa,
ya dade yana wankar daga bisani yafito ya kimtsa jikinshi yashirya cikin yanayi mai kyau da daukan hankali yasanya turaren sannan mai kamshi dadi mai wuyar barin jiki yanufo downstairs,
inda ya cilla key tare da phone dinsa yanufa wanda tunkan yakariso wajan yakejin karan ringing phone dinsa yana tashi alamar kira but kafin yakariso takatse,
Nan yashiga duba wayar yaci karo da miss call din doctor fu' ad kaca kaca ahanzarce yafice daga parlourn yafito yanufi motarsa yashiga mai gadi yabude masa gate yafice,
aban garan nisha kuwa tunda tabar side din IG tanufi sashinsu idonta sefidda kwallah yake , tana shiga parlour tanufi kitchen tare da ajiye tr din abincin bisa table din kitchen din tafice da sauri tana shashshekar kuka, barka dake tsaka da aiki jin motsin shigowar nisha ta ajiye tr tafita tana kuka hakan yasa barka ta tsagaita da abunda take tabi bayan nisha cikin bedroom din su,
koda barka tashi akwance tasamu nisha tayi rubda ciki tanitsa kanta cikin pillow kuka mara sauti ahankali barka ta matsa kusa da bed din tana fadin,"
yar nan lapia kuwa kike kuka? dib Nisha ta tsaya dakukan jin muryan barka tana tambayarta, mikewa nisha tayi daga kwanciyar datayi tazauna tanamai share hawaye tana fadin,"
Ba komai, "
Aa yarinya yazakice ba komai bayan gashi kuka nazo natadda kinayi , wani abun aka miki, kinzo kin ajiye tr kintafi kina kuka , kuma nasan daga sashin ajmal kike wani abun ne yafaru,
barka takuma tambaya tana kallon baby face din Nisha dayayi jawur bawani bata time nisha tashiga labartawa barka abunda ya wakana takarishe zancen da kuka tana fadin,"
sam papan aheel bayida ahali irin na yayan gdn nan halinsa ya banbanta danasu , kowa dake cikin gdn nan ya karbeni hanu biyu bawanda ya kyamaceni, amma shikuma gaba bayason ganina daga shi har matarshi ko alakata da dansa baso yakeba kwata kwata bayason narabeshi bansan dalili ba,
Nikuma tunda Allah yayi zuwana gdn nan Allah ya hada jinina da na dansa , Allah yadauramin son da kaunar aheel cikin zuciyata jinake tamkar ciki daya muka fito , ko wuni nayi bansa aheel aidonaba banajin dadi, gashi yau yamin iyaka da inda suke balle nasake haduwa dashi, waishin wani irin hali gareshi haka? Nisha tafadi gamida sunkuyar dakai kasa tanamai matsa kwallan da suka cika idonta,
dan numfasawa barka tayi tareda matsowa kusa da nisha tadafo shoulder dinta tana fadin,"
kiyi hakuri yar nan dama ita rayuwa haka take akwai mutane iri da kallah , amma sam wannan abunda yafaru ya dameki ko yadaga miki hankali , ajmal ahaka yake bayida saurin sabo da mutum lokaci daya , ammafa mutumne maisaukin kai, sede kuma kafin a fahimceshi abunda wuya
nima kaina dakike ganin nake aiki agdn nan ankai ruwa rana kafin ajmal yasuma sabawa dani , kingani nan yanzu kusan shekara goma nake nema agdn nan ina aiki ,
Tun bayan dawowarsu ammi Nigeria nasoma aiki agdn dominko da sunacan yankin turawa seda gabaya suka dawo Nigeria har nasamu daman zuwa aikatau dani da yata hajjo mukazo gdn nan neman aiki wata hajiace takawomu gdn nan , sede ita hajjo ba tare mukeba tanacan gdnsu heelah acan tasamu rabon nata aikin , nikuma nake aiki anan , tunda nafara aiki agdn nan bantaba samun matsala da waniba seta kan ajmal domin kuwa duk abunda nadafo na kawo daga yakalli yanayin abincin ko one spoon bazaiyiba seya tashi yabar gurin bazaiciba , idan ammi ta tambayeshi dalili seyace akoshe yake yaci abinci awaje,
kinsan dalili dayasa bayaci , barka tafadi tana kallon nisha , girgiza kai nisha tayi alamar "
Aa
saboda suba yan gargajiya bane bai iya cin abincin gargajiyaba, yafisabawa da abincinsu can yankin turawa saka makon duk yarintarsu da girmansu acan sukayi bai saba da abincinmu Nigeria ba nikuma shina iya kuma hajja mama ita take da bukatan abincin gargajiya, kuma shi take bukata adingayi sbd atunaninta gabaki daya jikokinta susaba da gargajiya al'adansu na gargajiya yadawo susanshi yabi jikinsu
yaran tunbasa sabawa da yanayin abincin harya zama musu jiki suka suma jin dadinsa , amma shi mutumin ko gwadaci bayayi sede yayi order daga waje , sam ammi batajin dadin hakan , dan haka tashiga bina kitchen tana nunamin yanda ake sarrafa wasu nau ikan abincinsu nacan dakuma abunda shalelen dan nata keso dakuma abubunda yafi bukata, dukda wasu nau ikan abincin bawani wahala ne dasuba
Tofa nanne akasamu yake zama yadanci nan dinma dayasan dasa hanuna wajan sarrafa abincin ba lallaine yaciba amma ganin ammice tashirya masa to nanne zaisamu yasawa abincin albarka,
hmm inzamu kwana muwuni ina labarta miki rayuwa irin na ajmal bazai kareba , yanada tsarabe tsarebe tamakar jariri , to daga bayade Allah yatakaita wahala domin ansanya ranar aurensu da heelah duk da bayida ra'ayin hakan hajja mama ita tashirya komai, duba dayanda heelah ta kwallafa ranta kansa tanuna tanasonshi , bada wani bata lokaciba hajja mm tasa aka shirya musu biki
tode kobayan auran bata sauya zaniba domin kuwa heelah sangartacciyace malalaciya ba abunda ta iya sezuwa office yau morning gobe nights ba uwar da take tabukawa ansha kawo mata yan aiki dazasu dinga taiYikawa sbd ita ko girkinnan nazamani bata iyaba , amma saboda bakin hali da mugun kishi irin nata haka take koransu haka yasa hajja mama tace adakata dakawo masu aiki hakanan azuba mata ido akwai rayuwarsuce bata waniba,
nitunda nake bantaba ganin rayuwar aure irin tasuba kowa cikinsu aikin gabasa yake kamar ba maurataba niwani lokacin ma har tunani nake ko taya akasamu cikin aheel oho dan naga kowanne su bayi da lokacin kansa balle agansu atare dan soyayyan nan tsakani mata da miji duk babu , uhm to koni meye nawa danazage naketa miki surutu haka, barka tafadi tareda mikewa tana fadin ,"
Yi hakuri na ajiyeki inata miki zuba nasan kuma ko breakfast bakiyiba yakamata muje kiyi breakfast, dan numfasawa nisha tayi tana fadin, "
Uhm nigaba daya koyunwarma banaji ,"
Aa yar nan ya kamata kisamu Abu kisawa cikinki ko kadanne dan haka biyoni muje nasama miki abun tabawa barka tafadi tareda shigewa gaba bamusu nisha tarufa matabaya,
nisha daga dining tazauna tana jiran barka da tashiga kitchen dan hadu mata breakfast, bawani jimawa tazo ta direwa nisha plate din chips da kwai tareda sandwich gefe ga sassanyar cornflake abunda nisha keso kenan , haka tazauna taci sosai batareda wani damuwaba tana kammalawa dakanta ta tattare kayan da tayi amfani dashi tayi kitchen, nan tasuma taya barka da wasu aikace aikacen duk da baba barka tanuna mata bata bukatar hakan , amma sam nisha taki hade takyaleta suka cigaba da aikin tare , sunayi barka na mata hira gamida bata wasu labaruka dasuka shafi rayuwan gdn da kuma halayen mutanen gdn da yanda komai yake tafiya , wunin ranar bakaramin dadi yayiwa nisha ba kasan cewarsu tareda barka tana mata fira duk setaji damuwarta yakau ahaka tawuni cikin alwala
Da dare kamar kullum bayan kammala dinner family din sun zauna sunsha fira abunsu anyi nishadi yanda yakamata wannan karun harda Daddy domin kuwa yau dawuri yadawo baiyi dare kamar yanda yasaba , ansha hira mai tsayi segurin 10 kowa yamike sukayiwa junansu seda safe daga bisani kowannensu ya hallarci makwancinsa, yarage daga ammi se Daddy, "
Tomudin memuke jira yakamata muje mukwanta dare yayi Daddy yafadi, dan kallonshi ammi tayi tana fadin "
kajeka kwanta zanbiyoka anjima,"
kedin mezaki zaunayi a parlourn, dan sunnar dakai kasa ammi tayi tana fadin, "
MODIBBO nakejira, na ajiye masa dinner dinsa , wani kallo Daddy yabi ammi dashi yana fadin,"
Ninarasa meke damunki , MODIBBO fa bayaro karami bane yagirma yanzu mata biyu garesa ga yaro shima ya haifa banga dalilin da zaki dinga takura kankiba ,"
Ammade karka manta daga MODIBBO har dan nasa ba macen datake kula dasu matar tashima kana ganin abunda bai taka kara yakaryaba tasa kafa tabar gdn ta nufi gdnsu tafake da zancen rashin lapia dukda dama ko tana nandinma ba abunda take tarewa , ita kuma barka aiyuka sun mata yawa yakamata atausaya mata taji da namu aikin ga shekaru sunja bai kamata taita zarya akanshiba
to yaushe zan tsaya amatsayina na uwa nazuba masa ido seyafito waje sannan yaci ammi tafadi cikin damuwa , Daddy tasowa yayi daga inda yake yadawo kujeranda take yazauna tareda dafa shoulder dinta yana fadin, "
To inbandake yanzufa matansa biyune mezai hana kisa nisha tadau nauyin wannan koba komai tahaka yauda gobe sesu saba har Allah yanuna musu randa zasu fahimci akwai alaka atsakaninsu ni inaga hakan kamar zaifi,"
Hmm kamar kana manta miskilanci irin nadanka , nayi kokarin gwada hakan amma abun baiyi kyauba domin barka tasameni bayan dawowana tafadamin abunda yafaru bayan tura nisha danayi side dinshi nan ammi ta karntuwa Daddy abunda barka tafadi mata tsakanin ajmal da nisha turatan da tayi side shi domin kaimasa breakfast takuma gyara masa bedroom
shiru Daddy yayi yana jinjina lamarin dan yasan halin dansa zai aikata , hmm allah ya kyauta abunda Daddy ya iya fadi kenan ammade bai kyautaba ya kamata kiyi masa magana bai kamata yatakura yar mutuneba dan tazo gdnsu nizanje nakwanta sekin shigo Daddy yafadi tareda haurawa sama yabar ammi agun azaune tana jiran dawowar ajmal,
Ammi ta dade a parlourn tana kaiwa da komuwa gami da leka window dan ganin shigowar ajmal but amma shiru harta gaji dajira har 11 naneman gautawa, han yatabbatar mata balle dawowarsa yanzu hakan yabata daman haurawa sama tanufi makwancinsu koda tashiga bedroom dinsu tuni tasamu Daddy yayi baccinsa , nan itama tasamu daman kimtsawa ta kwanta ,
washe gari dasafe ammi batayi kasa agwiwaba bayan ta sallami Daddy kamar yanda tasaba itama tashirya tanufo dining inda tasa barka tashirya mata breakfast din ajmal nan ta tarar dasu reeda suna karyawa yayinda nisha takecan bedroom tana sheka bacci suna ganin ammi suka shiga daga mata gaisuwa nan ta amsa tareda kai hanu ta dauki tray din abincin tafita tanufi bedroom din ajmal,
tanashiga parlourn shiru ba motsin kuwa aciki dan haka takarisa dining table ta ajiye tray din abincin saman table din tanufi upstairs, direct bedroom din ajmal tanufa ta tura kofar sallama dauke abakinta takarisa shigowa nan dinma de shiru baya bedroom din se motsin ruwa dataji daga toilet wanda hakan yabata tabbacin yana toilet, hakan yabata daman zama saman sofa dake dakin tana jiran fitowarsa ,
ba dadewa yafito yana daure da towel saman waist dinsa, ganin ammi zaune bisa kujera da wannan lokacin yasashi tsayawa daga bakin toilet yana kallonta da mamaki, duk da ammi uwace ga ajmal but seda gabanta yafadi because batayi expecting fitowar ajmal awannan yanayinba itade har kullum mamaki girman jiki irin na ajmal take gatsayi ga fadi duk da ba ta inda yabar Daddy sedeshi bayida girman jiki irin haka ko hakan yasamu asali da irin motsa jikin dayake yawan yine oho uwa uba ga kwarjini, dan kirkiro murmushi ammi tayi tayi tana kallon dan nata shima kallonta yake ko damuwa da yanayin da yake baiyiba yakariso yazauna gafe da ita yana fadin,"
Barka da safiya,
Yauwa barkade I hope katashi lapia ammi tafadi tana dubansa, ,"
Fine , gakanni a bedroom dinka sassafe koh breakfast nakawo maka ammi tafadi tana dan waige waige am ya ina aheel banganshiba dan tasan tare suke kwana, "
Yana gurin mommynshi , "
incede lapia yatafi gurinta ammi ta tambaya,"
Tunjiya yake kuka sena kaishi gurinta shine nakaishi ajmal yafadi yana dan hade gira , "
to ita heelah baranan dawowartane ko baka tambaya bane? Ammi tasake watso masa tambaya, "
babukatan hakan maybe tafi bukatan zama can ajmal yafadi tareda mikewa yanufi dresse mirror yadauki hairbrush yashiga tace kanshi, girgiza kai ammi tayi tareda numfasa tana fadin,"
MODIBBO dama inaso magana dakai jiyuwa yayi yakuma kallon ammin tasu wacce tamike daga inda take takariso inda yake tsaye tasuma cewa,"
Am jiya naturo nisha takawo maka breakfast sannan nace tashigo bedroom dinka tagyarama because naga yana bukatar gyara but sede banji dadin abunda yafaru tsakanin kuba , zuru ajmal yayi yana kallon ammin tasu yanda fiskanta yakoma yanayin damuwa, hand dinsa takama tarike cikin nata taci gaba dafadin,"
magan ganunda kamata sam bai daceba, wannan yarinyar dakake gani tamkar amanace agaremu bata dakowa semu daukota mukayi muka sanyata cikin family tazamto daya daga cikinmu idan bamu sotaba baikamata kyamaceta ko mutakurataba ita marainiyace koma rikon maraya akwai dinbun lada cutar dashi akwai zunubi,
yarinyar nan tunda tazo gdn nan bawanda ta kaunaceshi kamar danka tanason yaron sosai karkaga bayan tafiyarka heelah bata nan yanda nisha ke kula dashi wanda ko heelah da tahaifeshi bata masa irin wannan kulawar shima aheel din inka duba yanason nisha sosai kuma yashaku da ita cikin kankanin lokaci baikamata kadinga sauke fushinka akantaba harkana kokarin yimata sha maki da dankaba ,
karfa kamanta maison naka kai yakeso kamata yayi duk maison naka kajashi ajiki bakayi kokarin yageshi daga jikinkaba , yarinyar nan alkhairice agaremu ba sharriba wani lokacin abunda bamuso shiyake zama alkhairi agaremu abunda muke matukarsu wani lokacin ba alkhari bane, plsease kadauki yarinyar nan tamkar sauran yan uwanka,
bawani abu bane yasa naturota ganin nayi late shiyasa nace tazo takawo maka kuma bedroom dinka na bukatan gyara tunda yanzu ba mata kakedashi akusaba kuma nasan zaka bukaci wasu abun kafin matar taka tadawo but tunda baka bukata balaifi , ni inna samu time zan dinga ziyartarka
sorry maybe kana da abunyi nazo ina kokarin bata maka time, nibarinaje karnayi late koda akwai wani abunda kakeso kuma ? Ammi tafadi yayinda take zami hanunta daga nasa,"
No things ajmal yafurta slowly yana kallon ammin tasu jiki duk amace,"
Alright nibari nawuce sena dawo , ammi nagama fadin haka tajuya tafice tabar ajmal agurin wanda yarintsa ido magan ganun ammi se yawo suke masa bisa , kunne gaba daya kalamunta sun kashe masa jiki , shikanshi baisan meyasa yake kin yariyar ba bakuma dalili duk dacewa tun lokacin da yayiwa yarinyar warning yaji ba dadi baiga kyautawar hakanba kodan sonda take nunawa aheel baikamata yamata hakanba gashi yarinyar akwai tsafta ta iya aiki balaifi,
kusan karfe 9:30 nisha ta tashi daga bacci toilet tanufa tayi wanka tareda wanke bakinta tafito tashirya takimtsa cikin riga da skirt rigar tanada duguwar hannu White color se black skirt mai laushi tayi stoking harsaman stomach dinta dressing din yayi matukar yimata kyau, nan ta daure gashinta yayi style din donut tasanya back hula mai kwaliya irin na butterfly kamar wata yar baby haka tafito tayi tas da ita masha allah,
tana fitowa parlour tasamu su hajja mm da goggo rabi harsun suma yin breakfast dinsu, nan ta karisa garesu tana ta zuba murmushi, suma murmushin suke tunda suka hangota harta kariso tasuma gaishesu fiska cike da annashiwa suka amsa mata goggo rabi tasuma fadin,"
Kai sirkata kinyi kyau gaskiya sekace maizuwa gasar kyau ta duniya masha allah amaryanmu , kallonda hajia tayiwa goggo rabine yasa rabi tahadiye maganar tareda washe baki tana fadin, "
Kizauna mana kintsa atsaye , sumu sumu nisha tanemigu tazauna, "
yau kintashi da wuri kenan dan nasanki da bacci shiyasama nace kar atasoki ashema kintashi hajia tafadi yayinda ta turawa nisha plate din abinci gabanta, murmushi nisha tayi tana fadin,"
ai tundazu natashi natsaya shiryawane bansan kunfitoba da nafito tundazu ai, "
To ai shikenan maza kizuba abunda kikeso kisoma ci , nan nisha tashiga serving dinkanta tasumaci , sunaci suna taba hiransu ,"
Yakamata muke kirakani saloon nawanke kaina dan gobe ko jibi nakeson komawa kd , garinku ya isheni , dan zaro ido nisha tayi tana kallon goggo rabi muryan ciki nisha tace,"
Tafiya kuma ? dariya Goggo rabi tayi tana kwaikwayan maganan nisha tana fadin,"
Eh tafiya zanyi zakibini mutafi tarene , dasauri nisha ta gyada kai tana dan shagwabe fiska kamar mai shirin kuka because gaba daya taji ba dadi zasuyi kewar goggo rabi mai barkwanci , dariya dukansu sukayi daga Goggo rabi har hajia suna kallon nisha wanda tayi fiskar tausayi ,"
waneni natafi da matar mutane ammade wani lokacin zakuzumin hutu koh, Goggo rabi tafadi tana kallon nisha , gyada akai kawai nisha tayi because duk taji jikinta yayi sanyi ,"
oh allah ya kyauta da barin zance irinna rabi , hajia tafadi cikin zuciyarta tana kallon rabi yanda taketa zuba tana tsokanar nisha , harsuka kammala karyawa suka nufi parlour suka cigaba da hiransu anan,, suna cikin tsaka da hira daya daga cikin dake securityn dasuke gadi agdn yashigo cikin parlourn yana dan wul wulga ido ganin su hajia azaune cikin parlourn yasa yayi saurin daga musu gaisuwa ,
seda suka amsa daga bisani yasoma isar da sakon da akaturoshi ,"
Ogane yace nazo nakira bakowar yarinyar dake zaune gdn nan (nisha) hajiya da goggo rabi kallon juna daga bisani suka maida kallonsu da tayi zuru zuru da ido
🦚🦚AJEEMAL🦚🦚
Story and writing by oum amreesh❤️
DAGA ALKALAMIN
Khaleeseart Raeeys✍🏼
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Page4️⃣0️⃣&4️⃣1️⃣___________✍🏼 To ke kanji papan aheel nakira maza seki hanzarta kije , goggo rabi tafadi cikin rawar jiki tana kallon nisha dake rarraba idanu, asukwane nisha tamike tasuma kokarin bin bayan security suka fice tana biye dashi,
suna zuwa side din ajmal security yasa hanu yabude mata door seda yaga tashi yamaida kofar yarufe yakoma bakin aikinsa , Nisha tunda tashiga parlour taketa tsilli tsilli da ido dan bataga kowa a parlourn ba, hakan yasa ta tsayawa daga nisa tana yan kalle kalle,
jin motsin sakkowa tab tab yasa nisha tamaida kallonta ga upstairs , kallo daya nisha tayiwa ajmal yayinda yagama sakkowa tamaida kanta kasa , fiska bayabo ba fallasa yakariso yazauna bisa kujera yajanyo table din abinci gabansa yasuma zubawa kanshi abinci yafara ci , sam ko kula da inda nisha take baiyiba , kokadan baisan da tsayuwarta cikin parlour ba, cikin natsuwa yakecin abincin hankali kwance kamar ance ya dagokai carab idonsa yasauka kan nisha dake tsaye ta dukarda kai kasa , kauda kai yayi yaci gaba dayin breakfast dinshi kamar bai gantaba ,
seda yatabbatar cikinsa ya dauka yakoshi sannan ya dakata da cin abincin ya kai hanu yadauki coffee ya kuma yajigina da jikin sofa yansha ahankali yana latsa wayarsa , gaba daya nisha jitayi gaba daya tagama gajiya da tsayuwa duk da yaganta but baice mata komaiba , "
Ke! cikin hanzari nisha ta dago takalleshi jin yana magana "
Come here ajmal yafadi yayinda ya dire cap din coffee saman table yana kallon yarinyar da mamakin hali irin nata tayi silent dayawa taita wani noke noke kamar mara gaskiya , cikin natsuwa nisha ta kariso kusa ta tsaya tana kallonshi , shikuwa seda yagama karemata kallo tsaf sannan yace,"
ke kurmace ?
Ahanzarce nisha ta dago tana girgiza kai alamar"
A'a, "
tsayuwar mekike acan? ajmal yakuma tambaya ,
jiwata tambaya nisha tafadi cikin zuciyarta , azahiri kuma cewa tayi ,"
bakai katura akirani kanason ganinaba tafadi tana dan turo baki, dan hade gira ajmal yayi daga bisani yamike yana fadin,"
Kigyaramin bedroom dina kafin nadawo , bajira amsawartaba yawuceta yawuce upstairs yanufi bedroom baki bude takebin bayan ajmal da kallo harya kurewa ganinta ,"
hala yamance ba aikatau take zaman yi agdnsuba koda yaga tagyara masa wacan time dinma saboda amminne , mutumin da koda tabauta masanma ba lallai yaji dadi ya gode mataba duk da ita dinma zatayine ba dan yaji dadin yagode mata bane sede tayi dan kanta, ta dadai tana tsaye agurin tana surutai cikin kokon zuciyarta , jin takun sawayen ajmal na sakkowa yasa tayi saurin maido da tunaninta tashiga tattare kayan breakfast din dake kan table tashiga kiciniyar fita daga parlour ,
ajmal yana karisowa parlourn yanufi inda ya ajeye key din motarsa ya dauka yafice daga parlourn shima yanufi motarsa daya daga cikin security yanufo cikin sauri da nufin budewa mai gidansa murfin kofa but ajmal ya dakatar dashi bayaso , yawanci kusan kullum se anyi hakan da zaran ajmal yafito zaifita se ansamu daya daga cikin security's wani yatasu zai budemasa mota seya hana because bayaso , hatta driving yafi bukata yayi da kanshi se inwani time din yanajin kasala ko ya taso office yagaji to yana bukatan agaji but akasin hakan tofa yafi gane yayi da kanshi, yana shiga motar yamata key mai gadi yabude kofar gate ajmal yasakai yafice,
Nisha tana karisawa parlour yanda tabarsu goggo rabi da hajia haka tazo ta tarar dasu se fira suke suna raha, asukwane ta wuce kitchen ta ajiye tray din abincin tafito parlour indasu hajja mma suke ta zauna tadanyi shiru kai sunkuye , "
Ke lafiya kuwa kiranme ajmal ke miki , goggo rabi ke tambayar nisha , murmushinda baikai zuciba nisha tasake tana fadin ,"
bakomai wai bedroom din shi yakeson nashiga na gyara mishi, "
Yo kajimin yarinya shine kikazo kikayi zamaniki maza tashi kije kiyi aikin lada , Goggo rabi tafadi tana washe baki, sam nisha tayi tsammani baza akyaleta tajeba because itaba yar aiki bane dazai sata aiki time dinda yabukata yahanata lokacin yakeso kuma tariga ta alkawartawa kanta bazata sake gigin dosa part dinshiba tunda baya bukatarta , but jin datayi Goggo rabi tace taje tayi aikin lada kobadan shiba tasamu ladan tunda ko bakomai ta taimaki gwauro tunda ba mata kusa dashi kuma bugu dakari yanzu shida kanshi ya nemi agajinta, "
Tunanin mekike? ko kingajine hajiya ta tambaya tana kallon nisha data tsaida idonta guri guda tana nunani , ,"
A' a hajiya barinaje nisha tafadi yayinda tamike tafice daga parlour, "
Hhh Ravi kinji mutumin nakifa da neman magana , hajia tafadi tana kama haba , "
Hmm naji allahde yashige mana gaba komai yadai daita kafin waccen shashar yarinyar tadawo abunda Goggo rabi tafadi kenan hajia tace ,"
Ameen tana yar murmushin farin ciki ,
nisha tunda takuma sashin ajmal tasuma aikace aikace tagyara ko ina ta kimatsa tashare tagoge ko ina yayi fes , tasanya turaren daki kamshi ya dauka kota INA, wannan time din har dakin aheel seda tashiga room din dabata samu shiga wancan lokacinba , tundaga mashigar bedroom din wato door din dakin pink color, haka cikin bedroom din yake gwani shaawa bedroom din aheel yayi kyau kwarai , komai pink color ga kayan wasa kaca kaca azube akasa ba kalan kayan wasan da babu, haka nisha tashiga taketa karewa dakin kallo tana murmushi kamar gunar auduga seda tagama kallon dakin ya isheta sannan ta gyara abunda zata gyara tafito tanufi downstairs tafita tabar side din tanufi nasu ban garan ,
wannan karun koda tashi parlour ba tarar dasu hajia ba alamar cewa sun bar parlourn hakan yabawa nisha daman wacewa bedroom dinsu ta dale saman bed tayi kwanciyarta tana mai ajiyar heart, phone dinta nagefe sejin ringing din wayar tayi yaratsa dodon kunnenta , dagawa tayi dan taduba waye kekan layi setaga number ne , kuma ba number Nigeria bane, kamar baza ta daukaba harya kusa yankewa , daga bisani ta daga takara akunne batare da tayi maganaba still de akwance take bata dagoba,"
Hello my little sisi kamal ke magana ,
daram nisha kirjinta yabuga wanda yasa ta tashi tazauna daga kwanciyar da tayi, but takasa magana tsantsan farin ciki,"
Hello sisi kinajina kuwa , harya yayi niyar kashewa jin shiru ba ayi maganaba , seji yayi tana fadin, "
Inaji ya kamal antashi lapia ? wani dadine ya ziyarci zuciyar kamal nan da nan jin tattausan muryan nisha ya ratsa kunnuwansa, ,"
Alhamdulliha ya kike yasu hajiyarmu I hope kowa lapia, "
Kowa lapia nisha tafadi cikin sanyin murya,"
Ya kewar dan karamin yayan naku , ko bakuyiba ? kamal ya tamabaya cikin sanyin murya , "
Munyi kewarka mana yaji nisha tafurta ahankali , wani cold smile yasaki kafin yace ,"
banga alama ba tunda ba akiraniba tunda natafi ballai aji lapia ta, kamal yafadi yana lumshe ido kamar yana gabanta, nisha maimakon tabashi amsa se tambayarshi tayi,"
ina Aunty nabilah, bude idonshi yayi daga lumshesu dayayi yace ,"
Bama tare yafadi atakaice, shiru nisha tayi bare da takuma cewa komaiba shima shirun yadanyi kafin yace,"
Mekika shirya min because munkusa dawowa soon insha Allah"
To allah yasa duk abunda kakeso shi za ashirya , nan suka dan taba hiransu na dan wasu mintuna kafin daga bisa suka tsahirta sukayi sallama yakatse wayar ,
Nisha phone din ta ajiye gefe tana dan murmushi ta kuma komawa ta kwanta idonta na kallon sama se zuba murmushi take tana lumshe ido , bacci takeso tayi but se baccin ya kauracewa idanuwanta , haka ta jima tana yan tunane tunane daga bisani tamike tanufi toilet dan gabatar da alwala domin kuwa time din sallah yayi , koda tafito tayi sallah tasake neman guri ta kwanta amma wannan karun bacci yayi nasaran cinye idanuwanta ,
haka nisha tayita sharan baccinta harsu fadeelah suka dawo suka tarar tana bacci mai nauyi kasan cewa yau suna cikin farin ciki sunka kammala exam din second semester sun tsaya shagalin bakwana da friends dinsu kasance hutu mai dugun zango za ayi, shiyasa sukayi late din dawowa dawuri,
koda suka dawo suka tarar da nisha na barzar bacci basu tashetaba suka wuce sukayi lunch dinsu daga nan sukayi sashin hajja mama, se guraren la' asar nisha tasamu daman farkawa tun tashinta taga alamunsu reeda sun dawo daga school amma bata gansu adakinba, dan haka tamike tanufi toilet tayiyo alwala tafito tayi sallah,
tana idarwa tayi parlour tanufi hanyar kitchen, tasamu barka tasanar mata tana jinyunwa ta sama mata abunda zatasa acikinta haka tazauna bisa dining table Barka tazu tajere mata kayan abinci gabanta , nan da nan nisha tazuba abincin tasuma ci dominko ta tashi da yunwa acikinta, seda ta kammala tashiga tattare kanyanda tayi amfani dasu tayi kitchen ta ajiye , daga nan tashiga kiciniyar taya Barka dawasu aikace aikace, "
Oh nikam yar nan da kinbarni nayi aikina kidaina wahalar da kanki inkin barnima yanzun nan zan kammala komai aiki bayamin wahala nasaba, kekuwa basabo ataredake dan Allah karki wahalar dajikinki kibarshi na gode, "
Kai haba mana dakin bari natayaki narege maki wasu aikin nisha tafadi ashagwabe ,"
Aa barshi kawai bari na hadamiki abincin papan aheel kikai mishi yanzun nan ya dawo yakuma aiko kikai masa abun tabawa, gimtse fiska nisha tayi
" wato miskilin nan dawo harwani nakai masa abun tabawa karfi dayaji yar aikinsa yakeso ya dawo da ita hmm "
Magana kikeyine Barka ta tambaya tana kallon nisha da tamaida kai gefe tana surutai kasa kasa , cikin hanzari nisha tana washe baki tace, "
Ah cewa nayi kawo nakai masa, "
To to bari na hada yar albarka, nan Barka ta hada komai cikin tray tamikawa nisha , takarba tafice tana surutai cikin zuci , tana fita direct tayi sashin ajmal tabude kofar ahankali tashiga bakinta dauke da sallama,
yana zaune bisa kujera idonsa yana kan TV yana kallo jin sallamar nisha yasa ya maida kallonsa gareta tareda amsa sallamar tata yana mai gyara zamansa, nisha karisowa tayi ta durkusa harkasa ta ajiye tray din abincin bisa table din gabansa daga bisani tadukar dakai kasa tana fadin, "
Sannu da dawowa anwuni lapia "
Fine kawai ajmal yace yasuma taba kayan ciye ciyenda nisha takawo masa, har nisha tamike zatafice seji tayi yace,"
where are you going? jiyuwa nisha tayi ta kalleshi baki na bari tace"
dama zan tafine , zauna kijira abunda yace kenan yacigaba dacin lallausan bugar dinsa mai dadin ci , guri nisha tasamu daga gefe saman carpet tashiga kurawa TV ido , shiru kakeji parlour kamar ba dan adam acikinsa se tv dake aiki, ahankali yakecin abinci kamar zaici kamar bazaiciba yanaci yana latsa wayar kaikace bajiransa akeba , gaba daya nisha jitayi tagaji dazaman nan nisha tashiga hararoshi tagefen ido se danna wayarsa yake yadaura kafarsa gefen table se karkadasu yake , kauda kai tayi tacigaba dakallon TV cikin zuciyarta banda banda tsinuwa ba abunda yakesha, karo nabiyu da nisha ta dago zata kuma hararansa suka hada ido time dinda yajiyu, batasan sanda tasake fiska tamasa murmushi ba, gimtse fiska ajmal yayi daga bisani yamike yana fadin, "
Zaki iya tattarawa kifita yana fadin haka yajuya yanufi upstairs, nisha bin bayan ajmal tayi da kallo tareda murguda baki tasuma tattare table tanufi hanyar fita , yayi daidai da shigowar heelah da aheel cikin parlour, nisha tamlar tasake fitsari haka taji kaikace bala' ika tagani , gaba daya nisha takasa yin gaba ko baya, "
Oyoyo aunty nisha, aheel yafadi cikin zumudi yayi kanta dagudu yarungumeta , nisha kuwa baki bude take kallon heelah wacce itama itan take kallo da tambaya iri da kala cikin zuciyarta , mai wannan stupid girl din take mata cikin parlournta ga kuma traydin abinci ahannunta tana tsaye tsakiyar parlour,
daker heelah take daga kafarta tana kokarin karisuwa cikin parlourn , jima kadan bayanta aka bude koda akashi , KB ne tareda wani security sunshigo da akwati suka ajiye tsakar parlour suka fice, shiguwar KB kenan idan nisha yasauka akanshi nan da nan bugun zuciyarta yasake karuwa da sauri dasauri hanunta har bari yake , shikanshi KB lokacin da idonsa yayi tuzali da nisha gaba daya mamaki yagama kamashi sam baiyi tsammani sake kallon yarinyarba ,gaba daya ta canza tasake zama cikakkiyar budurwa inba kamata farin saniba bazaka taba cewa ita bane, kuma yanayin kallon da nisha datake mishi nasanaiya yakara tabbatar masa nisha ce,
heelah gani tayi nisha da KB sunayiwa junansu wani irin kallo wacce bata san nameyeba nan ta matsa kusada nisha tafizge aheel daga jikin nisha tayi gefe dashi, daga bisani tashako wuyar rigan nisha tana fadin,"
Uwar me kikashigo yimin a parlour tukunama uban waye yabaki izzini, "
Nine ! sukajiyu muryan ajmal daga sama yana hangosu, aheel dake gefe yayi rau rau da ido yana shirin kuka jin muryan papansa daga sama yasa yaruga dagu yayi sama gun papanshi , heelah kallon nisha tayi da idonta yacika taba da kwallah sakin wuyar rigan nisha heelah tayi tana fadin,"
banza wuce kifita kibacemin dagani karna sake tuzali da kazamar fiskarki cikin side dina inba hakaba senayi kasa kasa dake heelah tafadi cikin murya mara sauti, cal cal nisha takama hanyar fita still de idonta nakan KB dashima nashi yake kanta harta gama fita, tajanyu musu kofar tarufe ,
cikin hanzari nisha takarisa part dinsu ta dan gwarar da tray din abincin bisa dining table, tayi bedroom dinsu da gudu bakowa cikin dakin hakan yasa tanufi toilet cikin hanzari, domin ko fitsari yacika maranta tam , sedatayi tagama sannan ta kimtsa daganan hawaye suka suma ziyartar face dinta, daker tasamu ta danne zuciyarta tahana kanta kuka, daga bisani tawanke face dinta tafo tana goge fiskanta da dan wani karamin towel,
gabantane yakuma faduwa ganin KB tsaye gefen toilet kamar wani mai gadi yana jiran fitowarta, nisha batasan sanda tayi wurigi da towel din hanun taba tasuma kokarin komawa toilet aikuwa cikin hanzari KB yashige gaba dasauri ya hanata shiga bakin nisha har bari yake gurin fadin,"
Meye haka bani hanya,"
Kije ina? KB yafadi yana zuba murmushin keta, "
Wlh kaban hanya ko inyi ihu intara maka mutanen gdn nan , "
Kiyi ihunki narufe kofar bamaiji, zaro ido nisha tayi tana kallonshi kafin tayi hanyar door dasauri tashiga murda handle din kofar taji arufe,"
Ga key dinfa ahanuna kidena wahalar dakanki, magana Nazo muyi dake bawani abun zan mikiba dakike ta gudu , matsowa KB yayi har inda nisha take dab da ita kamar mai shirin rungumarta , rintsa ido nisha tayi jiki sai rawa yake , KB kuwa se fashewa yayi da dariyar mugunta ya matsa baya yana fadin ,"
Ashede kedin mara kunyar ganganne idan ban mantaba kefa ba matso rajiya bace dan har maza kina iya duka but mai kama ace jaruma kamarki taji tsoron hukuncin da namijiba KB yafadi yana kuma tinkaran nishaaaa🦚🦚IG AJEEMAL🦚🦚
Story and writing by oum amreesh ❤️
DAGA ALKALAMIN khaleeseart Raeeys💦🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹4️⃣2️⃣&4️⃣3️⃣_______Please waime kakesone katakurawa rayuwata dayawa , nisha ta tambaya cikin bacin rai, ,"
Kwantar da hankali yan mata Ba abunda nakeso magana nakeso muyi dake KB yafadi yayinda yasa hanu yadafe door dinda nisha take jingine har numfashinsa na dukan face dinta , "
Niba wani magana da zan tsaya ji daga gareka , face dinkama banason daga ido nakallah balle munanan zan tukanka kunnuwana su saurara, nisha tafadi afusace tareda sa hanu tature kirjin KB dakarfi wanda hakan yasa yayi baya haryana nemana faduwa , "
Ke nikika ture haka? KB ya tambaya yana mai dafe kirji yana kallon nisha, ,"
Eh kai nature , inaso kasani inde dan marinda namaka yasa kakasa mancewa haryanzu yana yawo cikin kwakwalwarka kaketa kokarin bibiyar rayuwata da sharri kakeson lalata rayuwata to kazu karama ga fiskata nan sekasamu daman fita daga rayuwata, "
Uhm aike yanzu kinwuce hukuncin mari sede hukuncin kisa ta hanyar ratayeki ko fasa goshinki da bindiga , because laifinki yasake girma , bansan meyakawoki gdn nanba ammade kinkawo kanki inda ake nemanki, because babban yayanmu yana kan neman yar ta addan da tayiwa yan uwansa rashin imani , taso hallakar da rayuwarsu ,
To kisani duk Randa yafahimci kece wannan yarta addan kikashiga hanunshi ba tsayawa check sawa zaiyi adaureki se igiya tasaura ko yasa asaki dakin duhu wanda ko tafin hanunki bazaki ganiba har iya tsawon rayuwarki
KB dakatawa yayi da maganar yadan numfasa tareda yar dariya yanemi bakin bed ya zauna yana karewa nisha kallo yana sake shu' umin murmushi kafin yacigaba da fadin,"
Hmm ayanda nasan big bro da namijin zuciya da alokacinda kikaso illatamu dubunki yacika yayi nasaran kamaki agurin toda sede ahaifu wata bakeba,"
harsashi zakiji bisa kwakwalwarki kuma gwaarkima bazai samu mutuntawaba , can jeji za atattaraki ajefar dake namun daji sukarisa KB yafadi yana wani sakin bad smile, gaba daya yagama daure jijiyoyin nisha da kalamansa , duk ilahirin jikinta se kyarma yake aikin tsorita da maganganusa ( nisha taji bakin bindiga) jitake kamar tasake fitsari , "
Hmm kince namareki nafita arayuwarki koh,?toshiga rayuwarki yanzu nasoma duk inda kike ina biye dake, yanzu sekijira kiga abunda zaibiyo baya matukar kina gdn nan se nasa asirinki yatunu bani guri nashige KB yafadi yana kallon nisha datayi tsamu tsamu da ita, daker nisha ta iya jan kafa tamatsa KB yasa key yabude yafice daga dakin, "
Hasbunallahu wani'imal wakil, ya allah kamana tsari ga shaidanun mutane masharanta, masuson ganin lalacewan gobenmu , nisha ke fadi ahankali yayinda take jan kafarta ahankali harta karisa bed ta kwanta tayilamo abin tausayi goshinta se tsatso zufa yake, "
Ya ubangiji kajikan mahaifiyata nima kajikaina badan namutuba , kabani ikon barin cikin gidan nan kafin wannan azzalumin yabatamin suna sukoreni, matukar babu alkhari zamana gidan nan ya allah kafitar dani daga gdn cikin sauki batareda nasha wahalaba, ahankali take maganar tana kuka kasa kasa tareda shashsheka ,
tadau tsawun lokaci tana kuka, jin motsin shigowarsu fadeelah yin sallah domin magarib ya gabato kai yasa nisha tayi saurin goge hawayen face dinta tareda maida ido ta lumshe tamkar mai bacci , "
Oh ni allah wannan wani irin bacci yarinyar nan tayine haka , reeda tafadi yayinda suka karisa shigowa dakin suna mai karisawa kusa da bed din da nisha ke kwance ta dunkule guri guda ,"
Nisha! wake up mana wani irin bacci kikene fadeelah tafadi yayinda ta haye saman bed tana jijjiga nisha, slowly nisha tabude idanu kamar maiyin baccin da gaske idanunta sunyi jawar fiskarta gaba daya ya sauya tsabar damuwa ,
tundazun muka dawo daga school muka tadda kina bacci harmukaje muka gamu firanmu sashin hajia still de baccin mukazo muka tarar kina shekawa"
I hope de lapia, nisha kallon kowannensu tayi daga bisani tamike daga kwanciyar da tayi tana dan kakalo murmushi, "
lapiata qalau kwaide kaina ke dan ciyo shiyasa Na kwanta nayi long bacci basan time yaja hakaba ,"
Ayya sorry kinsha magani ? fadeelah ta tambaya, "
Ah naji sauki banajin ciyon yanzu ,"
Okay to yanxu kitashi muje muyi sallah , bayan nan akwai story mai dadi , reeda tafadi yayinda taja hanun nisha tana murmushi , seda sukayi alwala sukayi sallah , bayan nan suka dawo saman bed suka suma yin firansu , suna bawa nisha labari hutunda sukayi dakuma irin shashewar dasukayi
nisha kwai murmushi take tana karawa , domin allah kaidai yasan tunanin datake juyawa cikin ranta , suna dade suna firan gabatowan sallahn ishane ya datse musu firan batareda bata lokaciba suka tashi suka gudanar da sallah
Bayan idarwansu harsun hai saman gado zasucigaba da firan kenan ammi tashigo fiska cike da fara'a , ganin ammi da sukayi yasa dukansu suka shigayiwa ammi smile , ahankali ammi takariso kusa da bed din tazauna tana kallon nisha da itama kallon ammin take cike da farin ciki, "
Oyoyo ammi su fadeelah suka fadi yayinda sukkinsan kanta suka rungumeta suna dariya , "
Ku da allah ku kyaleni seyanzu kukasan da ina gdn ko nemana ai bakuyiba da nadawo ammi tafadi tana hararo su reeda dasuka tura baki gaba sun shagwabe fiska suna fadin ,"
Ai bamusan kindawo bane ammi kinsan mumuke fara miki welcome"
Uhm kukajiyo ni kubani guri wajan kyakykyawar yata nazo, ammi tafadi tana kallon nisha da tasunnar dakai tana satan kallonsu fadeelah tana murmushi , "
Tashi muje muyi dinner kinjiko ammi tafadi tareda jan hanun nisha suka mike ,"
Mukumafa ammi? Reeda ta tambaya cike da niman magana ,"
Inzaku iya kwa iya biyomu ammi tafadi tana tabe baki, daga nisha har su fadeelah dariya suka fashe dashe suka nufo parlour,
a parlour suka yada zango indasu hajia da goggo rabi suke zaune, suma gurin suka samu suka zauna fareeda nakusa da goggo rabi reeda kuma kusa da hajia yayinda nisha ke makale kusa da ammi , "
Oh yaukam yar taki wuni zubur tana hutawa abinta ko duk gajiyan aikinne yasake bacci haka ko lekomu bakiyiba , goggo rabi ta tambaya tana kallon nisha da tamakalewa ammi ,"
Aiki kuma ?waye yasa kyakykyawar yata aiki ya wahalarmin da ita, ,"
Waye kuwa banda shalelen danki MODIBBO da neman magana , hajia tacabe maganar tana murmusawa, ,"
yau kuma shida kanshi ,? Ammi ta tambaya,
Kwarai kuwa harda turowa ayi kiranta kamar abun arziki , goggo rabi tafadi,"
Alhamdulillah MODIBBo yafarajin magana tasan hakan yanada nasaba da magana da nasihunda tamasaba, ammi ke magana cikin zuci , azakiri kuwa kallon nisha tayi datake tazuba murmushi , gefe kuwa takalli su fadeelah da reeda daketa kallon juna suna maganar kurame ,"
Incede lapiar ku qalau ? Ammi ta tambaya tana kallon su fadeelah, "
Lapia qalau ammi suna kuma kallon junansu , ammi batakai ga karisa maganarba , Barka tazo tasanar dasu komai yazama ready , "
To ai seku tashi muje yannema hajia tafadi tana yar dariya tana kallonsu reeda, gaba dayansu dariya suka sake sannan suka nufi dining suka suma gudanar da dinner cike da farinciki da annashuwa , suna cin abincin suna fira , harsuka kammala dinner, daga inda suke basu motsaba suka cigaba da firansu cikin raha, nan goggo rabi take shaida musu tafiyarta gobe zata dagashi because se antsaida sa ranan wadannan yaran fadeelah da reeda domin acewarta bataki adaura auran yanzu suyi gaba da matar danta wato mahaiseen , amma komai na bukatan shiri da lokaci domin ita dayar wato fadeelah bawai sun gama fiskantan juna da samarinta bane , kaf cikin samarinta nawanda ta tsayar madubin da zata duba matsayin abokin rayuwa, domin ita hankalinta ya karkata kan babban likitansu kuma aboki ga yayansu wato doctor fu' ad hadaddan matashin nan maisaukin kai da barkwanci , abunda yake yasake burgeta dashi kenan ,
bayida girman kai kwata kwata ga son dariya da wasa kullum face dinshi dauke da fa' a , kusan kowani lokaci da hotonsa take kumalo because duk safiya inta tashi seta kalli kyakykyawar pic dinsa tashafa face dinshi tacikin screen din wayar ,
wani time din inkewarshi yamata yawa tanason sashi cikin idanunta seta kirkiro rashin lapia dan kawai taganstaganshi, amma koda yazo haka zai gama dubata ya bincikata amma bawani abunda ke damunta sannu ahankali doctor fu' ud yagane salon iyashege irin fadeelah na rashin lapia da take daurawa kanta,
dan haka daga zaran annemeshi fadeelah ba lapia dazaran yazo ya dubata ya tabbatar bawani problem seya dauko allura yace zaimata yasanta datsoron allura itako tana ganin haka zata zura dagu tayi toilet bazata fitoba seta tabbatar yatafi,
tunda tafahimci tsorata da allura dayakeyi yasa tadena kwanciyar , setunani kodayaushe da addu'an allah ya maidu da hankalinsa gareta ya farajin abunda takeji gamedashi,
washe gari da asuba bayan su nisha sunyi sallahn jikinta fadeelah da reeda suka koma bacci dan yau bacci yaga takansa kasancewa sunsamu hutun school yau bacci se abunda yaturewa buzu nadi se anga farkawansu , nisha kuwa bata komaba se karatun Qur'an datadan tsayayi, ahankali take karatun gudun kartashiga hakinsu , segurin 6 sannan ta dakata da karatun , tashiga toilet ta sheka wankanta tafito takimtsa jikinta tanemi yar duguwar gown da dan karamin mayafi ta daura bisa kanta tanufi hanyar parlour,
direct kitchen tanufa ta tarar bakowa aciki , hakan yasa tayi hanyar dakin baba barka tana zuwa tabude kofar ahankali tashiga lekawa , akwance tasamu barka sesake gwarti take kwar kwar bacci harda minshari , murmushi nisha tayi gami da kada kai tamaida kofar tarufe , takoma kitchen,
nan da nan nisha tashiga dawainiyar hada girki kala kala , tadafa wannan ta sauke wannan seda takusan kammala komai barka tashigo tana hamma gami da murza idano tana kallon nisha kitchen duk ya kacame da kamshi girki, "
yau naga takaina da wanga diya , mekikeyi hakan nan barka ta tambaya tana kama haba, dariya nisha tasaki tana fadin,"
Aiyukan nake dan ragemiki dan naga kamar agajiye kike baccinki yayi nauyi dan har dakin nashiga inata tashinki amma naga baki tashiba shiyasa nace bari nafara rage aiyukan kafin kizo,"
uhm wlh kekam murane da ciyon kai yadan matsamin to tunda nasha magani kuma shikenan dan ko sallahn asubama amakare nayi bakiga bisa sallaya naketa gyan gyadawaba, barka tafadi yayinda tasuma tayata da aikin, "
Masha allah yau kitchen yayi bakowa , me ake dafa mana ne , sukajiyo muryan ammi tafado kitchen din kamar daga sama, tana sanye cikin shirin fita office, "
Barka da safiya ammi antashi lapia, atare nisha da barka suka dagawa ammi gaisuwa nisha se washe baki , ammi amsa musu tayi cikin fara' tana mai karisowa kitchen din,"
Maizamusamu mubawa cikinmune nida Daddynku kafin muwuce ammi ke magana yayinda takalli nisha tana yan bude bude , "
Ammi kije kizauna yanzun nan zan kawo miki nisha tafadi cikin zumudi ,"
to shikenan bari naje inajira, ammi nagama fadin haka tajuya tafice tana murmushi , ba bata lokaci nisha tashirya abinci cikin tray, tafice dashi , dinning tanufa ta tadda ammi da Daddy suna zaune bisa kujera suna dan kuskus , motsin isowar nisha gurin yasa suka dago kai suna kallonta suna murmushi, "
Daughter yau hardake cikin kitchen kina wahalar dakanki ko, Daddy ke fadi yana murmushinsu na dattawa murmushi kawai nisha tayi tareda dagawa Daddy gaisuwa "
Daddy antashi lapia, amsa mata gaisuwan yayi yana mai tambayan me aka kawo musu , nan da nan nisha tashiga bude abincin kamshin abincin ya cikawa su ammi da Daddy hancinansu , "
Masha allah allah yasa yanda kamshin abincinnan ketashi yacika mana hanci haka zamuji dadinshi abakinmu ammi tafadi yayinda tasuma zuba musu abincin , nisha se zuba murmushi take kamar gunar auduga, nan tajuya ta koma kitchen din, tadauko wani hadadden flaks da cups ta dawo dinning tundaga isowata gurin ta fahimci delicious din da ta hada ya tashi kansu ganin yanda sukeci suna kada kai ,
Ajiye cups din tayi sannan ta dauki flaks tashiga tsiyayamusu special kunun madara mai matukar dadi da bada shaawa ta dire musu cups din gabansu tana murmushi, kallon juna Daddy da ammi sukayi kafin suka kai hanu suka dauki cup din suka kaibaki, ammi seda tayi rabin kofi kafin tasauke cup kasa shikuwa Daddy seda yaga kwal uwar daka , kafin yasauke nashi kofin ,"
Masha allah daughter allah ya albarkaceki , Daddy yafadi yana shafa cikinsa alamar koshi, "
Ameen! Nisha ta amsa tana sunar dakai, "
Ammade zakikaiwa yayanku wannan delicious din nasan zaiji dadinta ,ammi tafadi tana kallon nisha, cikeda murmushi nisha tace ,"
Eh zainkai mishi ammi , dama yau nisha daniyar burgeshi ta tashi , domin shima da NASA special din agefe data tanada masa, "
Uhm dan nakinma da ba gwaninta ake masaba Daddy yafadi yana tabe baki , "
Ai halinka ya dauko ammi tafadi tana dan yamutsafisa ,"
Ah nikam rabani bahaka nakeba kema shaidace tashi mutafi daddy yafadi yana murmushi tareda mikewa itama ammi murmushin take tamike sukayiwa nisha sallama suka fice , haba data jikin nisha seyayi sanyi jin abunda daddy yafadi ba ayiwa papan aheel gwanita gaba kidaya setaji tasare, tattare kayan abincin dasu ammi sukayi amfani dashi tayi tamaidasu kitchen,
Dawowa parlour tayi tazauna natsawun wasu lokuta, tana dan tunane tunane, guraren 9 nisha tamike tanufi kitchen ta dauka tray din abincin da zata kaiwa ajmal tanufi hanyar waje, sannu ahankali nisha ta dangana ga side din ajmal, security dake gefe yana ganinta dauke da tray din abinci yayi saurin bude mata kofar parlourn yana mata sannu, "
Thanks tace misha kafin tashige yamaida kofar yarufe , daga nisa tahangeshi saga dining area yana zaune bisa kujeran table din yana sanyi da wando short black iya gwaiwa se white shirt ya minmike kafa fuwa yana latsa waya yana rike da cup din coffen yanashaa , yanajin motsin shigowarta ya gyara zamansa yana maicigaba da latsawar tasa,
Ahankali nisha takariso kusa ta ajiye traydin abincin tasuma gaisheshi , maimakon ya amsa mata sai yatsareta da tambaya,"
Meya hanaki kawomin dinner jiya in the nights? batakaga bashi amsaba nisha ta hangi heelah jikin cikin dressing nazuwa aiki yanayin shigar yayi matukar amsar jikinta tayi kyau sosai ganin nisha tsaye tareda papan aheel sun zuba mata ido suna kallonta yasa takarisa sakkowa ahankali tana kuma kare musu kallo itama,
Ajmal kwaida kaiyayi yamaida idonsa kan wayarsa yacigaba da abunda yake , heelah da nisha kallon kallo sukashiga yiwa junansu nisha tasunnar dakai kasa kirjinta sai bugu yake , kwata kwata batayi zammanin ganin heelah ba tayi zaman tana can wajan aikin nata ,
heelah kallon traydin dake gaban ajmal tayi sannan takai kallonta ga ajmal din daya hade gira yabata fiska babu alamar wasa ko sakin fiska atare dashi, kallonta takuma kaiwa ga nisha wacce ido suka fito waje sezaresu take ,
wani dugun kwafa heelah tasaki bata da time dinda zata bata dan anjima kadan operation zataskhiga dan haka taciza lips dinta takalli nisha takuma hararanta kafin tashige fuuuu tafice daga parlourn tana sunbatu , nisha bin bayan heelah tayi da kallo hartafice daga parlourn kallon da heelah tayi mata tana ciza lips yasa taji gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya , "
To amma ita haka aiki rayuwa mutum da mijinshi sam bawata damuwa ko nuna kulawa yanzu haka ko breakfas batayiba bare wani kimtse kimtse na dakin fitarma dazatayi daga ita har mijin bawanda ya kulawani haka tasakai tafice ,uhm allah ya kyauta aheel da papanshi suna ganin takansu ga wanga diya, sam nisha ta mace da inda take se surutai take cikin zuci tajuyawa ajmal baya tashiga tunani ,
bata ankareba seji tayi ana zuba mata ruwan zafi bisa gefen wuyanta harcikin rigarta, wani ihu nisha tasake tayi baya ahanzarce ta dafe gefen wuyan nata tana kallon ajmal dake tsaye da cup din coffee ahanunshi yana hararanta ya hade gira, allah ya taimaka ruwan bawani zafi yasuma hucewa daba hakaba dase dan buzunta ,nisha kallonshi take tana zare ido nan da nan maganar KB yafadu mata ✍🏼🦚🦚IG AJEEMAL🦚🦚
Story and writing by oum amreesh❤️
Khaleeseart Raeeys💦💦💦
Page 4️⃣5️⃣&4️⃣6️⃣
______________🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹✍🏼
Gudu take sosai tamkar maishirin barin gari , bata tsagaita da tafiyarba harseda ta iso daidai wani dan kareriyar hotel tanufi compound din hotel din daidai parking space tayi parking, ko tsayawa daukan handbag batayiba wayarta kawai tazaro tabude morfin kofa tafito cikin hanzari tanufi cikin hotel din,
dedai door din wani bedroom tatsaya tashiga yin knocking ahankali , bugu daya zuwa biyu akabude , dan leko face dinshi yayi kadan yana kokarin fadin,"
Wa,,ye,, ganin heelah dayayi tsaye bakin door yasa yagimtse baki yashiga sakin wata iriyan murmushi ta marasa gaskiya still yakasa bata hanya tawuce, wani kallo heelah tawurga masa ganin yana tsaye baibata hayaba balle yamata iso, "
Yadai katsaya bakin door bakada niyar min cemin nashigo , kodai baka gane wayece a gabanka bane , murmushi yakumayi yana dan sosa head yana fadin ,"
Nagane mana come in , ya dan silale jiki yamatsa , cikin hanzari heelah tura kofar tayi daniyan shiga cikin, sekuma ta tsaya cak tana fadin ,"
Ya ilahi mai zangani haka? faruk ! wacece wannan yariyar kuma? heelah tafadi tana nuna wata yar matashiyar budurwa dake zaune bisa kujeran dakin tana sanye cikin t-shirt da dan wando iya gwaiwa , saman kanta tayi kitson atach har gadon baya , ga wasu uwar farata tsaro tsaro kallo daya zakamata kagane bata inda suka hada dan gantaka da musulunci alamade ba musulmabace , tana zaune tana danna phone dinta kallo daya tayiwa heelah da tashigo bata kuma sake daga ido takalleta nabiyuba tacigaba da harkan gabanta,"
Nayi maka tambaya kayi shiru bakace komaiba , who are she? kuma zaman metake anan, heelah takuma tambaya karu nabiyu tana tinkaran faruk Wanda yasunnar dakai kasa yana sanye cikin gajeran wando se yar vest , "
friend dinace tawajan aiki ziyara takawomin bana fadamiki kwana biyu banajin dadiba shine tazu tagaisheni dajiki, am,,am,"
Wait ya ishene haka , cemata tadauki komatsanta tafice daga nan kaikade nakeda bukatan gani, heelah tafadi yayinda taja gefe ta tsaya ta harde hand dinta saman chest dinta tana kallonshi , shiru faruk yayi baice komaiba kuma baiyi niyar aikata abunda heelah ta umurceshi dashiba , "
Ko bazaka iya sallamar gimbiyar takabane ninaje nasaita ta ahanya inuna mata bakin door, heelah tafadi tana hararo faruk sidi didi faruk ya wuce yanufi wannan budurwar yasunkuya daidai ita yashiga yimata rada kamar munafiki , meyace mata se allah daga bisani yanufi bedroom ba jimawa yafito hanusa dauke da makudan kudade ya taho yamikawa wannan budurwa , takarba tasanya cikin jakarta tadauki mayafi tadaura samankanta tareda rataye Jakarta tadauki hanyar fita ,
seda budurwar ta tsaya suka kalli juna kowanne ya harari dan uwansa daga bisani budurwan tasamu daman fita taja kofar da karfi tarufe, "
Hmm cin amanar dakasa gaba kenan kana tunanin asirinka bazai taunuba wataran , heelah tafadi gamida gyara tsayuwa tana kallon faruk dayanemi guri yazauna yana kallonta,
tsam yamike yanufi inda take cikin yanayi na magiya yashiga fadin ,"
Sweet mekike kokarin fadine wlh ba abunda kike tunani bane kinsan bayanda za ayi naci amanarki kamar yanda kike zargi tayama zan iya hada soyayyarki da wata macen kema kesan abune mai wuya agareni yafadi yana kokarin rungumarta , cikin sauri tamatsa baya tana fadin, "
Hmm faruk kenan kaifa namijine , ko kamanta takenku cewa namiji ba dan goyu bane to dan meyasa zan yarda da wadan nan zan tukan naku, bari kaji niba long talk nazo muyi dakaiba, dan numfasawa tayi sannan tamatsa daga inda faruk yake tanufi kujeran da yatashi tazauna kafin tacigaba da fadin ,"
ni dakai mundau tsawan lokaci muna tare tun before nayi aure still harnayi auran bamurabu ba muncigaba da kasancewa tare , ina baka kulawa da soyayya da lokacina wanda ko mijina da Dana da aikina ban bawaba, amma karshe cin amanace zata biyu bayan kyautatawar da namaka,
nasan abaya banida madubi naso dakauna danake dubawa face kai tun muna school a England bayan kammala warmu Allah baiyi zamucigaba da soyayya dakaiba , harna dawo gd nayi aure, sebayan aurena kafin allah yayi haduwata dakai har muka kulla wata soyayya sabowa wacce ko tunanin aurena banyiba nasaki jiki dakai namance da aure dake kaina ,
To amma yanzu na dawo haiyyacina , dagowa heelah tayi takalli faruk tana fadin, "
Gaskiya bazan boye makaba , ina kaunar mijina da dana kuma duk abunda zai kawomin cikas atsakanina dashi zan iya dakileshi , ina nufin akwai wani gibi dana bari atsakanin aurena banyi tunani akwai mecikeshiba, amma saboda sakaci irin nawa da rashin kula wata tana kokarin cikemin batareda na ankaraba, cikin katsaita da magana faruk yamatso daga inda yake ya tsuguna saman carpet tareda daura tafukan hand dinsa saman thigh din heelah yana fadin,"
Sweet waimeye kikeson fadine ban gane inda maganganunki yadosaba, mikewa heelah tayi tana fadin, "
ba lallai kaganeba faruk amma inaso kasani as from today na dakile duk wata mu amala tsakanina dakai zamudaina haduwa , banki mugaisa iya phone ba ya wadatar gaisuwarma intayi yawa tsan iya jigineta, "
Awani dalili zaki dakile mana jin dadi rana tsaka kodan kingani da wata shine kikeso kiyanke wannan danyan hukunci haka, faruk ya tambaya gamida mikewa tsaye yana kallonta "
Hmm kusan hakane because dama can inaso nasanar dakai haka to yanzu da time yayi nazodaide inda akazo gaban cin amanata , wlh tunda naganka tareda wata nake sakejin banason sake wata mu amala dakai , zanje nacigaba da kula da mijina da dana kamar yadda kowacce matar aure keyi nabakar lapia, heelah nagama fadin haka tajuya daniyar fita,"
Hhhhh yariya kenan wayace miki in akashiga bari saukin fita gareshi, ballema bariki irin nawa ba afita hakanan , karki mantafa kema cin amanata kikayi kinsan muna soyayya dake but kika zagaya kikaje kikayi aure ba tareda saninaba se labari naji amma duk namance dahakan nadawo muka daura inda aka tsaya ahakama nina nemuki kekinma banta da babina, amma wai nikike kallon idona kikefadin zaki koma gun mijinki zaki rabu dani,
mai mijin naki yafini dashi idanma ace kyau yafini da matsayi da kudi ninasan baifini zama namijibat , nasan saboda gazawarsa yasa kika amince dani kike bibiyata, ko kin mantane , nan kikezuwa da yunwarki mijinki baya kula dake bayida time dinki, nan kike zuwa ninake ciyar dake bawata gazawa kitashi kiyi godiya kitafi, wani dariya yafashe dashi kafin yacigaba da fadin ,"
Yanzu zaki koma kicigaba da zama da yar uwar takine , dan wannan mijin naki dashi da mace marabansu kadanne , gwarama ke wani lokacin kina nuna mazantakan kikwaci hakkin ki awajansa , wani lokacinma baya ahankalinsa wayo kike masa, ince ahaka kuke lallaba rayuwar harkuka haifi dan naki dakikeji dashi,
hmm tode idan wannan rayuwarne muna nan zakidawo kitarar dani , dan kyau ko kudi ko wani mukami bashi bane, kanuna kai namijine shine magana faruk yafadi yana wani kakkashe idanu , yana shafa suman habansa yana dariya,
heelah tacika tab da takaicin magan ganun faruk da dawani abun agefe seta dauka tarutsa masa kai dashi , yanzu mijinta yake duka da wanga kalamai haryake kokarin kirashi da mace ,hmm lallai kuwa da yasan waye IG da wadan nan zantukan basuyi saurin fitowa daga bakinsaba, kyauda matsayi kawai yasani baisan sauran zancenba, inbanda rashin kulawa da IG dayake mata maima zaisa tayi kokarin zuwaga wannan mutumin haryake jifanta da wadan nan zantukan girgiza kai heelah kawai tayi because tarasa abincewa, nan tajuya tayi ficewarta tabar faruk awajan yanata dariyar asara,
parking space tanufa tashiga motarta taye mata key tafice daga cikin hotel din tadauki hanyar gida, gudu take sosai tana tafe tana zuba tsaki tana mai takaicin faruk a rayuwarta, bawani bata lokaci hanya ta kawota gida tashiga yiwa mai gadi hon , cikin hanzari maigadi yatasu yabude mata geat takutso da motar cikin filin gidan ko dai daita parking batayiba tafito tanufi side dinta,
Tana shiga ta yada handbang dinta saman sofa itama zubewa tayi tazauna Tana tunani iri da kala cikin ranta, tadau tsawon lokaci tana zaune agun daga bisani tamike tahaura sama tanufi bedroom dinta,
*****neesha*************
aban garansu nisha kuwa, shopping din kayan abinci sukajeyi komai da komai nabukata ajmal yasa aka dankarashi cikin moyarsa daga bisani sauka sake daukan hanya, atunanin nisha hanyar gida yakamata sukama sekuma taga yama hanyar wani wajan daban, tafiya suke cikeda nitsuwa ajmal yakunna sautin Qur'an cikin mota sa yana saurara yana kumabi ahankali,
gaba daya nisha jitayi ta tsorita inakuma ajmal zaikaiso , dan haka seta kasa hakuri tadago kai kadan tadubeshe cikin barin baki tace, "
in,,na,,kuma zamuje? hankali kwance ajmal yajiyu yakalleta kafin yace,"
gidan da ake seda kan mutane abunda yace kenan yamaida hankalinsa ga tukin dayake, hadiye miyu nisha tayi tazubawa sarautar Allah ido dagani inda zasu, sunyi tafiya sosai kafin hanya takawosu wata anguwa gurin shiru yake kaikace bamasu rayuwa cikin arean daidai wani gida dan madaidaici maikyaun gaske ajmal ya tsaya yashigayin hon,
maigadi security yatasu yabude masa geat nan yakutsa kan motar ciki yanufi parking space yayi parking, tunda suka shigo nisha nisha take kallon gdn gidane maikyan gaske da ban shaawa gamai kallonsa gaba daya hanjin cikin nisha se kaduwa yake aikin tsoro kaddai ace da gaske yake gdn yankan kai yakawota, "
Ogar sir barka da iso security yafadi yana sarawa ajmal alamar ban girma, karsa fitowa daga motar yayi yana fadin,"
Mutanen suna ciki? "
Eh sir , you can go ajmal yafadi daga nan security yakuma bakin geat yatsaya, ajmal hankalisa ya mayar kan nisha dake zaune cikin mota tayi tsuri tsuri da ita Tana kallon motocin dake jere haraban gidan tana tunani se tsintar muryan ajmal tayi yana magana Wanda yayi saurin dawo da ita daga tunanin da tatafi,"
Stay there and waited for me yana gama fadin haka yarufo kofar motar yanufi ciki, shiro nisha tayi tazauna harna tsawun wasu lokuta tazaune cikin motar tana jiran fitowarsa but shiru haryanzu baisa ran fitowaba, cande nisha tashiga kokarin morda handle din murfin kofar motar but tajita arufe alamarde ya rufeta gaba daya maida kanta tayi seat din kujeran tajin gina seji tayi hawaye tsil tsil yana diga ,
gaba daya takaici ya isheta sekace ba mutum yarufe cikin motaba yayi tafiyarsa yanzu kusan minutuna 40 kenan amma baifitoba , nanma Allah yasa ya sauke mata glass din motar isa yana shiga dabatasan yazatayiba, itakam tagaji da jira tsabar takaici kwantar dakanta tayi saman cinyarta tashigayin kuka tamkar karaman yarinya,
jim kadan wasu manyan alhazawa guda biyu sukafito sebaza gare suke fiskan nan ba annuri se guna gune suke kasa kasa suka nufi motarsu dasukayi parking cikin haraban gidan suka shiga suka nufi hanyar fita security yabude musu geat suka fice, ba ajimaba shima ajmal yafito gefensa dauke da wani matashi mutumi minti 2zuwa 3 sukayi suna magana kafin suka rabu matashin mutumin yanufi motarshi shima yatafi, ajmal naganin fitarsa shima yanufi tashi motar,
jin ana kiciniyar bude mota yasa nisha tadago dasauri tashi share hawayenta tanajan hanci nan da nan face dinta yayi jawur dashi , face dinta takawar gefe ajmal nashiga motar baicemata komai ba yayiwa motar key suka fice daga harabar gidan suka dau hanyar gd,
Kofa suka hanyarsu takumawa ajmal yalura da yanayin yarinyar kamar bata yanayi na happy but baidamu da hakanba yacigaba da tafiya sannu ahankali har Allah yasa suka iso gida lapia, nan yadanna hon din motar mai gadi yabude geat kafin yasamu daman karisawa haraban gidan yayi parking ✍🏼✍🏼
Ayimin afuwa🙏nayau yayi short dayawa banajin dadi kuma banida charge🦚🦚IG AJEEMAL🦚🦚
Story and writing by
Oum amreesh❤️
Khaleeseart Raeeys💦💦. 4️⃣7️⃣🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹_,_,__________✍🏼 nisha kamar jira take yayi parking cikin hanzari tasuma kokarin murda handle din kofar tafito, ajmal yayi saurin dakatar da ita "
wait zaro dan karamin card yayi wanda kedau keda number waya yamika mata yana fadin,"
any time you can call me kiji ko inada bukatan wani abin,
ba tareda wani musuba nisha takarbi card din tafice daga motar tanufi part dinsu , shima fitowa yayi tareda bude bayan motar , wasu daga cikin security's mutum uku suka tasu suka iso gareshi suna masa"
barka , nan ya amsa tareda umartasu da daukan kayan shopping dinda yake tafedashi su isa dashi ciki , yakuma umurcesu da duk wani abunda ya lalace cikin store koyagama amfani afiddasu asanya wayanda yakawo ,
bawani bata lokaci sukashiga yin aikin da ogansu yasasuyi, daga bisani shima yadauki wasu ledar yabi bayansu , koda yashigo parlourn heelah yatarar tsaye zakiyar parlour tana kallon shiga da fitan security's wadda tana ganin shigowarshi tanufishi tana yar murmushi,"
your welcome dear heelah tafadi tana kokarin karban ledar hanunsa , ajmal kallonta yayi da mamakin ganinta wannan lokacin sam bayi tunani zai dawo yatarar da ita cikin gidanba, dan haka seya sakar mata ledar hanunsa daga bisani yawuceta ya haura sama ya nufi bedroom dinsa ,
yanashiga yacire kayan jikinta still toilet yasake fadawa domin yin wanka , yana fitowa yakimtsa yashirya cikin kyakykyawan manyan kaya wadanda yamusu kyau domin kowacce kaya shiyake musu kyau basu suke masaba , nan ya matsa gaban mirror yana tace suman kanshi
yana tsaka da tace kan heelah taturo kofa tashigo hanunta dauke da wani dan madaidaicin tray wanda yake dauke cup cikinsa ice tea gefe kuma plate ne maidauke da pizza akai wanda ajmal yashigo dasu cikin leda,
seda tazo tsakiyar dakin ta dire tray din saman table din dakin , daga bisani tadago tana dan murmushi ta kallaishi kauda kai yayi yakalli mirror yacigaba da abunda yake , seda yagama comb din kanshi , daga bisani ya ajiye comb din yadauki hula yasanya yadauki agogo yana kokarin mannawa hand dinsa ,
cikin hanzari kamar wacce akasata heelah tamike tanufeshi tana kokarin taimaka masa wajan sanya agogon , but se dakatar da ita yayi yamatsa gefe , yasa kayanshi sannan yadauki phone dinsa saman bed yasoma kokarin fita daga dakin,"
wait honey heelah tafadi tareda shan gabansa ta tsaya tana fadin "
where are you going too, bakaga nakawo maka abun tabawa bane? heelah tafadi tana nuna masa saman table, seda yakalli gurin da ta nuna masa daga bisani ya kalleta baice mata kalaba yakai hanu gefen shoulder dinta yadan matsar da ita gefe yasamu daman shegewa yabar bedroom din daga nan yafita yashiga mota yabar gidan ,
komawa heelah tayi tazauna tana kallon tray dinda tayiwa ajmal gwanita takawo masa yaki kallah ,tsaki kwai tadinga buguwa tana sakewa daga bisani taja tray gabanta tasuma cin pizza tana zugar ice tea tana kuma tsinewa nisha cikin ranta ,
karfe 9 nadare bayan kammala dinner yau Ba awani tsaya yin hira dayawaba daddy da ammi kusan tare suka dawo yau kowannensu agajiye yake dan haka suna gama dinner sukayiwa su hajia sallma suka nufi bedroom dinsu , suma su hajia da Goggo rabi ba dadewa suka mike zasu nufi makwancinsu dan haka suka umurci su reeda suma suje sukwanta dare yayi daga haka sukayi sallama kowa yanufi turakansa,
Su nisha suna shiga bedroom sukayi shirin kwanciya bacci , harsun kwanta kenan , nisha tamike daga kwanciyar da tayi tasanya hanu kasan pillow tajanyu card
din da ajmal yabata ,"
hmm wannan papan aheel din yacika jin kai dayawa harda wani bani card number dinsa , wai nakirashi naji koyanada wata bukatar bama shizaikirani yafadi abin da yakesoba nine maikira? Nisha ke maganan zuci,
dan turo karamin bakinta tayi nan tayi copy number izuwa cikin phone dinta , sanna tawurga card din saman bedside table,
kiran numbern tashigayi bugu daya zuwa biyu dataji Ba adaukaba takashe wayar tamaida kanta saman pillow takwanata dama zuwa kai masa abinci bawai yaje har ranta bane kawai kaimasa take ,especially yauda yabata mata rai bata sawa ranta kai masa wani abinba, nan takwanta tayi baccinta sauran kam already sunriga sun kulle idonsu sunyi bacci,
yau weekend nisha tunda tatashi sallah bata komaba seda tadan taba karatun Qur'ani sannan ta koma takwanta amma bacci yaki zuwa juyawa tayi takallisu fadeelah sunyi dai daiya abunsu saisheka bacci suke, wayarta tadauka daniyar shiga game dan debe kewa but se ganin 1 miss call na ajmal tayi misalin karfe 11am time din tayi bacci,
nan tadan tabe baki tashiga game abunta tasuma bugawa , guraren 8 ta tsagaita because tagaji dayin game din ta ajiye wayar tanufi toilet tayi wanka ta tsaftace jikinta daga bisani tafito takimatsa tashiraya cikin skirt and blouse na atamfa sabo Wanda yake daya daga cikin kayanda ammi tasa akayi matasu ,
tayi kyau hartagaji duk da bawata kwaliya tayiba tana tsaye jikin mirror tanasu tasanya dan kwalin bisa kanta but kasa because bata iya daura dan kwaliba hasalima tafison ta ammali da hula shiyafi zama kanta , amma dan kwali baya zama saboda gashinta yanada santsi sosai shiyasa idansuka hadu da dan kwali basa shiri , nanfa takama hanyar fita daga bedroom din tareda dan kwalin bisa hanunta,
direct kitchen tanufa ta tarar da bakar na aikin da tasaba , baba barka naganin nisha tashigo da dan kwali a hand dinta Ba asaman kantaba yasa Barka tashiga yar dariya tana fadin,"
Ikon Allah yau koma kallabin baisamu wajan zama bane bisa kanki naganshi ahanu ana yawo dashi? dan tura baki nisha tayi tana dan buga kafa tana shagwabe fiska tace, "
Wlh baba bakar kasa daurawa nayi daga nadaura se yazame shine nazo kitaimaka min , "
Hhhhh kai Allah ya kyauta tahu nadauramiki , ammafa ban iya daurin yan mataba natsofi zanmiki idan kinyarda? bakar tafadi tana dariya,"
Eh kimin inaso nisha tafadi gami da matsawa kusa da baraka tashiga daura mata dan kwalin , nan Barka tashiga ninke dankwalin rubi biyu taimata dauri irinna yayinda but amma yanzu kusan yammata shisuka sabonta shi yan matanmu suka yawaitayi(ture) Wanda za aturo dan kwali gaban goshi madaurin kuma amaidashi tsakiyarkai"
yar nan Namiki daurin zamanin mu amma daurin tayi miki kyau sosai Barka tafadi tana kallon kyakykyawan face din nisha,"
Oh kai nagode sosai baba Barka, "
Laah bakomai Yar nan , nan nisha tasa hanu cikin aikin da ta tarar Barka tanayi sukashiga yin aikin tare, nan da nan guraren9:30 suka kammala komai sukajera Inda yadace , daga nan nisha takuma kitchen dan haduwa gogan nata nashi breakfast din seda tahada komai tajereshi saman kyakykyawan tray din daga bisani tafito tanufi hanyar waje ,..
ahankali take tafiyar har takariso side din ajma security din dake zaune gefe dawajan wanda tundaga nisa yaketa yake hakwara yana kallon nisha har takariso shide baya gajiya da kura mata ido because yariyace masha Allah wanke hanu kataba ,"
Barka nisha tafadi tana kallonshi tana murmushi yau da gobe harsun saba daganin juna,"
Barkankide yafadi yana washe baki gamida bude mata kofar nisha ma murmushi take tareda shigewa ciki yamaida kofar yarufe, koda nisha tashigo bakowa cikin parlourn sai aheel dake kasan carpet yakurawa TV ido kamar zaishiga ciki yana kallon cartoon, ga plate din indomie da kwai gefe dan bowl din corn flakes yanata juya spoon yana wasa ganin nisha dayayi tsaye bakin door tana zuba masa murmushi yasa yatashi dasauri yanufota yafada jikinta ya rungumeta
dan matsawa kadan tayi tasamu tasauke tray din abincin saman table din parlour sannan takalli aheel tadaukeshi cidak tashiga juyawa dashi tana fadin,"
Miss you so much my little angle, kafin tasaukeshi suka cigaba da kyakyatawa because sunyi kewan junanso ,"
To yar anace , shugaban masu iyayin duniya yar shishshigi tsakanin miji damata , kamar daga sama tajiyu muryan heelah tafito daga kitchen hanunta rike da tray din abinci, seda heelah takarisa da abincin dining kafin tajuyo takalli nisha da aheel yamakale ajikinta tamkar mai komawa ciki, "
hmm to yaude abiwani sarkin gdn ahanuna yake nakarbi gidana bana bukatar iyayinki cikin familyna , dan haka kidauki tarkacenki kikara gaba mana bukatan sake ganin kafarki cikin parlourna heelah tafadi gami da karisowa tsakiyar parlourn taja ahanun aheel tana fadin,"
Banason iyayin banza zauna kacigaba dacin abincinka, kuka aheel yasuma kokarinyi yaki zama kamar yadda mummyn shi tace, cike da takaici heelah taja hanushi tana kokarin haurawa sama ganin ajmal na sakkowa yasa tadakata tareda sakin hanun aheel ,
ahankali ajmal yagama sakkowa yana dan gyara hanun rigarshi yasanya kananun kaya yayi kyau dashi , cikin sauri cike da kirsa irin namata heelah takarisa gareshi tana wani ringwada tana karya jiki, "
Dear seyanzu bacci yabar idonka tundazu naketa gadinka ina dubaka cikin bedroom din but baka tashiba se bacci kake , nikuma banaso nakatse maka bacci shiyasa ban tashekaba muje kayi breakfast gashi can yana jiranka heelah tafadi tana rungumarsa gamida jan hanunsa but sejitayi komotsawa baiyiba balle yabita yana tsaye kikam karmar tsuhun soja,
hanunsa yatsame daga nata yatahu yazauna bisa kujera time din aheel ya sidado yazauna gefensa tareda hugging hand din papansa, ajmal ido kawai yadaga yakalli nisha tashiga matsuwa ahankali seda tazu dab tasunar dakai ,"
Antashi lapia"
Fine kawai ajmal yace bayan nan baikuma cewa wani abuba, itama nisha shirun tayi gani haka yasa ajmal dagowa karu nabiyu yakuma kallonta yana fadin, "
sena roka ayi serving dinane? cikin hanzari nisha takalleshi sannan tamaida kallonta ga heelah tayi tsaye kamar gunki tana kallonsu ✍🏼✍🏼✍🏼